Monday 3 April 2017

SURBAJO

[4/2, 22:37] zahra muhammad mahmoud: 🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀
         *SURBAJO*
🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀


Zahra Muhammad mahmud

*this page is dedicated to my sweet Aunty,hajiya meelmoh, owner of meelmoh magazine.Allah yatsareki aduk inda kika shiga*


*page 67-68*


Al-ameen ne zaune, yayinda surbajo Tay matashin kai da cinyarsa, Suna hira.

Al-ameen ne Yace,

"madam yaushe zaki bani new baby ne?yafadi yana shafo cikinta,dariya tayi medaukar hankali,hannu tasa Tana wasa da dimples dinshi,sannan tace,

"lalle ma my dear nan,nafahimceka sokake inyi saurin tsