Monday 17 April 2017

CIN AMANA KO FANSA

πŸ““πŸ““πŸ““πŸ““πŸ““πŸ““πŸ““πŸ““πŸ““
          *CIN AMANA*
                   *KO*
               *FANSA*
πŸ““πŸ““πŸ““πŸ““πŸ““πŸ““πŸ““πŸ““πŸ““



Zahra Muhammad mahmud


*pure moment of life writers*
          *p.m.l*


*Dedicated to My sweet Aunty,Hajiya Jameela (meelmoh)C.E.O meelmoh magazine Allah yak'ara d'aukakaki farar mace alkyabbar mata,Aljanna me masoya dayawa nagode.*


*page 6-7*


Fatima nadawowa daga rakiyar Hydar,Khairat tajata zuwa d'akinsu,ko zama bata bari sunyiba tace,

"Sis wai nufinki ke Hydar yakeso?,kuma shine wanda ya amshi numbern ki?,pls ineed more explanation."


"Why are you asking me all those questions?,ina tunanin bakya buk'atar k'arin bayani sabida tambayoyinki tafe suke da amsoshinsu,tunda idonki yagane miki,I hope you understand what I mean?".

Ajiyar zuciya tayi ta nemi guri ta zauna tayi tagumi,Fatima ce ta dafata tace,

"Sis are you ok?".

Asanyaye tace,"yes am ok, but Sis let me ask you  something".

Fatima tace ,"uhum inajinki".

"Dama ba wani abu bane tambayarki zanyi kuma kema kina sonshi?,sannan zaki iya auranshi?"Khairat tafad'i kamar me shirin yin kuka.

shewa Fatima tayi tafad'a jikin Khairat d'in tace,

"Wlh Sis har kinbani wata bazawarar dariya,to ke ko idona kika kallah ay kinsan na mato akanshi,wacce macece aduniyarnan zata samu kamar Hydar tace bata so ay wlh sede in bata samuba,ni wlh yanzu banida wani buri daya wuce naga na aureshi badan kudinshiba sedan nagartattun halayansa wanda najima ina burin miji me irinsu, ay Sis ki tayani addu'a kawai Allah yabarni tare dashi kusha biki,"tak'ara rungume Khairat cikin farin ciki mara misaltuwa.

Khairat jitayi kamar ta watsamata wuta ajikinta,a sanyaye tace,"Allah yanuna mana lokacin natayaki murna y'ar uwa".

Ranar Khairat batayi bacciba sabida tunanin yazatayi, tanason y'ar uwarta matuk'a amman batajin son datakema Fatiman yakai wanda takema zuciyarta,tanaji zeyi wuya tabar Fatima ta haramta mata abinda ta dad'e tana nema wato Hydar.

Koda safiya tayi zasu tafi makaranta,khairat sam babu walwala atattare da ita gaba d'aya ta sauya,cike da kulawa Fatima tace.

"Sister alamu sun gwada baki da lafiya don Allah ki sanar dani meke damunki,kinsan banison damuwarki hankalina tashi yake don Allah ki sanar dani ko hankalina ze kwanta".

Azuciyarta tace,"kece damuwata Fatima,kuma kece ciwon dake damuna,neman hanyar dazan magance hakanne yasa kika ganni haka",amman afili setace mata,"Wlh da ciwon kai na kwana Sis shiyasa kika ganni haka amman ba abinda yake damuna".


Haka suka tafi makarantar Fatima se tausayawa Khairat takeyi,bata zargi komaiba game da sauyawar Khairat d'in daga jiya zuwa yau.

Son da Fatima takewa Khairat rai ne kawai bazata iya bata ba jinta take har ranta burinta ta faranta mata akullum dan farin cikin Khairat shike sata farin ciki.

Ana tasosu daga makaranta gida suka dawo ga mamakin  Fatima Hydar tasamu a k'ofar gidan yana jiranta,tun kamin Ta k'araso ya iso inda take jakar makarantarta ya amsa yace.

"Barka da dawowa me d'akina ya karatu,?ina fatan baki wahala ba?".

kunyace duk ta rufeta ganin irin kallon dayake mata murmushi kawai takeyi ta rufe fuskarta a hijab,takasa bashi amsa.

Khairat jitayi kamar ta kurma ihu dan bak'in ciki ga wani azababben kishi daya tasomata,maganama takasa. Hydar ne ya waigo ya kalleta yace, "k'anwarmu ungu jakar Auntyn ki kishigar mata da ita yanzu Zata shigo itama".yamik'a mata jakar,yata iya dole ta amsa tashige gidan,shikuma da Fatima suka shiga daga cikin gidan amman ba sit room ba.

Agurguje suka gaisa yace ze wuce Abuja ne yanzu shine yace bari yazo yaganta dan inyatafi zekai two months acan sabida zeyi wata tafiyane daga cand'in,Fatima ranta besoba hakade yay ta kwantar mata da hankali da alk'awarurruka masu yawa har tak'aitaccen tarihin rayuwarsa seda yabata,itama akunyace tabashi nata.

"Princess zamu fahimci juna kamin nadawo sabida ina dawowa zan turo zancan auranmu bawani lokaci nakeso ad'aukaba nak'osa naganki gidana wlh kuma zuwa lokacin kungama Waec d'inku dan haka don Allah ki amince muyi aure Kya ci gaba da karatun agidana".

murmushi tayi tace, "bakomai Allah ya zab'a mana abinda yafi zama alkha'iri Allah kuma yakaika Lfy yadawomin dakai lafiya",tana gama fad'a tak'ara rufe idonta tana dariya mara sauti,shima dariyar yayi yace, "Ameen my Princess".

Kayan dayayomata shopping su yadunga fito dasu almajirai suka shigar mata dasu cikin gida haka sukai sallama kowa na bak'in cikin rabuwa da d'an uwansa.

Khairat ganin kayan da Hydar yakawowa Fatima shi yasa tak'ara kwad'aituwa da son mallakarsa,numfashinta har rik'ewa yakeyi inta tuno da irin kallon dasukewa juna d'azu tsakanin Fatima da Hydar.


*Waye Hydar*

Hydar Jeebrin Lameed'o shine cikakken sunansa,d'ane guda ga Alhaji Jeebrin Lamid'o.

Shikad'ai Iyayensa suka haifa shiyasa yataso cikin so da kulawa,hydar miskili ne na ajin farko baruwanshi dashiga sabgar dabata shafeshi ba shi mutumne meson girma,kuma yanada tsaron Allah duk abinda addininsa yahana yana k'ok'arin kiyayewa yana takatsantsan da imaninsa kud'i da mulki basu sa ya kauce hanya ba.

Mahaifinsa babban ma'aikacin gomnati ne ajihar kaduna amman asalinsa d'an jahar Adamawa ne acikin garin michika zamane yakawosa kaduna kuma anan ya had'u da Hajiya Hadiza wato mahaifiyar Hydar kenan.

Suna zaune acikin wata anguwa me sunshine kinkinau dake garin kaduna.

Hydar cikakken d'an siyasane wanda kowa kesonshi,yayi degree har zuwa Masters duka akan fannin siyasa shiyasa yake yinta bisa tsari, yarik'e muk'amai kala-kala a ma'aikatun gwamnati har zuwa yanzu dayake wakilcin Kaduna South a Abuja.

Hydar  yayi aure da matarshi me suna Maryam Sun haifi yaro d'aya mesuna Haisam inda tasake samun wani cikin gurin haihuwa tarasu bayan ta haifi y'amace inda yariyar taci sunan mahaifiyarta wato Maryam suna kiranta da Iman.

Tunda Maryam ta rasu Hydar yarasa natsuwarsa sabida Maryam tana da kirki ga hak'uri duk abinda yakeso shi take mishi shiyasa yakasa mantawa da ita,seda iyayensa sukai ta nemar mishi taimako daga malamai sannan zuciyarshi ta natsu,amman duk sanda yakalli yaransa se yayi kuka na rashin mahaifiyarsu, yaran na hannun mamanshi ita take kulawa dasu.

Sam Hydar yacire batun aure aranshi kwatsam se yahad'u da Fatima kuma  Allah yajarabceshi da sonta wanda har yasanar da iyayensa yasamu mata in yadawo daga tafiyar nan dazeyi ze turasu aje anemar masa auranta.

cigaban labari

kubiyoni


Maman Yusuf.

Sunday 16 April 2017

CIN AMANA KO FANSA

πŸ““πŸ““πŸ““πŸ““πŸ““πŸ““πŸ““πŸ““πŸ““
            *CIN AMANA*
                    *KO*
                *FANSA*
πŸ““πŸ““πŸ““πŸ““πŸ““πŸ““πŸ““πŸ““πŸ““



Zahra Muhammad Mahmud


*pure moment of life writers*
         *pml*


*page 4-5*



Koda suka isa gida Khairat gaban mirror taje ta tsaya tana k'arewa kanta kallo,can kuma tasake fashewa da kuka ta fad'a kan gadonsu,Fatima wacce dariya tagama kamata da k'yar ta daure tace.

"Sis lafiyarki k'alau kuwa?, wai kukan me kikeyine haka?".

Cikin kuka Khairat tafara magana.

"Haba ki dubenifa wai ace duk had'uwar nan tawa manyan mutanennan bawanda yakalleni bare yace yana sona,nibama wannan ne yake sani kukaba more than 3hours nad'auka ina Kwalliyar nan Amman wai ace me hotone kawai na burge ay dole nay kuka,"taci gaba da kukanta harda majina.

Fatima ko inbanda dariya ba abinda takeyi sabida gaba d'aya takasa magana abun yabata dariya sosai. Fita Khairat tayi a d'akin sabida dariyar da Fatima take mata.

Tunda wannan D'an majalisa ya amshi number Fatima se yau ya gwada kiranta kimanin sati guda kenan da had'uwarsu,lokacin daya kira suna zaune ita da Y'ar darunta wato Khairat suna labarin wani littafi da ake rubutawa na online writers nawata marubuciya Zahra Muhammad mahmud me suna *Allah gatan bawa*.ajiyar zuciya Khairat tayi tace.

"Ya Ubangiji nima kasa nayi irin wannan dacen da jarumar littafinnan ilham tayi,nima nasamu miji kamar Anwar Tunda nima kyakkyawace",ta fad'i harda d'aga hannu sama,dariya Fatima tayi tace.

"Allah yataro minke Sister".

k'arar wayar Fatima ce takatse musu hirar,number tagani da kamar karta d'aga cande kuma ta d'auka,tace,

 "Salamu alaikum".

"Wa'alaiki salam ya ma'abociyar natsuwa da hankali,".

Tsigar jikinta seda ta tashi sabida jin daddad'ar muryar me maganar, katseta yayi da cewa.

"Am sorry princess tunda na amshi numberki ban kiraki ba se yau please ayimin afuwa, al-amurane suka sha kaina tuba nake sarauniyar mata".

Murmushi ne ya sub'ucewa Fatima kamar yana kallonta,sabida ba k'arya muryarshi kad'ai dataji tasa taji takamu da son mamallakin wannan murya.cikin salo najan hankali tace.

"Ammaka afuwa duk da bansan dawa nake maganaba pls can you tell me more about your self?".

muryarta se yau yake k'ara jin dad'in muryar da k'yar yace.

"Am Hydar Jibrin Lamid'o, wanda yaturo kibashi number ranar bikin friend d'inki Jameela sati guda daya wuce, so inbazaki damuba inason address d'inki dannazo mugaisa kinji pls badan na isa ba sedan Allah."

Fatima tunani tashiga yi agame da sunannashi dan ita tabbas tasan d'an majalisarsu me wakiltarsu a Abuja sunanshi kenan,toko suna ne yazo d'aya?, ko shine dakanshi?,kai mezeyi dani?bashi bane.haka tadunga tunani ita kad'ai shine dayaji shurun tayi yawa yakatseta.

"haba princess wlh ba cutar dake zanyiba kidaure kibani address d'in kinji zuwa anjima da yamma zan shigo mugaisa,"ba musu Fatima tai mishi address d'in gidansu,yay mata godiya yace se yazo anjiman sukayi sallama. Tana ajiye wayar Khairat wacce tun d'azu kallonta kawai takeyi tace.

"Sister wlh tunda nake bantaba ganin budurwa me arha irinkiba, haba don Allah shikenan kowa yataya ba jan aji kike siyarwa Wlh kina badamu,nide gani nake yadda akasan address din gidanmu ta dalilinki ko gidan gomna se haka ace ayi mutum sam bajan aji wlh kigyara halinki ni nafara gajiya da hakan,"tafad'i har da tsakinta.

murmushi Fatima tayi tace.

"Sister kenan shi wannan Jan ajin dakike magana ba irinshi addininmu yakoyar damuba, sabida duk wacce takeyin irinshi ba sunanshi Jan ajiba wulak'anta halittar Allah sunanshi wanda kinsani nasani ba abune me kyau ba dan haka ni inde hakan danakeyi shine rashin aji to nayarda har atashi duniya bazanyi ajiba arayuwata".

"to Allah ko yakyauta miki wlh,yanzu kuma wanne d'an wahalar ne yakiraki?"inji Khairat.

"Wanda ya turo nabashi number na ranar dinner d'in Jameela Habib,yacema zezo anjima mu gaisa."


Dariya Khairat ta kwashe da ita tace.

"lalle Sis wato ke baki d'au ishara akainaba kina ganin duk kyannan nawa me hoto kawai na burge agurin,ayko tunda haka ko tafaru akaina Allah Sis may be megadin gurinne ya turo kibashi number,"tasake fashewa da dariya.

Fatima itama dariyar takeyi tace,"to in megadine seme?, shiba mutum bane?,koko shi ba Allah ne yayi shiba?,kinga rabani da wannan shirmen naki koma waye ni ina maraba dashi,tunda wannan Karon gurina megadin zezo ay da sauk'i bagunki naturoshi ba bare ki tsine mishi son ranki."

Wata shewa Khairat tayi tace, "ina wlh Sis ayni nafi k'arfin irinsu sede ke, ni ay matar manyace ko kin mantane?".

"Natuna matar Donald Trump,"
Fatima tabata amsa tana dariyar tsokana ita ta d'auka Khairat zataji haushi ga mamakinta seji tayi Khairat tarungumeta tana fad'in.

"Wlh Sis kinyimin fata me kyau,ni abin yace yana sona wlh auransa zanyi baruwana da kafircinshi yayi addininshi nayi nawa,nazama First Lady a America wai ranar ina zansa kaina dan dad'i".

Tureta Fatima tayi cike da mamaki tace.

"Sis ke har son kud'in naki yakai ki auri kafiri matuk'ar yanada kud'i kuma sunanki ze fita as celebrity a duniya wato zaki iya auransa kenan?Allah yashiryaki lamarinki yafara bani tsoro wlh,"tafad'i cike da damuwa.

Khairat ko ko a jikinta mik'ewa tayi tad'auki gyalenta tace ni natafi gidan su Zainab Umar zan amso note book d'inta na chemistry na kwafa sabida banida complete note sena dawo Ummu shuhada",tafad'i tana dariya tafice a d'akin tabar Fatima baki bud'e.


5:30pm Hydar yazo gidansu Fatima,acikin wata arniyar motarshi Range Rover new model fara tasha tinted glass bak'i sosai bame ganin naciki,numbar motar sunane ansa  Hydar 1,gashi yayi shiga ta alfarma wacce duk macen data ganshi seta koka ba laifi Hydar kyakkyawane ajin farko dan yafi Fatima kyau nesa ba kusaba.

Kiranta yayi a waya ya shaida mata gashi ya iso.


Hijabi tasa bayan tad'an k'ara gyara fuskarta tafesa turare tafito zuwa k'ofar gidan, lokacin Khairat bata dawo daga anso littafinba.

Fatima koda tafita wata arniyar mota tagani a k'ofar gidansu wanda batai tsammanin acikinta me nemanta yazo ba, waige waige takeyi tarasa ina wanda yazo gurinnata yatsaya,shiko daga cikin motar K'are mata kallo yakeyi yana k'ara godiya ga Allah daya had'ashi da nutsatsiyar yarinya irinta,ganin tana nemanshine yasa yakirata a waya yace gashinan acikin motar dake gabanta,dasauri yaga ta kallo motar sannan tace.

"to kafito mana,"yace.

"Princess inda hali mushiga daga cikin gidanku in akwai inda zamu zauna peacefully banason intsaya awaje kowa yazo yaganni kinji pls,"amsa tabashi dacewa.

 "sekace mara gaskiya".

dariya yayi wacce tasa Fatima k'ara fad'awa kogin sonshi yace.

"watak'ila hakanne banida gaskiyar ay ba laifi bane dan na nemi mafaka daga gareki," murmushi tayi sannan tajuya cikin gidan,gurin maman Khairat tanufa tace mata tayi bakone tade fad'amata yadda sukayi dashi yanzu tanason abata key d'in sit room d'in Abban su,jamata kunne maman tayi sosai akan tade tsare mutuncinta sannan ta bata key d'in.

zuwa tayi tabud'e sannan tafita takirashi awaya tace yafito to yak'araso sushiga daga ciki, ga mamakinta me makon taga yafito setaga ya tuk'o motar har zuwa k'ofar gidan sosai sannan yay parking yafito.

Hasbunallahu wani'imal wakil itace kalmar dake fita a bakin Fatima sanda tai arba dashi,ba iya kyan shine ya ruda ta ba a'a sanin wayeshi a jihar kaduna shine ya rud'ata, shiko se murmushi yake sakar mata me kashe zuciya har yak'araso gurinta bata saniba,Ta tafi tunani hura mata fuska yayi sannan tadawo daga duniyar data tafi,kashe mata ido d'aya yayi yad'aga gira yace.

"yadai princess wannan kallo ay sekisa nafad'i ayimin dariya", kunyace takamata da k'yar tace mishi su shiga daga ciki.
       
koda suka shiga gaisheshi tayi sannan takawomishi drinks kad'an yasha sannan yace.

"Princess the way you act for the first time dakika ganni nasan kinsan koni waye so no need natsaya ina cemiki nine wane, kawai abu d'aya zan iya sanar dake shine tunda naganki Allah ya jarabceni da sonki so me tsanani,don haka nake rok'on alfarmarki kisoni koda rabin son danake miki ne pls,"yafad'i cikin sigar tausayi.

Fatima bata hana kanta abinda takeso inde be sab'ama addini da al-adar ta ba don haka bata jamishi raiba ta amshi soyayyarsa kuma dama Hydar ba irin mazan da ake cewa kaje senayi shawara bane.

yaji dad'in amsar soyayyarshi datayi batare data wulak'antashiba, abinda y'anmata suka d'auka wai Jan ajine,hirarsu ta soyayya suka shigayi duk da Fatima kunya ta isheta takasa sakin jikinta dashi shine ke mata hirar.


Khairat ta dawo daga amsar littafin lokacin datayi arba da motar Hydar a k'ofar gidansu seda tayi tuntub'e ta fad'i sabida kallon datakewa motar,Allah yasota bakowa agurin da sauri ta Mik'e tashiga cikin gidan tana waigen motar.
   tana tunanin gurinwa me motar yazo a gidansu,zata wuce cikin gidane taga takalmin Fatima a k'ofar sit room d'in Abban su da kamar ta wuce se tafasa taje tayi sallama a k'ofar d'akin,Fatima ce ta amsa gami da cewa.

 "yauwa ga Sis d'ina ta dawo danake baka labarinta Sis kishigo mana kintsaya",bud'e k'ofar tayi tashiga da sallamarta.

Ya Ilahi!!!!.

ita Khairat ta furta sanda tai arba da fitaccen d'an siyasa kuma d'an majalisa me wakiltar kaduna South a Abuja mutumin da Nigeria ansanshi sabida motion d'in daya kaiwa majalisa, uwa uba shine mutumin data dad'e tana mafarkin samunshi a matsayin mijinta na aure.

Zama takeso tayi akan kujera amman dayake arud'e take zamewa tayi tafad'i ak'asa sabida hankalinta nakanshi, dasauri Fatima tazo takamata Ta tashi itako ko ajikinta k'ok'arin gaisheshi takeyi,amsawa yayi bayabo ba fallasa danshi mutum ne miskili ba kowa ke ganin fara'arshiba.

memakon dasuka gaisa tabasu guri ay ina k'ara shishshigewa take tana kwarkwasa ita game kyau hakan beyiwa Hydar dad'i ba don haka sallama yay musu gami da cewa Fatima.

"My Princess zamuyi waya innaje gida kinji take care of your self OK".

amsa mishi tayi da Allah yakaishi gidan lfy Ta gode da ziyara.

bunch d'in one thousands yaba Khairat yace, "to k'anwarmu ga wannan kisha ice-cream,"juyawa yayi yafita bayan yabata kud'in,har gurin mota ya tilastawa Fatima tarakashi sannan sukayi sallama ya wuce.


Maman Yusuf

CIN AMANA KO FANSA

πŸ““πŸ““πŸ““πŸ““πŸ““πŸ““πŸ““πŸ““
         *CIN AMANA*
                *KO*
             *FANSA*
πŸ““πŸ““πŸ““πŸ““πŸ““πŸ““πŸ““πŸ““
  *(TRUE LIFE STORY )*

Zahra Muhammad Mahmud

 ® *PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*
       *PML*

*Godiya ga Allah mad'aukakin Sarki, tsira da Aminci sutabbata ga annabinmu Muhammad sallallahu ala'ihi wasallam.*

*Wannan labari ba k'agagge bane yafaru dagaske,duk abinda ke ciki anyine da gaske, suna kawai na wa'inda abun yashafa Nasauya,da d'an abinda ba'a rasaba.baya ga haka babu abinda Nasauya*

Ya Allah, yadda nafara rubuta littafinnan lfy,Allah kasa nagamashi lfy.

*page 1*

Y'anmatane su biyu, y'an kimanin shekara goma sha shida da haihuwa,suka rugo da gudu zuwa Cikin d'akin kakarsu suna ta kiranta,  uniform ne ajikinsu, alamar daga makaranta suke,

 "Grany!!! Grany!!!  where are you? we miss you so much,mekika tanadarmana yau."
A zaune suka ganta tana Kallonsu, k'arasawa jikinta sukayi, suka rungumeta,  kowacce tamata kiss a gefen kumatunta.

"Kai ni banason iskancinnan naku, ace gird'a gird'a daku Amman har yanzu baku girmaba,wato abinnaku gaba yakeyi,yau kuma harda sumbatata ko?".

Dariya sukayi suka K'ara rungumeta,Khairat ce tace,

"Haba Grany, danma kinsamu munzo gidanki yau shine harda yimana wulak'anci,ni dama wlh banso zuwa ba,Fatima ce da shegen naci tace muzo gidanki,gashi daga zuwanmu  kinfara halinnaki."sakin Grany tayi takoma gefe tazauna,

Fatima tace, "Wayyo Sis kiyiwa Grany uzuri, bakiga se kallonmu takeyiba, alamun taji dad'in ganinmu, hala taji haushin bamuyi sallama bane, ko Grany?",tawaiga Tana kallon kakar tasu.

Grany dariya tayi sannan taruk'osu dukansu tace ,

"Haba kha'iriyya ta fushi kikeyi danine?, nicefa babbar k'awarki ranar bikinki,"dariyace takwacemusu dukansu,khairat tace,

"Wai,dagwargwajiya kenan Grany ansha gwargwaro ranar aurena,"cigaba sukayi da dariyar.

Ranar wuni sukayi agidan Grany,seda la'asar suka mata sallama suka wuce gida.

Khairat da Fatima sa'annin junane, dan anhaifi Fatima da Sati biyu aka haifi Khairat.

Iyayensu mata ya da k'anwane,haka zalika, Iyayensu maza suma wa da k'anine.

Alhaji Nasir Abubakar shine mahaifin Fatima,suna kiranshi da Abba,mahaifiyarta Mesuna Hajiya Salamatu suna kiranta da Umma.yaran Alhaji Nasir hud'u biyu maza biyu mata,Yaya Jameel shine babba, se Yaya Umar mebimasa,se Fatima, da autarsu Yasmeen.

Alhaji Mukhtar Abubakar shine mahaifin Khairat,suna kiranshi da Daddy, Wanda wa yake agurin Alhaji Nasir,uwa d'aya uba d'aya,
Matarshi d'aya Hajiya Binta,wacce take yaya ga mahaifiyar Fatima, yaransu guda shida,hud'u mata biyu maza,Aunty Fareeda Itace babba ,se Yaya Kamal mebimata,se Aunty Khadija,se Kha'irat, se Fa'eeza,da autansu Yusuf.

Gidan Alhaji Nasir dana Alhaji Mukhtar ahad'e suke sede katanga data rabasu,
Suna zaune da iyalansu agarin Kaduna awata anguwa Mesuna Tudunwada dede layin k'osai kan katagum road,

kansu ahad'e yake haka na iyalansu komai nasu tarene ko kasuwancin suma a tare sukeyi inda suke Saida kayan sawa kama daga na maza zuwa na mata, da yara, komai suna saidarwa a kasuwar checheniya dake Kaduna.

Zumunci ne me k'arfi a tsakaninsu inda ahalin yanzu babban d'an Alhaji Nasir yana auran Y'ar gidan Alhaji Mukhtar Khadija, harda yaransu guda biyu suna zaune a kinkinau dake Kaduna,ita kuma Farida wani ma'aikacin nepa take aure harda yaranta guda uku.

Rayuwar wannan family rayuwace mecike daso da k'aunar juna.

Grany,wacce sunanta na aynihi Hajiya Asiya amman jikokinta nace mata Grany,yayinda y'ay'anta da sirikanta kecemata Hajiya,  Itace tahaifi  Iyayensu maza,kuma a kakanninsu ita kad'aice tarage musu sauran duk sunmutu

Kha'irat da Fatima kansu ahad'e yake ko bacci tare sukeyinsa babu abinda ke rabasu suna matuk'ar k'aunar junansu ko kad'an ba'ajin kansu,ajinsu d'aya Boko da Islamiyya, suna da k'ok'ari sosai dan sotari  twins ake cemusu,dan duk jarabawa sede suyi bracket, kowa cikinsu beson b'acin ran d'an uwansa.

Maman Yusuf
πŸ““πŸ““πŸ““πŸ““πŸ““πŸ““πŸ““πŸ““πŸ““
            *CIN AMANA*
                    *KO*
                *FANSA*
πŸ““πŸ““πŸ““πŸ““πŸ““πŸ““πŸ““πŸ““πŸ““

Zahra Muhammad mahmud

*LOSING SOMEONE WHO DOESN'T RESPECT OR APPRECIATE YOU IS ACTUALLY A GAIN, NOT A LOSS.*

*pure moment of life writers*
             *p.m.l*

*page 2*

Rayuwar Fatima da Khairat rayuwace mecike da son juna.

Khairat irin matannanne masu azababen kyau don ko daga nesa ka hangota kasan me kyauce,farace me hanci ga yalwar gashi tamkar indiya, komai da akeso ajikin mace Allah yabata,wannan baiwa da Allah yay matane yasa ta d'auki dogon buri akanta tanaji da wannan kyau da Allah yay mata shiyasa ko saurayi take burin me kud'i,in talaka yazo gurinta seyasha wulak'ancin dako a hanya yaganta baze sake marmarin kulataba,
   har k'awayensu na makaranta sunsani shiyasa yanzu kirarin dasuke mata shine matar Manya,jin dad'i take insuka kirata da sunan.

Fatima nada kyau dede misali Amman bata Kama k'afar khairat ba,sede dirin halitta na y'a mace itama Allah yabata,batada da wulak'anci ga kowane ne yanuna yana sonta burinta de Allah yabata miji nagari.

Akan wannan halin na Khairat sunsha yin fad'a da Fatima sabida hakan,inkaji fad'ansu to akan wannan halin na Khairat ne Sam Fatima batason halin.

Yau ba makaranta dan haka su Fatima suka tsefe kansu sukaje Kitso,ahanyarsu ta dawowane wani me liffan yatsaresu,saurayine matashi ba laifi akwai natsuwa da kamala atattare dashi sallama yamusu,

"yan mata barkankude," yafad'i yana kallon Khairat da alamun ita yabiyo.

Khairat bata amsaba sema wata uwar harara data watsa mishi.Fatima ce ta amsa,

"barka kadai malam".

murmushi yayi sannan yace,

"Don Allah kuyi hak'uri da tsaidaku da nayi wlh son yar uwarkine yakamani tunda na hangota duk danaga ita ranta kamar beyi na'am daniba Don Allah kubani number d'inku da Address dannazo har gida nasameta,"yafad'i yana kallon Khairat.

"Dank'ari mune zamu baka address d'inmu harda number waya,to wlh bakaji da kyauba gwara tun wuri kanemi dede kai danmu ba sa'anninka bane dahar zaka wani ce kana sona Allah yakyauta wlh farashin gold beyi karyewar da za'ayiwa jaki mangala dashi ba,"tafad'i rai abace taja hannun Fatima da niyar suwuce subarshi, kwace hannunta Fatima tayi ta tsaya,itako Khairat gaba tayi abunta,cikin sigar tausayawa Fatima tace mishi,

"Don Allah malam kayi hak'uri wlh banji dad'in abinda tayi maka ba, kuma in zan baka shawara ka hak'ura da ita wlh tunda tanuna bata sonka banajin akwai abinda zesa tasoka kayi hak'uri kanemi wata don katsira da mutuncinka kaji,don Allah kuma kayafemata pls,"tafad'i cikin sigar rarrashi.

Murmushi yayi Yace, "bakomai baiwar Allah nagode dake kika saurareni, Amman kinsan sharrin so wlh jinake bazan iya hak'ura da ita ba kitaimaka kibani address d'inku da sunanku pls banak'i shawarar ki bane zuciyata ce bazata iya hak'uraba ki taimakamin pls",yafad'i kamar zeyi kuka.

Ba musu Fatima tabashi abinda ya buk'ata dan ta tausaya mishi daga k'arshe tamishi fatan alkha'iri, dazasu rabu yafad'a mata sunanshi Ahmad.

A hanya tasamu Khairat se cika take tana batsewa kotakanta bata biba sabida inda sabo tasaba da halinta, ahaka suka ci gaba da tafiya bamecewa kowa uffan.

Suna shiga gida d'akinsu suka wuce dan ajiye hijabansu ananne Khairat tacewa Fatima,

"Wai don girman Allah sis se yaushene zaki gane darajata tafi k'arfin irin wa'innan samarin? kina zubarmin da ajina wlh ni matar manyan mutanece,yakamata kigane har yanzu ban samu kalar mijin daya dace daniba, amman ke da Kare da doki kowama address d'inmu kike basu suzo su tak'uramin dan Wlh wannan ma nasan kinbashi address d'in watak'ila ma harda rakiyar phone number mitsss,"tayi tsaki ranta ab'ace.

murmushin takaici Fatima tayi ta dubeta tace,

"Sis kenan wani lokacin inkikayi wani abun senaga kamar ba'a family d'aya mukeba,dan de tarbiyya dede gwargwado iyayenmu suna bamu kuma sunsamu a makarantun da ake koyar damu sanin darajar d'an Adam.Haba Sis kituna fa Allah dakanshi yace yakarrama bani adam kewacece dazaki dunga wulak'anta mutane?,kituna Allahn daya baki kyaun dakike wulakanta mutane sabida shi shine yayi kuma wainda kike wulak'antawar bayan yahanemu dayin hakan, tabbas nabashi address sede inyazo shima ki koreshi kamar yadda kika saba,ni narasa mekike nema aduniyar da watarana ko labarinki baza'aji acikintaba, haba Sis yakamata ki farka daga wannan banzan mafarkin dakikeyi."

"Mafarki fa kikace Sis to wlh kece kike mafarki ni reality show nake yi, koma mezakice naji amman wlh babu yadda za'ayi nakai kaina gidan talauci sede kita fad'in abinda kika dama,kuma wlh shima wannan dakanshi ze kama kansa dan bade niba sede wata wlh."kiran da Umman Fatima tai musune yasa suka bar maganar suka tafi gurin kiran.

Maman Yusuf
πŸ““πŸ““πŸ““πŸ““πŸ““πŸ““πŸ““πŸ““πŸ““
         *CIN AMANA*
                  *KO*
              *FANSA*
πŸ““πŸ““πŸ““πŸ““πŸ““πŸ““πŸ““πŸ““πŸ““

Zahra Muhammad mahmud

*Pure moment of life writers*
            *pml*

*Page 3*

Yau Ahmad yashirya yazo gurin Khairat hira, dakyar tayarda tafito koda tagashine me kirannata wani uban tsaki taja gami dayimasa kallon uku saura kwata,Shiko se Murmushi yake adole ze saci zuciyar ta tun kamin yay magana tarigashi,

"Amman duk yadda akayi agidanku cikin tumaki kake kwana Shiyasa zama dasu yasa kad'auki halinsu,kai jakin inane nace ma bana sonka bana k'aunarka Amman sabida taurin kunne irin na balama yasa kabiyoni gidanmu wlh baka da zuciya sam ni matar manyan mutanece ba irinka ba ubanme kaci ubanme Kabani dan haka kaje kanemi dede kai d'an wahala kawai",ta fad'a tana tsartar da miyau.

Zuciyar Ahmad kamar zata fashe sabida bak'in ciki,tunda yake wani mahaluki betaba cimishi mutunci irin hakaba se yau,hannu yad'aga ze kifa mata Mari sekuma yafasa.

Wata shewa tayi sannan tace,"hattarade d'an samari ni ba irin wa'innan matan bace da ake duka wlh ka kuskura katab'ani sekayi danasani wawa kawai,

Dakyar ya iya cemata,

"Ni acikin tumaki nake Kwana amman wlh bantab'a tsammanin tumaki suna haifar y'ay'an mutum ba se akanki,baki da hankali bakisan darajar mutane ba Kije duniya ce zaki had'u da dede ke komai daran dad'ewa,yana gama fad'amata haka yaja liffan d'inshi yabarta atsaye baki bud'e. Dagudu tashige cikin gida tana kuka kai tsaye d'akinsu tanufa inda ta sami Fatima na kwance tana chatting a wayarta,fad'awa kanta tayi tana kuka, afirgice Fatima ta ruk'ota sabida batasan damuwar Khairat ko kad'an in akwai abinda kesata damuwa toshine ganin hawayen Khairat,arud'e take tambayarta,

"Sis keda waye don Allah Ki sanar dani abinda aka miki zaki sani cikin damuwa pls",cikin kuka Khairat tace,
"Sis nida shegen Ahmad d'innanne yau ancimin mutuncin da tunda nake bawanda yatab'a yimin",tasake rushewa da kuka.

"me yayi miki just tell me",
Cikin kuka takwashe duk abinda yafaru ta fad'amata bata b'oye komai ba,duk da Fatima taji zafin kiran Iyayensu tinkiyoyi dayayi amman Seta daure tace,

"Wow that's good,gaskiya gayennan yaburgeni wlh inason mutumin dayasan darajar iyayensa, ke kin kira iyayensa tinkiyoyi why not baze kira naki da sunanba ?bayan kece kike aykata abinda kowa yagani ze d'auka tinkiyoyinne iyayenmu,ni wlh banji haushinshiba ke nake jin haushi sabida kece kika ja yazagesu,"

"Sis kinada hankali kuwa?, su Abba fa yazaga amman shine bakiji haushinshiba Lalle ma Sis wlh kinbani mamaki,"

Dariya Fatima tayi tace,tana k'ok'arin fita daga d'akin cikin dariya,

"Wayyo ga abin duka amman ba Kara Allah yataroki Sis",tak'arasa ficewa daga d'akin.

Ranar wuni Khairat tayi kuka dan takaicin zagin iyayenta da akayi,wanzami bayason jarfa dama.

Yau ana bikin wata k'awarsu acan cikin unguwar rimi GRA,dan haka Khairat shiri take kamar zata sauya fata dan kwalliya ita ala dole zata samu saurayi me kud'i tunda bikin manyane,Fatima dariya kawai takeyi tana mata fatan shiriya.

Sun isa gidan bikin k'arfe hud'u na yamma nanfa kawayensu aka shiga koda kyan da Khairat tayi habawa tuni tafara shan k'amshi ita ga me kyau Musammam insuka kirata da sunan datake matuk'ar k'aunar wato matar Manya kanta har girma yake k'arawa.

5:30pm  suka tafi dinner zokuga Khairat yadda take tafiya kamar Bazata taka k'asaba ita adole zata jawo hankalin mutane kanta Fatima ko gaba tayi ta kyaleta.

Dayake k'awar tasu wani Reps ta aura to gurin dinner y'an majalisu ne sosai suka zo,anyi duk abinda akeyi agurin dinner inda aka bukaci Khairat da Fatima suyi jawabin godiya ga manyan bak'i ,kunsani base nafad'iba,khairat gwalli da iyayi bawanda batayiba me hoto se d'aukarta yakeyi ,har tagama Fatima ta amsa tunda Fatima tafara mgn hankalin wani d'an majalisa me wakiltar Kaduna south,yadawo kanta sosai ta burgeshi shigowarshi kenan yatarar tana mgn,beji Lokacin da Khairat tai nataba.

Koda aka tashi agurin dinner da sauri yasa wani excode d'inshi yakaiwa Fatima wayarshi yace tasa mishi number d'inta amman be fad'i kowaye yaturoshiba kawai yace wani bawan Allah, Fatima ba wulak'anci amsa tayi tasa number tayi flashing anata wayar,Khairat wacce haushin rashin kasuwar datayi yacikata Masifa tadunga yiwa Fatima akan me zata bada number d'inta ga wani banza,Fatima bata kulataba Illa janta da tayi su tafi gida,dagudu me hoton dayayi hotunan bikin yak'araso gurinsu gaishesu yayi sannan yafad'i abinda yakawo shi Wai Khairat yake so😜.ay Khairat rushewa Tay da kuka tashiga tsine mishi tunda yace yana sonta,Fatima ko inbanda dariya ba abinda takeyi dakyar tajata Suka tafi gida.

Maman Yusuf

SURBAJO

πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€
       *SURBAJO*
πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€


Zahra Muhammad Mahmud


Kuyimin afuwa masoyana wlh raina ne yab'aci Shiyasa na kula.Amman Namuku alkawari bazan sake kulasuba  kugafarceniπŸ™πŸ™πŸ˜­


*Dedicated to, faty axland,rufaida umar, sadnaf,seemaluv,ummu yusura,maryam s bello,duka members na pml this page is yours love you all with all my heart😍😍😍😍😍*


*pure moment of life writers*
         *p.m.l*


*page 91-95*


Al-ameen binsu yayi d'aki dukansu kowacce yay mata fad'a,yaja musu kunne sosai yanuna musu b'acin ranshi,hak'uri sukai ta bashi dakyar ya hak'ura suka koma zamansu kamar da.


Yau Surbajo ce da girki dan haka tun safe take ayki sabida sunk'i yarda ad'aukomusu me ayki ba yarda beyi dasuba amman  fafur sunk'i yarda, se azahar tasamu tagama kintsa komai,da sauri tashiga wanka tafito ta shirya acikin wasu shegun kaya tayi kyau ba kad'anba,d'akin Al-ameen tanufa sabida yakira ta yace mata yadawo.tana shiga da gudu taje tarungumeshi takaimishi kiss, rungumota shima yayi yana Murmushi yace,


"Haba Baby wannan runguma haka ay Seki karyani,koda yake John cena ce ke bakyawa mutum dukan rashin imani",yafad'i yana dariya duka takaimishi sannan tasa kukan ahagwaba tace,

."Wlh bazan yardaba nice John cenar?,kai shikenan kafi son mukyale su suzo su wargaza mana gida, muna zaman lfy su kunno mana bala'i wlh k'aryarsu dole mud'au mataki",tafad'i tana murgud'a masa baki .


Dariya abun yabasa Dan haka rungumota yayi suka fad'a gado yana fad'in,


"Da kyau tawan Shiyasa nake sonki bakya d'aukar non sense, dan haka nima bari nad'au mataki anan, "romance d'inta ya shigayi kota ina tun tana tureshi harde Itama tabi yarima akasha kid'a.

Seda komai yalafa sannan suka sake wani wankan suka shirya suka fito zuwa dinning inda Aisha Itama fitowarta kenan, d'auke da Hanif  d'ayan hannun rik'e da hannun Yusuf,cin abinci sukayi cike daso da k'aunar junansu.



Rayuwa taci gaba da tafiya cigaba ta ko ina zuwa yake musu komai tare yake musu ba banbanci, amman matsayin Surbajo aranshi dabanne yana mata son
 dashi kanshi besan
 iyakarsa ba, kuma Itama haka ko kad'an bata had'a soyayyarshi data kowa, iyayenta yana ganin darajarsu haka Itama tana ganin darajar nasa iyayen, rushe gidansu yayi a rugar  yamusu gini na zamani dede da rayuwarsu,sannan yabasu jari me kyau dansu dunga sana'a, Surbajo har rasa bakin godiya tayi,sede fatan gamawa da duniya lfy data dunga yimasa.


B'angaren Aisha ma rushe gidansu yasa akayi akayi musu gini nagani nafad'a yaba mamanta jari me yawa dan ta dunga juyawa Tana kulawa da yaranta, Wanda hakan yasa Aisha K'ara nadamar abinda ta aykata masa abaya sosai tayi masa godiya har tana kuka.


Surbajo tasake samun wani cikin,Allah sarki Aisha murna takeyi fiye da ma Surbajon, tattali da kulawa daga Aisha har Al-ameen babu irin Wanda basayiwa Surbajo,tun cikin nak'arami Aisha tafara siyan kayan Babies tana tarawa unisex, Surbajo har dariya take mata.


Cikin na wata takwas sukaje scanning akace musu Baby girl ce,Wayyo dad'i rasa inda zasu sa kansu sukayi dan murna.


Siyayya suka shigayi kamar hauka don murnar Baby girl dazasu samu, basu da hira Seta cikin ahaka har Allah yasauketa lfy, tahaifo ta mace me kama da ita sak,babu inda ta barota har gwalo suka dunga yiwa Al-ameen na rashin d'aukoshin da Babyn tayi.

Ranar suna baby taci sunan maman Surbajo, wannan Karon harda Ard'o seda yazo suna jin ansama Babyn sunan masoyiyarsa,suna kiranta da Hanifa.

So da k'aunar da Al-ameen ke nunawa iyalanshi abin koyine ga duk magidanci kud'i basusa yarasa lokacinsuba duk kulawarsa nakansu bashida Lokacin komai senasu da iyayensa.

Lokacin aykin hajji yazo dukansu yabiya musu ta international suka tafi harda yaransu, sunyi addu'oi sosai Akan Allah yaba Aisha haihuwa domin Alfarmar Annabi da Alqur'ani.


Haka ranar tsayuwar arfa ma suka tsaya gurin yin addu'ar,suna kuka Surbajo tafi kowa yiwa Allah kukan yaba Aisha haihuwa domin girmansa.

Lokacin dasukaje d'awafin bankwana da kyar Al-ameen ya b'anb'are Surbajo ajikin Ka'aba tana kuka tana sake rok'on Allah, ahaka har suka dawo gida Nigeria kullum addu'arsu kenan.

Maman Yusuf
πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€
         *SURBAJO*
πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€


Zahra Muhammad mahmud



*This page is dedicated to Zahra Muhammad Hausa novels group's nagode da irin soyayyar dakuke nunamin wlh acikin masoyana kune first Allah yasa yadda kuke sona Allah yasa inna mutu ku nunamin irin wannan soyayyar gurin yimin addua ngd banda kamarku yan uwana  sonku ajinina yake love you all from the bottom of my inner heart.😍😍😍😍😍😍😍*


Na jinjina muku..


Mrs fawwaz
Anty khady
 garkuwa
fareeda
feedyluv
Maman sultan
Zee yabour
hafsey
Momyn janan
Maman ihsan
      Kunada yawa wainda kuka dace a jinjinamuku Wanda bankira sunanshiba afuwan abinne da yawa mutuwa tashiga kasuwa,Allah yak'aramuku basira,yakuma d'aukaka pml up up up.   p.m.l backward never insha Allahu.


*pure moment of life writers*
           *p.m.l*


*last page*


*page 96-100*


Allahu gafurur raheem watansu biyu da dawowa Allah yaba Aisha ciki zokuga Surbajo har azumi tayi na nuna godiyarta ga Allah daya amshi addua'rsu,Al-ameen yayi murna sosai itako Aisha harda kukanta gurin nuna godiyarta ga Allah.

kulawar da Surbajo take bata abin gwanin Sha'awa dole su burgeka duk abinda Aisha takeson ci shizata bata ko menene, dayake cikin Aishan me kwad'ayine abubuwa da dama se anbar kaduna za'a samo mata shi in kwad'ayin abunda ba lokacinshi bane a kadunar ya motsa mata.ko kad'an basa gajiyawa da hidimarta wanda ita godiya kawai take musu da fatan alkhairi.

Cikin Aisha se girma yake wanda girman cikin har tsoro yake ba su Surbajo sabida girmane na sose,gashi lafiyarta k'alau ba
ciwon komai se na kwad'ayi gashi yanzu tazama rumbu cin abinci kamar hauka intaci kuma takasa tashi  sesun d'agata.

Watan cikin bakwai suka kwasheta zuwa scanning dan su girman cikin ya tsoratasu,koda sukaje cemusu akayi komai normal kawai de twins ne a cikin.

Wayyo dad'i πŸ’ƒπŸ’ƒSurbajo sujjada take yi tana k'arawa ga ubangiji shiko Al-ameen duk girman Aisha da cikinta be hanashi d'agata ba yana murna.

Daga gurin scanning kasuwa suka wuce suka barta a mota suka shiga wani boutique na babycare suka shiga jidar kaya kamar hauka,daganan gida suka nufa.
Har walima seda sukayi dan murna inda akai addu'ar Allah ya sauketa lfy.

Watan haihuwarta yatsaya kullum cikin addu'a suke Allah ya raba Lfy, wata jumma'a Aisha ta tashi da ciwon nak'uda da sauri suka d'auketa zuwa asibiti.

Da isarsu labour room akasata, Surbajo kamar zatayi hauka dan tausayin Aisha, addu'a kawai sukeyi dan shima oga hankalinshi atashe yake.

Suna nan tsaye wata nurse tafito tamusu albishir data haihu Lfy ansamu twins duka mata,rungume juna sukayi Surbajo da Al-ameen suna nuna farincikinsu ga Allah.

Bajimawa aka fito da me jego da twins d'inta kyawawa dasu aka kaisu d'akin hutu.Surbajo tunda ta d'auki yaran kasa ajiyesu tayi sabida kyan da Allah yay musu kuma abin mamakin yaran da Surbajo suke kama kowa seda yayi mamakin hakan.

Aisha kallon Surbajo tayi murya araunane tace,

"Sister nagode da addu'ar ki gareni,wlh base kin ce kina k'aunataba inda banyarda ke me sona bace yanzu dole nayarda duba da kammanin da yarannan sukeyi dake, nayi imani inba nagartacciyar soyayya hakan bazata yiwuba,nagode miki sister da addu'ar ki gareni Allah ya rabaki da bak'incikin duniya da Lahira,"tafashe da kuka da sauri Surbajo tamik'awa Al-ameen yaran tarungume Aisha tace,

"Haba Aunty yau ranar murnace agaremu ba kukaba Allah ya amshi addu'ar damuka dad'e munayi danhaka godiya kawai zamuyi masa, kimance da komai Aunty na ni mesonkice."

Koda aka Sallamosu Surbajo ce d'auke da yaran tun kan su k'araso gida gidan yacika da y'an uwa kowa murnar haihuwar su twins yake.

Al-ameen yanajin son yaran har zuciyarshi badan komaiba sedan Kama da Surbajo dasukeyi bame kallonsu yace ba ita ta haifesuba, Allah Kenan.

Ranar Suna Surbajo ba k'aramin mamaki tayiba,
   dataji yaran duka sunanta Aisha tace asa musu d'aya Zahra d'aya fatima suna kiransu da mamah da mimah, amman Al-ameen me suna zahran Surbajo yake ce mata yayinda ita kuma yaci gaba da kiranta Babynsa.Surbajo godiya tadunga yiwa Al-ameen da Aisha abisa karar dasuka yimata.


Rayuwa taci gaba da tafiya inda Ahalin yanzu Surbajo tagama university d'inta Amman Al-ameen yace bazatayi aykiba,bata musaba ta hak'ura,Aisha nakan nata karatun dan itama tuni takoma makaranta,Yaransu gwanin Sha'awa bame gane wannance Mamana acikinsu sabida duk kulawa d'aya suke basu.

Al-ameen hankalinshi akwance na iyalanshi ma haka so da k'aunar dake tsakaninshi da Surbajo se son barka duk da yana b'oyewa gudun kar ran Aisha ya b'aci,amman son da yakewa Surbajo gagara misaline.


ina labarin su Ruky?

Ruky tunda suka bar gidan Aisha da wata uku tafara jin canje canje ajikinta dan haka ta nufi asibiti gwajin farko aka bata sakamakon HIV,yanke jiki tayi tafad'i sumammiya Gado aka bata a asibitin.Zuly nasamun labari tazo asibitin tagaida Ruky kamar abin arzik'i daga k'arshe se cewa tayi.

" Wannan k'awance  namu ina sonshi tunda gashi nayi nasarar saka miki ciwon danake d'auke dashi."daganan takwashe labarin komai tafad'a musu tana dariya, Maman Ruky shak'e Zuly tayi kamar zata kasheta tana yimata Allah ya isa,likitoci sunkasa kwaceta a hannunta dan haka suka kira police sukayi gaba da Zulyn.

Ruky ko kuka take me tsanani tashiga barin wasiyya tace ma mamarta tanemarmata yafiyar Aisha tasan hakkintane yake bibiyarsu don Allah tayafemata,ranar Ruky bata sake kwanan duniyaba tace ga garinku bayan tayi kalmar shahada.Allahu akbar Allah nason masu tuba Allah kasadamu da rahamarka dan darajar Annabi da alqur'ani Ameen.

Zuly ko kotu aka shigar da ita k'ara inda aka yanke mata d'aurin rai da rai agidan kaso,gamida horo me tsanani har iya k'arshen rayuwarta. Duniya kenan shiyasa akace abinda kashuka shi zaka girba Allah yasa mudace Ameen.


Su Aisha dasuka sami labarin mutuwar Ruky har gida sukaje gaisuwa ananne mamar Ruky take sanar da Aishan sak'on Rukyn,kuka Aisha tasa tace,

"Wlh nayafe mata duniya da lahira Allah yajik'anta yakyauta namu zuwan,"
godiya yan uwan Ruky sukai tayiwa Aishan.

To Ruky Allah yajik'anki yasa kin huta ya yafemiki kurakuranki.

Surbajo uwar biyu yanzu haka wani cikinne ajikin Surbajo tsoho yafi na Aisha girma scanning na farko aka shaida musu yan biyu ne duka mace da namiji,fad'in murna da farincikin da Al-ameen da Aisha sukayi page din yayi kad'an se fatan Allah ya sauketa Lfy.

Tahaihu  Lfy inda yaran suka ci sunan iyayen Al-ameen. So da k'auna agurin Al-ameen da Surbajo abin fatane ga kowacce mace agidan mijinta.


*Godiya ga Allah subuhanahu wata'ala daya bani ikon kammala wannan littafi nawa me suna Surbajo.ya Allah kuskuran danayi kagafartamin wa'azin dake ciki gamu mata masu zafafa k'iyayyar kishiya Allah yasa mata sund'auki darasin, maza mata masoyana ako ina kuke afad'in duniya me surbajo na k'aunarku harcikin ranta Allah yabarmu damasu son mu ameen wandama baya sonmu Allah ka jarabceshi da sonmu,Allah yazaunar damu cikin aminci. Kubiyoni cikin sabon littafina mesuna CIN AMANA KO FANSA*

NGD


maman Yusuf love you all πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹

SURBAJO

πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€
          *SURBAJO*
πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€


Zahra Muhammad mahmud




*pure moment of life writers*
          *p.m.l*



*page 83-84*



Al-ameen ya'isa Abuja Lfy Kai tsaye gidanshi yanufa masu gadin gidan sunyi mamakin ganinshi sabida ganin ba'a jimaba da kawo madam.

Gaisheshi sukeyi amman ko takansu bayayi cikin gidan yashige,afalo yasameta akwance Yusuf kuma na wasa,tayi mamakin ganinshi amman seta d'auke kanta daga kallonshi,k'arasawa yayi kan kujerar datake kallonta kawai yakeyi Amman ita ko kallo be ishetaba sema rufe idonta datayi.

'Haba Baby meyasa zakimin haka don Allah? kinsan yadda kika d'agamin hankali kuwa,ay ina ganin bahaka yadace kiyi gurin nuna fushinki ba magana yadace kiyimin sena gyara,amman matakin dakika d'auka wlh yatashi hankalina,"yaruk'o hannunta ay kamar jira take tamik'e tsaye afusace, takwace hannunta tafara magana cikin fushi,

"Wato kama maidani karya ko?banida zuciya a k'irjinane aka fad'amuku? koni akace muku tinkiyace wacce batasan ciwon kantaba? any way ba laifinku bane laifinane dana karya farashina yay arha da yawa, nayi muku kara wacce ni kaina nasan nayi namijin k'ok'ari Wanda duniya ma taji seta yabeni bare ku danayiwa,matarkace ban hanaku kuyi duk abinda kukesoba shiyasa ma nabaku guri danku sake dakyau,inde bawani bak'in cikin kabiyoni ka k'aramin ba pls get out from my side,"tafad'i tana nunamasa k'ofar fita.

Al-ameen mutuwar tsaye yayi yana kallon Surbajo cike da mamakin kalaman dasuke fitowa daga bakinta, tabbas yasan Surbajon shi tana da fad'a amman be d'auka shima zata iya masa ba ya bud'e baki da niyar yayi magana takatseshi da cewa,

"I said get out from my side now!!!!"tafadi cikin k'araji,

Tunaninshi ya karu akan nada yana ganin anya Surbajo bata da Aljanu kuwa shi besanta da rigima haka ba,kasa motsi yayi a inda yake bare yay tunanin bin umarninta.
Ganin bashi da niyar fitane yasa Surbajo fara jifanshi da duk abinda yazo hannunta tana kuka ta fadin,

"Why why?mutane kuka fiye son kanku da yawa?,meyasa jama'a yanzu basu da buri daya wuce su rama cuta ga wanda yay musu alkha'iri?, meyasa........"kukane yaci k'arfinta ta zube agurin tana kuka.

Al-ameen beyi yunk'urin hanata ba dan tabbas yasan yadda take da kishi kuma ta iya yimusu wannan karar dolene ranta ya b'aci da abinda sukayi mata.jiki a sanyaye yakarasa inda take yarungumota jikinshi yana rarrashinta da duk wata kalma dayasan tana sata nishadi sosai yake rarrashinta seda yajima sannan ta hakura ta dena kukan,mikewa tayi ta dauki Yusuf sannan takai dubanta gurin dayake tace,

"Hak'uri kabiyoni kabani to na hak'ura seka tashi ka koma kaduna kar tajika shuru,yazamana kayi laifi,kuma dama ay saura sati biyu hutunka yak'are,dan haka ka koma can kagama hutun,inkakoma bakin ayki kadawo nan d'in".

"Haba Baby meyasa zaku dunga yimin hakane? da girma na agari amman ace kun sani agaba kunmaidani kamar wata kwallo kowa da salon dayake bugani,Aisha ta koroni gurinki kema yanzu gashi kin korani gurinta, bakya ganin kamin nakai kaduna yanzu dare zeyi sosai amman ko ajikinki meyasa kike son zama mara tausayine?,pls kibarni na kwana da safe sena tafine."

"Tab'd'ijan ay wlh sede kafad'i duk abinda Kaga dama amman wlh bazaka kwana agidannanba inko kace seka kwana to wlh ni bazan kwana acikiba, dan haka kajuya katafi dannasan aranka sokake katafin gulma ce kawai irin taku ta maza masu bakin ganga Kaga kawuce ni na rufe k'ofata".

Murmushin taka'ici yayi,yajuya yafice daga gidan,hotel yakama yakwana washe gari yawuce kaduna,shi abunma dariya yake bashi wato da gaske ne kenan zancan da maza sukeyi nacewa in matanka suka had'a kai to wlh ubanka zasuci, shide ko ba haka bane shi yayarda tunda gashi sanadin had'in kannasu kowa batason shiga hakkin kowa shi Kuma sun maidashi kamar ball wannan ta buga ta ba wannan.

πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€
         *SURBAJO*
πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€


Zahra Muhammad Mahmud

*this page is dedicated to Muhammad indimi family  more especially Presido Adama,maryam,hauwa,Allah yakareku a duk inda kuka shiga nagode*

*pure moment of life writers*

      *p.m.l*


*page 85-86*

Ya iso kaduna lfy a kitchen yasamu Aisha tana wanke wanke,tabaya yaje ya rungumeta yace,

"Ta honey me ake tanadarmana ne haka",da sauri tajuyo tana kallonshi cike da mamakin ganinshi zatayi mgn yarigata,

"wlh koroni tayi ko gidan bata bari nakwana ba wai dole sena dawo gurinki nasan cewa zakiyi Meya dawo Dani yanzu to koroni akayi kuma wlh bawacce zata K'ara korata na koru,nadawo nan bayan Sati biyu zantafi laifin damuka yimata ta yafe, so banason wani dogon turanci,"yafad'a yana d'aure fuska gudun kartaga k'ofar rainashi.
Abun dariya yaba Aisha ganin yadda yake kumbura, janshi tayi suka koma d'akinshi taimakamasa tayi yayi wanka yashirya suka sakko suka ci abinci sannan yakira Surbajo awaya bayan sungaisa yaba Aisha nan fa suka shiga hira bame cewa kishiyoyine, seda kud'in wayar yak'are suka hak'ura.


Rayuwar su taci gaba da tafiya Cikin so da k'aunar juna babu meson ganin bacin ran d'an uwansa.babban fili Al-ameen yasiya a Kaduna a anguwar governor road yasa aka gina masa gini nagani na fad'a gidan samane akayi part uku amman anyi babban falo tsakiyar sannan se step Kowanne b'angaren danashi anyi kuma k'ofofi ta waje wanda kowa zefita yashigo batare da wani yaganshiba.

Dukiya yazuba agidan bata wasaba ba abinda babu harda garden da swimming pool da filin ball madaidaici kai komai de yaji, cikin Surbajo na wata tara suka tare a gidan ita da Aisha yayinda shima yanemi transfer zuwa Kaduna da ayki, gidan inka shiga kaga yadda kowa ke tattalin kowa abun seya burgeka babu kishi na fili agidan sede na b'oye wanda a ko'ina akwaishi,

Yanzu Yusuf yakoma hannun Aisha Itace keyimasa duk abinda yakeso,hakan bak'aramin dad'i yakewa Surbajo ba haka shima uban tafiyar,
Wata safiyar laraba Surbajo ta tashi da ciwon nak'uda Wayyo Jama'a zokuga Aisha zaka rantse da Allah Itace take nak'udar dan Surbajo ma tafita dauriya, ko a asibiti dasukaje haka taita rusa kuka harse da Allah yasauki Surbajo lfy inda tasake haifar namiji zokuga murna gurin Al-ameen jiyake kamar ya goya Surbajo dan dad'i.


Ranar suna yaron yaci sunan baban Aisha suna kiranshi da hanif,kukan da Aisha tayi na godiya ga Surbajo baya fad'uwa rasa inda zata sa hanif tayi sonshi take fiye da kanta jitake tafi Surbajo sonshi har tausayinta Surbajo tadunga Ji, yayinda taci gaba da addu'ar Allah yaba Aisha haihuwa Itama taga d'anta .

Duk wata kulawa da dawainiyar yaran Aisha ce keyi kullum  yayinda Surbajo itake ke yimusu girki kullum gami da gyaran gida sam ta hana Aisha yin komai d'akinta kawai take gyarawa se kuma na Al-ameen ranar datake da girki,kai dole Rayuwar gidan ta burgeka, ko ruga Surbajo zataje tare suke zuwa haka Itama in zata gidansu.wani lokacin har mantawa suke waye me girki acikinsu se shine ke tuna musu wacce keda girkin.duk abinnan Al-ameen jin surbajo yake tazama shi yazama ita dan yasan zaman lafiyar gidanshi yasamune ta dalilinta son dayake mata ko da wasa baza'a had'ashi dana Aisha ba ji yake in yarasa Surbajo shima yagama ayki.


Maman Yusuf
πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€
        *SURBAJO*
πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€


Zahra Muhammad Mahmud


*this page is dedicated to my fans on facebook thanks for the care and support*


*pure moment of life writers*
          *p.m.l*


*page 87-88*


Waiwaye adon tafiya


Ruky tunda ta auri baballe bata tab'a sanin meye sana'ar saba.kullum cikin cin dad'i suke hankalinsu akwance kwatsam wani dare y'an sanda suka dira agidan su abin yabata mamaki dataji suna zargin baballe da laifin fashi da makami har sunshiga gidan wani Alhaji sunyiwa y'arsa fyad'e,shine aka kama sauran suka tonashi tanaji tana gani aka tafi dashi police station.

Kotu aka shigar dasu K'ara inda aka yanke musu hukuncin Kisa ta hanyar harbi da bindinga bayan Kotu ta kwace duk wata kadara dasuka mallaka, Ruky haukane kawai batayiba tana gani aka harbe mijinta wanda tafiso fiye da rayuwarta,tashiga halin k'unci da bakinciki dole takoma gidan iyayenta da zama domin yin takaba.

Zuly kuwa taci gajiyar soyayya domin cutar zamani musa yad'ebo ya shafa mata tana cikin mawuyacin hali gashi yak'i dena halinnashi yace seya shafa ma mutane da yawa shima, Zuly Itama fatanta kenan tashafawa Jama'a acikin burinnata shine aminanta yadace tafara sawa,wato Ruky da Aisha.


Yau gidan su Ruky Zuly taje da niyar yimata gaisuwa, bayan sungaisa suka shiga hirar duniya,Ruky tamik'e zata fita,carab Zuly tace," ina zuwa kuma muna hira?"

"Kinga wallahi yaro zankira na aykeshi yasiyomin reza Zan yanke farce na sun taru,"
Murmushi najin dad'i Zuly tayi,sannan tace,

"lah karki bata kudinki Inde reza ce inada ita ajaka sabuwa zauna ma na yanke miki farcen",Abun yayiwa Ruky dad'i bamusu ta zauna Zuly tafara yankemata farcen da rezar data yanke hannunta jininta yashafa dama tayine dan tayi amfani da ita gurin aykata manufarta,tana Cikin yanke mata ta yanke ta da gangan nanko jini yasoma tsartuwa agigice tasaki hannunta kamar gaske tafara kuka wai bata sani bane,murmushi Ruky tayi tace,"haba kawas dan tsautsayi yafaru shine kike kuka Wlh karki damu kanki bari nasa kalanzir."
Ranar wuni Zuly tayi agidan su Ruky inda a karshe suka tsaida shawarar Sati biyu masu zuwa Lokacin Ruky tafita takaba zasuje gidan Aisha subata hak'uri amman zuciyar Zuly ba haka bane manufarta dabam.


Aji dad'i


Yaude Aji dad'i tasha alwashin sake kiran Al-ameen, Lokacin data kira Surbajo ce Kusa da wayar Al-ameen yafita training, da kamar karta d'auka cande ta d'aga muryar mace taji tana fad'in,

"Haba namijin duniya don Allah Kadena wulak'antani wlh sonka nakeyi ni ko bazaka yimin komaiba don Allah Ka kusanceni ko so d'ayane wlh na kwad'aita dakaine Shiyasa."

Hankalin Surbajo ne yay mugun tashi kashe wayar tayi, dabara ta fado mata ta tura text da cewa,

"Tunda kin takuramin kizo kisameni agidana nikad'aine agidan kizo yanzu kuma namiki so d'aya bazan sakeba," tatura mata gami da Address. Lokacin da sak'on yashiga wayar Aji dad'i jitayi kamar tazuba ruwa ak'asa tasha fad'i take,"wato nid'in mesa'ace ashe rabon sake ganinshine yakawoni Kaduna gaskiya nagode wa Allah,"tashi tayi tashirya cikin wasu tsinannun kaya tasha magungunan tsumi harda na matsi sabida aji komai zam zam. Kai tsaye gidanshi ta nufa.

Surbajo ko tana gama tura text d'in d'akin Aisha taje da gudu ta sanar da ita zasuyi bak'uwa da manufar zuwanta ,nanfa suka ruga da gudu zuwa kitchen domin tarbar bak'uwar tasu😜


Maman Yusuf
πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€
         *SURBAJO*
πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€


Zahra Muhammad mahmud


*INA KUKE MARASA AYKIN YI SENA GULMA?KUZO GA AYKI NA SAMAR MUKU, TUNDA NAGA RASHIN SHINE YASA KUKA TASA NAMANA D'ANYE KUNA CI.NAYIWA INDIMI FAMILY DEDICATION YASA KUNKASA ZAUNE KUN KASA TSAYE TSOHON BASIR YA MOTSA TO GAWANI SABO*

*THIS PAGE IS DEDICATED TO ALHAJI ALIKO DANGOTE FAMILY ALLAH YAY MUKU JAGORA AKOINA KUKE A FAD'IN DUNIYA NAGODE*


*pure moment of life writers*
           *p.m.l*



*page 89-90*


Duk abinda yadace su tanadarwa bak'uwar tasu shi suka tanada.suka dawo falo suna jiran isowarta.


Aji dad'i tunda ta iso k'ofar gidan yawunta ya k'afe sabida kyan da gidan yay mata,take zuciyarta ta ayyanamata dama ta auri mamallakin gidan.koda tazo gurin sojojin dake gadin gidan basu hana ta shigaba sabida madam tace zasuyi Bak'uwa in tazo su barta ta shiga.

Shigewa tayi cikin gidan tana wani karayraya ita adole tazo kwartanci, cikin falon gidan tashiga inda megadine yanuna Mata hanyar,

Su Aisha ko jin motsine yasa suka tashi da gudu suka b'oye a cikin labulen bakin k'ofar shigowa har ta shigo bata Lura dasub, kan kujera taje tazauna tadora k'afa d'aya kan d'aya aka k'ara baza gashin atachimen d'in datasa tana taunar cingom ji tayi kamar alamar akwai mutum atsaye akanta da sauri ta juyo zabura tayi tamik'e,ganin Aisha da Surbojo kowa d'auke da muciya sun nufota neman hanyar gudu take amman ina sun cimmata ayko nan suka shiga kirb'a mata muciya ta ko ina,ihu take tana neman taimako Amman ina babu me cetonta,dukanta suke bada wasaba, daganan suka kwantar da ita ta k'arfi suka yimata matsi da garin barkono wani azababben ihu tashigayi bana wasaba ga jikinta duk inda suka fasa seda suka cikeshi da garin yaji Aji dad'i ihu take har numfashinta na d'aukewa.
    Dede lokacin Al-ameen yashigo gidanshi ganin masu gadi yayi tsaye cirko cirko abakin k'ofar falon gidan tambayarsu yashiga Yi  akan abinda ke faruwa, nan suka shaida mishi bak'uwa ce tashigo gidan yanzu shine kuma suka jiyo kukanta ga kuma sautin dukanan sunyi sunyi su bud'e k'ofar sunkasa,da sauri Al-ameen yafara dukan k'ofar yana kiran sunansu amman ina ba wacce ta kulashi cigaba sukayi da operation d'insu, ganin bazasu bud'ebane yasa yabi ta kofar part d'inshi wacce d'azu daze fita tanan ya fita kuma besa key ba, dagudu yabi hanyar yak'araso falon ganin abinda sukeyi bak'aramin mamaki yabashi ba tunaninshi me yakawota gidanshi?,tayama tasan yadawo kaduna?, ganin baze samu amsoshinbane Yasa yaruga dagudu yayi kansu dakyar yakwaceta a hannunsu se zunduma ihu take iya k'arfinta tana tsalle tsalle sabida yajin da suka yimata matsi dashi,Surbajo ce tace afusace,

"Dan kan ubanki kad'an muka yimiki dan wlh yau so mukayi muyi miki abinda ko sunan namiji kikaji an ambata sekin firgita bare har kice zaki yi mu'amala dashi shegiya tsinanniya me lalata mazan mutane,"Aisha ta amshe da cewa,

"Bar matsiyaciya de muna nan muna tattalin mijinmu ke kinaso ki b'ata mana ginin damuka dad'e munayi wlh kinsha k'arya kuma koda wasa kika sake bin mijinmu wlh semun sauya miki halitta tsinanniya kawai,"

Al-ameen ne ya katsesu dacewa, "Haba ku kuwa yanzu abinda kukayi kunyi adalci kenan?yazaayi kukama y'ar mutane kuyi mata irin wannan izayar wannan ay zalincine ina laifin kuyi mata warning da baki amma shine harda irin wannan azabtarwa,"Aisha ce takatseshi dacewa,

"wato abinda mukayi munyi laifi ko ?sabida munmata hukuncin daya dace da ita shine har Kake cewa bamu kyauta ba to wlh semun mata wanda yafi wannan muddin takuma kallon mijinmu,"Surbajo tace,

"ke kika tsaya ma yimasa bayani wlh Aunty kawai kijawo mana ita muci gaba da cin uwarta inyaso seya zab'a ko mu ko ita," tana gama fad'in haka ta finciko Aji dad'i dake b'oye abayanshi suka ci gaba da shirgarta harseda suka karyata a k'afa duk yadda yaso ya amsheta yakasa seda suka gaji dan kansu suka kyaleta, suka wuce d'akin Aisha suna dariya suka barshi tsaye akan Aji dad'i wacce ko numfashi batayi, kiran driver dinshi yayi yabashi kud'i da shot note yace yakaita asibitin  sojoji kinkimarta driver yayi yanufi asibitin da ita wanda yake mallakin sojojinne me suna 44 kuma babu nisa tsakaninsu da asibitin.


koda aka kaita asibitin seda tayi kwana goma sannan ta ji sauk'i sallamarta akayi yayinda k'afarta dasuka karyata kuma akayimata D'ori aka bata sandar dogarawa,ta koma Abuja cike da danasanin sanin Al-ameen datayi arayuwarta tabbas tunda take bata tab'a danasanin karuwancin datakeyiba se yanzu dan haka had'a yanata yanata tayi takoma gaban iyayenta tanemesu gafara.

Shiko Al-ameen gaba ya d'aura da matan nashi inda sukuma suka maidashi mahaukaci,
inyashigo gidan suyi masa dariya inze fita su kwashe da dariya sunde maidashi kamar tab'ab'b'e abin yafara damunshi dan har tsarguwa yakeyi in suna dariyar se yad'auka wani abun suka gani ajikinshi suke dariyar har gaban mirror yasha tsayawa yana k'arewa kanshi kallo dan yaga mesuke wa dariyar.


Rannande ritsasu yayi afalon suna masa dariyar Surbajo ya damk'o yace,


"Yaza'ayi kumaidani mahaukaci kusani agaba kunamin dariya to wlh yau sekun ciremin abinda kukewa dariyar,"yafad'a rai ab'ace, dariyar suka sake tuntsirewa da ita suna nunashi sakin Surbajon yayi yakama dube dube ajikinshi, da gudu suka bar falon kowa ta gudu d'akinta tasa key,murmushin takaici yayi yawuce nasa d'akin yaganosu wato gasashi sukeyi dan yanuna b'acin ranshi akan abinda suka yiwa Aji dad'i.A ranshi yace, "to fita harkarku zanyi ko kunamin dariyar".


Yau kuma su Ruky ne suka dira agidan bayan bak'ar wahalar dasukasha kamin su gane kwatancen da'aka musu,dakyar megadi yabarsu suka shiga,, afalo suka sami Aishan a zaune tana wasa da Hanif da Yusuf, da sallamarsu suka shiga falon mamakinsu ne k'arara a idon Aisha kallon tsana da k'iyayya take binsu dashi har suka zauna. Suna zama carab Zuly tace cabd'i Jan kice kece kika koma nani d'in yaransu ken...... bata gama fad'in abinda tai niyya ba Aisha ta kifeta da Wani lafiyayyan  mari tasake k'ara mata wani, mamakine yahanasu yin wani yunk'uri, d'aga murya Aisha tayi tace,

"Sister ki fito munada bak'i Wanda yadace ayimusu sanitation a brain d'insu,"da sauri Surbajo tafito daga kitchen hannunta d'auke da muciya guda biyu dan tun ranar dasuka daki Aji dad'i suka yi meeting akan duk sanda d'aya yaji d'aya yakirashi akan suzo suyi sanitation to abun dukane yasamu dan haka Surbajo harda d'amararta tana zuwa falon tamik'awa Aisha muciya guda d'aya ayko batare da b'ata lokaciba suka rufesu da duka ta ko ina k'arar hayaniyarsuce ta tashi Al-ameen a bacci da gudu yafito falon ganin yak'in da akeyi afalon ba k'aramin mamaki yabashiba,dakyar yak'arasa gurin ya rabasu da kyar su Ruky se kuka sukeyi sabida dukan dasuka sha,Aisha tace,

"matsiyata marasa kunya wato har kuna da idon dazaku sake kallona da Sunan k'awance to daga yanzu bani baku kunyimin illar da har na mutu bazan manta dakuba kuma wlh bazan yafe mukuba kufice daga gidannan yanzu wlh,"jiki asanyaye suka fice a gidan ran Zuly yafi na Ruky b'aci sabida bata samu damar ida nufintaba.

shiko Al-ameen masifa yarufesu dashi dacewa,

"Wlh maganar dakuke d'aukomin tafara isata ace gidana yazama filin dambe ay dana sani tun farko anginamin filin wrestling agidan dannaga alamar Roman reigns and Dean Ambrose ne agidan yakamata agina muku filin dambe,"ko kallonshi basuyiba suka wuce d'akinsu

SURBAJO

πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€
         *SURBAJO*
πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€


Zahra Muhammad mahmud


*®Pure moment of life writers*
                *P.m.l*


*page 77-78*


       *Rasha*

Sun isa lfy tun a Airport suka tarar da motar ambulance najiransu da kuma wata personal car,suna sakkowa akasa Aisha a Ambulance d'in zuwa Asibiti su kuma suka shiga d'ayar motar suka bisu abaya.

Likitocin dasuka duba Aisha ba k'aramin fada suka rufesu dashi ba akan barinta da ciwo da sukayi yaci k'arfinta. Sude ba baka se kunne, angama yimata duk abinda yadace sannan aka sallami su Al-ameen,sabida ba'a jinya a Asibitin sede kazo kaduba Mara lafiya kawuce.

Hotel yakaisu me kyau sosai,d'aki biyu ya kama d'aya na Inna d'aya nasu.tunda suka shiga d'aki wanka kawai sukayi suka ci abinci, suka rama salloli kowa yabi lafiyar gado sabida sun gaji sosai.

Tunda sukaje Rasha jikin Aisha yafara sauk'i, kullum Al-ameen natare da ita yana bata kulawa sosai,Surbajo Ma ba'a barta a bayaba tana yi dede gwargwado gashi duk dare seta tashi tayi sallolin nafila akan Allah yaba Aisha lfy,cikinta bashi da laulayi shiyasa take samun damar yin komai,Inna ko har cewa take  ita bata ga amfanin zuwa da itaba sabida komai da yadace tayi Surbajo ce keyi se albarka take sa mata.

Abinda Surbajo takeyi game da Aishan bak'aramin farantawa Al-ameen rai yakeyiba sonta da k'aunarta kullum k'aruwa yake azuciyarshi ya yarda Surbajo me k'aunarsa ce ba kad'an ba shiyasa yabata wani matsayi a zuciyarsa wanda be ba kowaba se ita.

Satinsu biyu da zuwa Aisha ta farfad'o,numfashinta
ya dedeta shiyasa aka cire mata abun oxygen d'in da'aka samata kuma anrage mata yawon na'urorin da'aka baibaye jikinta dasu,lokacin suna gida ta farkan daga can asibitinne aka musu waya akan suzo ta farka. Al-ameen da Surbajo har karo suka dunga yi gurin fitowa daga d'aki shaf sun mance da Inna da Yusuf (dayake agurin Inna yake kwana,)driver suka sa yakaisu asibitin.

Aisha na ganinsu kuka ta rushe dashi ta runtse idanunta sabida bazata jure kallonsu ba,da saurinsu suka karasa inda take Al-ameen ne yarungumota jikinshi hawaye na zuba a idonshi shafa kanta yakeyi alamar tayi shuru,Surbajoma kukan takeyi taruko hannun Aisha tace,

"Lalle Allah yayi gaskiya da yace be saukar da ciwo ba seda yasaukar da maganinsa, Aunty Aisha bayi murnar samun saukinki karki ce zaki nemi gafarata nadade da yafemiki Allah yakara miki lfy da zaman Lfy,"tafadi tana sake rike hannun Aishan da kyau, dagowa Aisha tayi tana kallon Surbajo cike da mamakin kalamanta Wanda bata taba tsammanin zata furtasuba gareta,ahankali ta juyo da kanta gurin Al-ameen tana kallonshi shima ita yake kallo yana murmushi magana zatayi amman yarigata, Yace,

"Shshh banason kiyi mgn duk abinda zaki fada munganeshi dan haka kuma dukanmu mun yafemiki Allah yabaki lfy uwargidana kinji,"kukane ya sake kwacewa Aisha jin kalaman da yamata yakara sawa tanajin kunyarsu sosai.

"Aunty wai kukannan na menene ni kimin kud'insa nasiya kidena yimana asarar hawayenki a banza,"inji Surbajo.

Waigowa Aisha tayi tana kallon Surbajon data turo baki gaba alamar shagwab'a,rungumeta Aisha tayi tana kuka take fadin,

"Wallahi ke y'ar Aljannah ce Surbajo,babu kishiya irinki a wannan zamanin,base anfad'aminba wlh nasan kece silar da Al-ameen ya waiwaye ni sabida nasanshi farin sani inyayi fushi da abu baya waiwayarsa har abada nagode miki don Allah kiyafemin wlh sharrin shed'anne da kuma na k'awaye pls kuyafemin dukanku nasan na cutar daku kugafarceni,"tafashe da kuka me tsuma zuciya.

Rungumeta sukayi duka suna fad'in Sun yafemata duniya da lahira.


Ranar wuni sukayi a gurinta yayinda Al-ameen ya ayka driver ya dauko su Inna da Yusuf,Inna rungume Aisha tayi tana kukan farin ciki da Allah yatashi Aisha Lfy.



maman yusuf
πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€
         *SURBAJO*
πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€


Zahra Muhammad mahmud



*pure moment of life writers*
          *pml*


*page 79-80*


Sannu a hankali jikin Aisha ke k'ara warwarewa, wanda hakan faranta ran su Inna yakeyi kullum Surbajo natare da ita tana bata labarai dazasu dunga sata nishad'i sabida likita yace adena barinta ita d'aya gudun karta dunga tunani.

Surbajo shawara taba Al-ameen akan in ciwon zuciyar Aisha yagama warkewa meze hana suga likita gameda rashin haihuwar da akace bazata sakeyiba ko Allah zesa adace da Maganin anan.shuru Al-ameen yayi yana kallonta daga bisani yajawota jikinsa yarungumeta sannan yace,

"Baby wlh you are too good,zuciyarki me kyau ce Baby, Allah yamiki albarka yasa y'ay'an dazan haifa su d'auko kyawawan halayenki,narasa taya zan nunamiki ina sonki ni kaina banawa kaina irin son danake miki pls Baby kirik'eni amana duk wuya dun runtsi karki gujeni wlh narasaki nayi imani mutuwa zanyi bazan iya rayuwa babu keba pls,"yafad'i yana sake rungumota.

Rungumeshi itama tayi sannan tace,

"Dear Kenan,toni ay arayuwata banida abin danake so sama dakai, inasonka fiye da kaina haka zalika nima bazan iya rayuwa babu kaiba,babu wani k'unci ko tsanani dazesa nabarka insha Allahu you are my soulmate dan haka babu me rabamu se mutuwa,"kiss takai mishi a goshi ayko ruk'ota yayi suka shiga romancing d'in juna ta ko'ina sosai suke enjoying abinda sukeyin seda taga ze wuce gona da irine tayi k'ok'arin hanashi, shiko nuna mata yayi besan zancanba sabida itace ta tsokanoshi dan tunda sukazo garin betab'a kusantartaba sabida bata yarda setacemasa yazeyi haka su dasuke da marar lfy haka dole yake hak'ura,shiyasa yau yace besan zancanba seda ya moreta son ranshi dan har kuka tafara yimasa sannan ya kyaleta.


watansu guda a Rasha Aisha ta warke sumul sede d'an abinda ba'a rasaba,zancan matsalar rashin haihuwarta ma and'orata akan magani wanda sede fatan Allah yasa a dace.

Visa yamusu daga Rasha suka wuce saudiyya domin yin umarah,wayyo dad'i daga kan Inna da Aisha da Surbajo babu wanda beyi kukan ganinsa a saudiyyaba, nan suka duk'ufa yin addu'o'i babu kamar Aisha da tana d'awafi tana kuka tana rok'on Allah ya gafarta mata kurakuranta,in tafara d'awafin setayi bakwa'i so bakwa'i babu abinda take rok'o se gafarar ubangiji sam bata kwana a masaukinsu kullum a masallaci take kwana kuma ba bacci takeba se rok'on Allah se safiya tayi take zuwa masaukin tayi wanka tad'an kwanta ta huta,su Inna har fad'a suke mata akan tadunga ragewa tunda bacikakkiyar lfy garetaba, itade sede tayi musu murmushi dan yanzu Aisha gaba d'aya ta sauya ko magana batasonyinta sosai seta Kama.

Satinsu biyu a Saudi Arabia suka dawo Nigeria cike da so da k'aunar juna,a airport y'an uwane na nesa dana kusa suka zo tarbarsu abin yamusu dad'i sosai koni nayi farinciki direct gidansu aka wuce dasu,ga mamakinsu jamaa ne mak"il da gidan daddyn Al-ameen ya had'a musu walimah ta murnar dawowarsu,wanka kawai sukayi suka ci abinci suka fito gurin walimar anci ansha an godewa Allah taro yatashi lfy.

Da daddare har d'akin Aisha Surbajo taraka Al-ameen sannan tamusu fatan samun dauwamamman zaman lfy gabad'ayansu, sallama tamusu ta dawo d'akinta tana shiga d'aki tarushe da kuka sabida Surbajo macece me kishin mijinta daurewa kawai take Amman batason taga wata ta rab'i mijinta,gudun kar shed'an yazo yazugata ne yasa tashige toilet ta d'auro alwala tazo tafara kai kukanta ga Allah akan ya yayemata wannan azababban kishin dake damunta.

Maman Yusuf
πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€
         *SURBAJO*
πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€


Zahra Muhammad mahmud


*® pure moment of life writers*
                *p.m.l*



*Page 81-82*


Washe gari da sassafe Surbajo ta tashi ta had'a musu breakfast me rai da Lafiya,tajera a dining d'in falo,sannan  taje tayi wanka tayima Yusuf suka shirya tsab dasu,zaman jiran su Al-ameen sukayi su fito suci abinci.


Har zuwa k'arfe sha d'aya na safiya basu fitoba,abun yayiwa Surbajo ciwo sosai dan haka taja Yusuf sukaje suka ci nasu,d'akinta tadawo tahad'a kayansu duka tafita takira driver yazo ya d'aukarmata kayan,da sauri driver yagama kwashe kayan yasa amota kamar yadda ta umarceshi.

Rufe k'ofar part d'inta tayi taja hannun Yusuf suka fice daga cikin gidan, motar da driver yashirya kayansu aciki tanufa tana zuwa yabud'e mata k'ofar baya tashiga ita da Yusuf,rufe k'ofar driver yayi sannan yazagaya mazauninsa yazauna yace,

"madam ina muka nufa ne?".


"Abuja ta bashi amsa a gajarce".


Tada motar yayi suka fice daga gidan yakama hanyar Abujan,tafiya suke sosai cikin awa biyu suka shiga Abuja kai tsaye gidansu yakaita yasauke mata kayan masu gadin gidan suka shige dasu cikin gidan.


Sallama driver yamata yajuya yakama hanyar komawa kaduna.awanshi biyu a hanya ya isa gida lfy.


Surbajo koda ta koma Abujan ranta bedena yimata zafi ba dan har ga Allah yau sun b'ata mata rai bana wasaba,har kuka tadungayi na bakin ciki,tsoronta kar Al-ameen yace ze wulak'antata akan Aisha dan taga kamar yunk'urinsa kenan.


Su Al-ameen basu fitoba se k'arfe d'aya na rana shima kiran sallah ne yatashesu daga baccin dasukeyi,tun bayan dasukayi sallar asubah, sabida ansha love bana wasaba shine suke ramakon baccin da basuyiba
wanka suka shiga atare kowa yayiwa d'an uwansa wankan sannan Al-ameen ya d'auko Aisha suka fito shiryawa sukayi sunyi kyau sosai kowa yagansu ze d'auka sababbin amarene.seda sukayi sallah dayake tun a toilet sun d'auro alwalarsu,sannan suka sakko k'asa,se alokacin kunyar haduwa da Surbajo ta kamasu tabbas sunsan abinda sukayi be daceba ga inda ake so azauna lfy, jikinsu a sanyaye suka karaso falon ga mamakinsu abincine iri-iri Jere akan dinning,dakinta suka nufa suka fara nuking amman shuru baa budeba hakan yasa suka dauka sallah takeyi,juyawa sukayi zuwa gurin dinning din bubbudewa sukayi suka gani ananne suka fahimci taci nata nasune wannan,amman duk da hakan basu fara cin abincinba suna zaman jiranta,gajiya Al-ameen yayi dan haka wayarsa yaciro yakirata seda takusa tsinkewa daga can Abujan Surbajo ta daga kiran bayan ta dedeta natsuwarta tace,

"Hello Dear ina kwana kun tashi lfy?yajikin Aunty?".

amsawa yayi da cewa,

"Lafiya lau Baby,jikinta kuma da sauki,munzo muna nurking kofarki baki budeba ko lfy?,kuma yanzu jiranki muke a dinning shuru baki fito ba, pls kiyi sauri mana kizo yunwa muke hi."

amsa tabashi dacewa,

"Ayya karku damu kuci abincinku  mu munci namu nakune wannan,kagaishe da Aunty Aisha bazan sami damar fitowaba yanzu sabida naga gidan na sababbin amare ne yana dakyau abarsu su huta ako'ina nagidan,kasan sababbin aure abun se a hankali a gaban kowama raba abin kunya suke batare dasu sunji kunyarba,sabida cike suke da so da k'aunar juna mantawa suke da kowa inba junansuba nabarka lfy,"tana gama fad'in haka ta kashe wayarta gaba d'aya.

Wani zazzafan gumi ne yaketowa Al-ameen dajin zancan Surbajo,sabida shi bahaushe ne dole ya fahimci bak'ar magana Surbajo ta gasa ma'i,kunyar tace tasake kamashi tabbas basu kyauta mata ba duk da tana musu kawa'ici amman yau sunsa tafara fusata, dan tun suna rasha sede tabasu guri insuka soma rungume rungumen juna,ajiye wayar yayi asanyaye,Aisha ce takatse mishi tunani dacewa,

"Honey tayi fushi damu ko?"

gyada mata kai yayi alamar eh,shuru sukayi dukansu jikinsu ya mutu babu ma kamar Aisha wacce ta d'auki laifin ta d'ora akanta,dakyar suka ci abincin sannan Aisha ta tattare gurin dasuka b'ata ta kwashe komai taka'i kitchen bata fitoba seda ta wanke komai ta adana.

D'akin Surbajo suka koma suna ta nuking ganin taki bud'ewa ne yasa Al-ameen yace bari yaje gidansu yadawo maybe zuwa lokacin ta hak'ura ta bud'e k'ofar, rakiya Aisha tamasa har waje,Al-ameen mamakin inda aka ka'i motar da yay niyar fita acikinta yakeyi,d'aya daga cikin bodyguard d'inshi yakira yatambaya ina driver yaje da motar?,bashi amsa yayi da cewa,

"Nide naga madam takirashi yadebo mata kaya daga cikin gida yasa amotar sun fita amman bansan inda suka nufa back,"hankalin sune yay masifar tashi wayarta yakira akashe take kiran wayar driver yayi bugu daya yadauka yace,

"Hello, good day sir we arrived safely now am on my way coming back from Abuja,"katseshi Al-ameen yayi azafafe yace,

"Hey stupid where did you took my wife and my son,?where?"yafadi cikin tsawa wacce takusa sawa sitiyari ya kwacewa driver cikin rudewa yace,

"Am sorry sir is not my fault she is the one who permitted me to take her to Abuja,right now she is in Abuja sir,"

Kashe wayarshi kawai yayi ranshi ab'ace juyawa yayi yakoma cikin gidan shida Aisha yafasa fitar huci kawai yakeyi meyasa Surbajo zatayi masa haka? shi bawanda ma yafi jin haushinsa irin driver daya ka'ita,

Aisha ce ta matso tana tambayarshi,"me yafarune haka?ina Surbajon taje?ta tambaya hawaye nasakkowa daga idonta dan yanzu bata k'aunar b'acin ran Surbajo ko kad'an kamar yadda itama tasan bata k'aunar nata b'acin ran,amsa yabata dacewa,

"ta koma Abuja ne"ya fad'i kamar me shirin yin kuka.

Kuka Aisha tasa mishi akan wlh se yabi bayanta yau d'innan ita bazata iya jure zama da b'acin ran Surbajo ba "katafi nace!!!!!",tafad'i cikin k'araji tana kuka da gudu tajuya ta haura sama inda d'akinta yake ta kulle k'ofar d'akin tafad'a kan gado tana kuka,tabbas tasan sunka'i Surbajo bangone shiyasa tagujesu sabida ko da suke Rasha abubuwan dasuka dunga yi agabanta in itace akayiwa Wlh bazata yarda ba amman Surbajo ta dauke idonta, dole wanda suka mata yau yay mata zafi.

Al-ameen kanshi ne yasoma charge rasa wacce zebi yayi,bashida zab'in daya wuce yabi umarnin Aisha dan haka juyawa yayi yafice a gidan,da kanshi yake driving yad'auki hanyar Abuja.



safe journey  Angon Surbajo.


Maman Yusuf

SURBAJO

πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€
         *SURBAJO*
πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€

Zahra Muhammad mahmud

*PURE MOMENT OF LIFE WRITERS(P.M.L.W)*

*page 71-72*

Koda ya'isa gidansu still ranshi abace yake dak'yar ya iya yimusu sallama,

Hankalinsu tashi yayi dasuka gansa ayanayin dabasu saba ganinsaba, tambayarsa suke meyafaru dashi,seda yad'an natsu sannan yafad'amusu abinda yafaru, Dukansu bawanda be firgita dajin labarinba, Daga 'karshe fatan Allah yasa hakan shi yafi alkha'iri suka masa, inda Mahaifinsa ya'kara dacewa, "Ka rage saurin yanke hukunci cikin fushi",amsawa yayi da insha Allahu yadena.

Aisha dak'yar tamik'e tafara neman mayafinta kuka take kamar ranta zefita,ga hannunta dayake mata azabar ciwo ahaka tadaure ta hada iya abinda zata iya d'auka tabarmasa gidansa cike da d'umbin danasani, tabiyewa k'awaye gashi sunkaita sun barota,rasa ina Zata sa kanta tayi,
  Driving take amma ko gabanta bata gani Allah ne kawai yakaita gidansu Lfy, Tanayin parking da gudu tashige cikin gidan tana kuka me tsuma zuciya kan mamanta tafad'a, wacce ke zaune Tana yankan alaiyahu dasauri taajiye wuk'ar Tana tambayarta meke faruwa?,
  Cikin kuka Aisha ke fad'in,"wayyo Allahna Inna nacuci kaina nabiyewa sharrin k'awaye gashi yau sunkaini sunbaro,yau mijina yasakeni had'e da sakamakon bazan sake haihuwaba arayuwata",wani kukan tasake rushewa dashi, Mamanta jikintane yakama rawa kamar mazari jin zancan Al-ameen yasaki Aisha dak'yar ta'iya tambayar Aishan metayimasa?, nanfa Aisha takwashe komai tasanar da Inna, wani gigitaccen Mari Inna tawankawa Aisha har so biyu tuni Aisha tasoma ganin taurari sabida Marine bana wasaba, cikin 'bacin rai Inna tace,
"Aisha gaskiyar Aminune dayacemiki kanki kika cuta to wlh kannakin ko kika yiwa, Aisha yaushe rashin imaninki yakai haka ki iya kashewa mace y'a tun aciki keko mekike nema wandau Aminu yagaza gurin yimiki, wlh kinyi rashin mijin da keda samun kamarsa har abada azamaninnan, natayaki murna seki zo mujeru agidan arasa gane wacece uwar acikinmu, zancan bazaki haihuba kuma sakayyace Allah yama wacce kika zalinta".

Maganganun Inna sunshigi Aisha sosai take numfashinta yafara barazanar d'aukewa, kamin Inna tayi wani yunk'uri tuni Aisha tazube ak'asa sumammiya,
  Agigice Inna tayi kanta tana kiran sunanta Amman ina ko numfashi batayi, ruwa tad'ebo ta yayyafamata shima abanza, arud'e Inna tayi k'ofar gida neman taimakon jama'a,nan da nan  aka shigo akad'auki Aisha zuwa Asibiti.

Al-ameen kwanansa d'aya yajuya Abuja,
  Cike da farinciki Surbajo ta tarbeshi domin tayi murna da dawowar tashi,abinci masu rai da Lafiya ta gabatar masa bayan yayi wanka yashirya sannan suka dawo dinning yaci abincin,

Falo suka dawo suka zauna Surbajo na mak'ale dashi, yayinda Yusuf yana makaranta dan ansashi a makarantar,
Tambayarshi take,"dear meyasa kadawo da wuri"? murmushi kawai yamata dan bayason yafad'amata abinda ze d'agamata hankali,
  Daminshi tayi da tambayar, "dear nagama kasauya kamar baka cikin walwala meke faruwane? don Allah kasanar dani",

Ganin tashiga damuwane yasa,yakwashe duk abinda yafaru tasanar da ita,afirgice tamik'e daga jikinshi tana maimaita kalmar," Itace tayi sanadin mutuwar Babyna ?me muka yi mata da zafi har haka dazata za'bi rabani da abinda nafiso arayuwata? menayimata!!!?
  Durkushewa tayi Tana kuka Al-ameen behanataba yabarta tayi sabida zatafi samun sauk'i a zuciyarta,

Seda yaga tayi dayawa sannan yakamota yana rarrashinta ahankali hartadena kukan,seda take natsu sosai sannan tace,

"Dear sakin dakayiwa Aisha bedaceba sabida cuta de tariga data gama cutar damu babu wani abu dazamuyi mata murama, nide anawa ganin kayi hkr kadawo da ita dakinta zefi dan wlh sakinta bashine mafitaba kuma ni nayafe mata sauran tsakaninta da ran data kashene ranar gobe kiyama kuma kaima inaso kayafemata Don...... Marin daya wanketa dashine yasa takasa karasa abinda zata fada, hankad'eta yayi tafad'i ak'asa bebi takaiba yanunata da yatsa sannan yace cikin kakkausar murya,

 "how dare you Surbajo?she killed my princess and also she destroyed my happiness, and she make you suffer alot,then for all this, now you are looking into my eyes without fair asking me to forgive her  how dare you? That means my  happiness it's doesn't matter to you thanks you so much",
   yana gama fadin haka yajuya yafice daga gidanma gaba d'aya,Surbajo kuka ta rushe dashi anan gurin daya yardar da ita, Sam ita bataga aybin maganartaba dahar zeyi fushi da ita har haka, kukanta taci gaba dayi.

Maman Yusuf
πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€
         *SURBAJO*
πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€

Zahra Muhammad mahmud

*PURE MOMENT OF LIFE WRITERS(PML)*

*page 73-74*

Surbajo gajiya tayi da zama afalon tamik'e ta shige d'akinta.

Al-ameen ko tunda yafita yabar gidan ranshi a'bace yake,milonian park yaje domin yasha iska,gurin da ba hayaniya sosai yasamu yazauna yana tuno abinda Aisha da Surbajo suka masa ransa nak'ara 'baci,idonsa a lumshe yake yana jin dad'in iskar dake kad'ashi,sallamar da'aka masace tasa ya bud'e idanuwannasa.

Wata budurwace wacce shekarunta bazasu gaza ashirin da biyarba,sanye take cikin wata purple din doguwar riga irin me kama jikinnan,ta yafa wani d'an siririn mayafi akanta fari,fuskarta sanye cikin wani bak'in glass yayin da abakinta kuma tana taunar cwingum, ba laifi tana da kyau da diri dede misali, ita yagani tsaye akansa fuskarta d'auke da murmushi,cigaba tayi da cewa,

"In bazaka damuba please zan iya zama anan,"tanuna kusa dashi,shiko Al-ameen binta kawai yake da ido tun kamin yace ta zaunan harta zauna kusa dashi,dubanta yayi sannan yace,

"Baiwar Allah lafiya?zakizo ki zauna anan ko aykoki akayi?," wani shu'umin murmushi tayi gamida fari da idonta tace,

"Wlh kaso kad'an bani dariya wato ni ban isa inzo gunka zuwan kainaba sede idan aykoni akayi,to zancan gaskiya bawanda ya turoni gurinka,ganinka nayi da alamun damuwa a tattare dakai shiyasa nace bari inzo ind'ebemaka kewa watak'ila inyi nasarar rabaka da damuwar dake ranka."

Al-ameen kallonta yayi sannan Yace, "ni nace miki inada damuwa?,kuma inaga ay in ina buk'atar ad'ebemin kewa nafiki sanin inda yadace inje ad'ebemin d'in,dan haka inbazaki damuba kibar gurinnan nazo nasha iskane kinzo kintaremin so please kid'an barni na huta".

Wani irin juyi tayi wanda yatilasta jikinsu had'uwa,tak'ara matsawa sosai jikinshi,faruwar hakan ne yasa jikin Al-ameen mutuwa yakasa wani kyakkyawan motsi,magana tafara tana shafo gefen fuskarshi cikin salo na yaudara tana wani tutturo kirji gaba wanda harsuna gogar jikin Al-ameen d'in tace,

"Haba namijin duniya gaka de kamar kawaye amman kanaso kabada maza, ay soyayyace take sawa daga kallon mutum kagano abinda yake damunsa,nasan kana buk'atar kulawar mace awannan lokacin so please let me try my best wajen taimaka maka,"

Dakyar Al-ameen yace,"you are welcome once again thanks for the care and concern,"murmushin cin nasara tayi sannan tace,

"Sunana jameela amma friends d'ina suna kirana da aji dad'i,ina zaune anan garin Abuja badan komai ba sedan naji dad'i, so ihope zakayi joining d'ina domin kaima najiyar dakai dad'in dake tattare dani."duk maganarnan datayi tanayine tana shashshafo Al-ameen gami da yimasa abubuwan da dole duk namiji me lafiya se hankalinsa yatashi.shiko sha'id'anne yak'ara samasa jin dad'in abinda take masa shiyasa sam  beyi yunk'urin hanataba.cikin salo irin na rikakkun karuwai Ajidad'i tadunga yaudarar Al-ameen harseda yabata number wayarsa sannan yadauketa yamata shopping sosai sannan yakaita gidansu ita da wata k'awarta mesuna  Ayna'u cleaner.

Da isarsu k'ofar gidan yayi parking dan yace sauri yakeyi baze shiga cikiba se next time,nanfa Ajidad'i tadunga yaudararsa harseda ya shiga,koda ya shiga gidan  bata saukeshi afolo ba seda ta dangana da d'aki sabida ita tunda taganshi taji tana sha'awarshi burinta kawai takawar da wannan sha'awa data kamata tashi,suna shiga kulle kofar tayi sannan tafara cire kayan jikinta,Al-ameen binta yake da kallo shed'an nak'ara k'awatamishi surarta,dasauri yaje yarungumeta suka fara romancing d'in juna har zuwa suka fad'a kan gado,Ajidad'i gabad'aya tagama k'osawa komai ya kankama dan itan irin matannanne masu jaraba,sede kash tuni tsaron Allah ya fad'owa Al-ameen azuciya jikinshi rawa yadunga yi yanata a'uziya neman tsari daga shed'an, tureta yayi ajikinshi yamik'e tsaye zuwa lokacin har hawayen  takaicin abinda yayi sunfara biyo fuskarshi ga Surbajo data fad'o masa a rai tabbas yau dayayi zina da ajidad'i  da besan da wanne ido ze kalleta ba, dan yasan dede gwargwado Surbajo nabiya masa buk'ata duk da k'ank'antar shekarunta tana jure duk buk'atunshi batare data gajiba ko taimasa k'orafi,kotakan Ajidad'i beyiba  yajuya yafice daga d'akin ranshi nak'una yaja motarshi yanufi gida gurin Surbajo.

Abangaren Ajidad'i kuwa tafiyar Al-ameen bak'aramin d'aga mata hankali tayiba dan gaba d'aya sha'awarta tagama tasowa gashi yagudu yabarta rasa ina zatasa kanta tayi,kuka tasa iya k'arfinta wanda yajawo hankalin Cleaner zuwa gurinta,da sauri Cleaner tashigo d'akin ganin Ajidad'i tsirara bedametaba illa k'arasawa gurinta datayi tana tambayarta meke faruwa, ganin takasa bata amsa ne yasa Cleaner ta fahimci abinda ke damun Ajidad'i danhaka bata 'bata lokaciba tacire kayan jikinta tajawota jikinta suka shiga aykata masha'a,wa'iyazu billah.

Seda komai yalafamusune Ajidad'i taba Cleaner labarin abinda yafaru tsakaninta da Al-ameen,tsaki Cleaner tayi sannan tace,

"wannan ay abune mesauk'i bade yabaki number d'insa ba ay anwuce gurin kedai kawai ki kwantar da hankalinki."

Maman Yusuf
πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€
       *SURBAJO*
πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€


Zahra Muhammad Mahmud


*PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*
        *P.M.L*

Afuwan nayi mistake din number ne


*page 75-56*

Yana isa gida a kitchen yasameta tana girki, rungumeta yaje yayi ta baya dasauri Surbajo tajuyo dan ganin waye yarungumeta, ganin Al-ameen ne yasa tasaki ajiyar zuciya.

Juyowa tayi Itama tarungumeshi tana fad'in,
"i know my dear bazaka iya fushi daniba don Allah kayafemin Inna b'atamakane bazan sakeba",
D'ora hannunshi yayi akan bakinta alamar tayi shuru sannan yak'ara sassauta muryarshi yace,

"Baki b'atamin ba baby kawai nayi fushine sabida ina ganin kamar baki damu dani bane Shiyasa amman yanzu komai yawuce kiyi hk'r kinji my lollipop,"yafad'i yana kaimata kiss abaki,janyewa tayi ajikinshi sannan tace,

"To yazancan dawo da Aisha d'akinta da nayi maka d'azu,?kaamince ko har yanzu baka yardaba,?"
Kunnenta yaja da hannunsa yana murmushi  yace,

"Ya na iya da gimbiyata tunda kince ta dawo naamince amman ba yanzuba gaskiya".

"Se yaushe",Surbajo ta tambaya.

"Se nasa ajiya anan"yashafo cikinta yana dariya,ture hannunshi tayi zatayi magana yadakatar da ita dacewa,

"Wlh this is my final decision Inkuma baki aminceba to nafasa dawo da itan",dasauri Surbajo tabashi amsa da cewa,

"Aradu na amince Kado,"dariya gaba daya suka sa sabida tuno da irin maganarta tada da takeyi.

Rayuwa suka cigaba dayi cike da so da k'aunar juna, kullum Surbajo na k'ara rok'onshi yadawo da Aisha shiko dagewa yayi akan se Surbajo tayi ciki sannan ze dawo da Aisha,hakanne yasa Surbajo tafara tsayuwar dare tana rok'on Allah yabata ciki dan Aisha tadawo d'akinta.

Bangaren Aisha kuwa ciwon zuciyar tane yatashi kuma tashi me tsanani, dan Inna har ta cire ranta akan Aisha dan kowa yaganta ze d'auka inyafita kamin yadawo ze tarar ta mutu,batasan waye akantaba ko numfashi ta oxygen take shak'arsa abun gwanin ban tausayi,Inna da sauran k'annanta sede susata agaba suna kuka,likitocin dake dubata sunayin iya bakin k'ok'arinsu dansuma suna tausaya mata.


Ajidad'i yau tashirya kiran Al-ameen dan haka bata batayi tunanin komai ba takirashi,seda takira yafi so biyar ba'a d'aukaba can taji yad'aga ,tace,

"Haba namijin duniya ba fad'a me yakawo gaba kuma,"tunda ta fara magana yaganeta ranshi ne yay masifar baci da kiran data mishi sabida ta tuno mishi abinda yafaru tsakaninsu katseta yayi da cewa,

"Banyi mamakin kiran da kikamin ba sabida nasan wacece ke,kuma dama duk inda karya take ba'a rabata da bin maza, nayi danasanin had'uwa dake Jameela,ke shaid'aniyace me kai jama'a wuta, daga yau se yau inkika k'ara kirana sena miki abinda baki zataba stupid kawai, be jira amsartaba yakashe wayar yana huci kamar tana gabanshi.

Itako Ajidad'i bata d'auki zancan nashi serious ba kullum seta kirashi baya dauka kuma bata denaba,dataje gurin bokanta yamishi asiri hkr yabata yace baze iya ba sabida Al-ameen akwai tsari ajikinshi.
   Duk da haka bata hkr ba sabida tasha alwashin Seta lashi zumarsa,ci gaba tayi da kiranshi shi kuma yak'i yasata a blacklist ne acewarsa ita bata isa tasashi yin hakanba tai ta kiranshi harta mutu.


Allah maji rok'on bawa.

Yau Surbajo da zazzab'i ta tashi ga kasala,danko Yusuf takasa yimasa wanka Abbanshine yashiryashi driver yatafi kaishi makaranta,sannan yadawo kanta,
 Wanka yamata Itama yashiryata sannan yabata abinci taci tana gama ci ama'i yataso mata da gudu tayi cikin bayi tafara kwara aman,binta yayi bayin yataimaka mata ta gyara jikinta sannan ya wanke inda ta b'ata suka fito, be jira komai ba yad'auketa suka nufi Asibiti,awon farko likita yatabbatar musu da tana da ciki har na wata biyu, ga mamakin Al-ameen Surbajo tafishi murnar samun Cikin har sujudul shukur tayi, murna sukayi bata wasa ba babu kamarma Surbajo sabida burinta ze cika nason Al-ameen yadawo da Aisha.

Suna isa gida tasamishi daru akan wlh seyaje Kaduna aranar yadawo da Aisha in ba hakaba wlh seta cire cikin,hankalin Al-ameen inyayi dubu yatashi rasa yazeyi da ita yayi dan yasan ta sarai bata fad'in abinda tasan bazata aykataba, bashida zab'in daya wuce yabi umarninta,shiryawa yayi driver d'inshi da excode d'inshi ne suka masa rakiya yatafi Kaduna.wanda hakan ba k/aramin dad/i yayiwa Surbajo ba.


Se sha daya na rana suka isa Kaduna.

Gidan iyayensa yafara zuwa yasanar dasu abinda yakawo shi sunyi murna sosai dajin zancan fatan alkhairi sukayi masa gamida yimasa nasiha akan yayi adalci atsakanin Matanshi godiya yamusu, mommy tafara tsokanarshi dacewa,

"Allah ya soka bata gama iddah ba data gama sede kashiga layin zawarawanta,"dariya yayi sannan yamusu sallama ya nufi gidansu Aisha.

Yana zuwa yasamu labarin abinda yasameta, hankalinshine yatashi dan bayason ganin wani na wahala sabida shi, Asibitin yanufa sanda yaga Aisha jiri ne yad'ebeshi ze fad'i da sauri excode d'inshi suka tareshi.

Kuka Al-ameen yake sosai tausayi da soyayyar Aisha ne suka shiga zuciyarshi akaron farko fad'i yake, "Aisha kiyafeni bansan halin dakike cikiba namaida igiyar auranmu guda biyu dasuka rage don Allah kitashi wlh ina k'aunarki inkika mutu bazan yafewa kainaba please,"ko motsi Aisha batayi batama san yanayiba abinda ya sake karya zuciyarshi kenan yadunga kuka kamar yaron daya rasa uwarsa.

Likitane yamasa bayani gameda cutar Aisha kuma yabashi shawara akan Inde da hali to afitar da Aisha kasar rasha domin duba lafiyarta.,Al-ameen yagamsu da shawarar likitan dan haka tun agurin yakira wayar masu yimasa visa inze fita yace yanason visa zuwa rasha nanda Kwana biyu ko nawane ze biya na mutum biyar yakeso yau komai dare ze kawo hotunan sauran dan ayi musu passport sabida basu dashi .

Aranan akasa Aisha a motar Asibitin zuwa international hospital dake Abuja tare da rakiyar mamanta da Al-ameen da tawagarsa inda k'annan Aishan aka kaisu gidan su Al-ameen,iyayensa sun tausayawa halin da Aisha take addu'ar samun sauk'i suka mata

Karfe goma na dare suka isa Abuja,adaren yakai hotunan Surbajo,Yusuf,Inna,Aisha,sabida shi yana dashi visa kawai za'a masa banda passport,se sha biyu yashigo gida,Surbajo tafirgita da ganinshi nande yakwashe komai yasanar da ita, kwana tayi tana kuka da sassafe tasa Al-ameen yakaita Asibitin ananne tai kuka bana wasaba dakyar aka rarrasheta. Ranar da ita aka kwana a asibitin fafur tak'i komawa gida.

Da sassafe jirginsu yad'aga zuwa rasha,

to Aisha Allah yatashi kafad'a .

Maman Yusuf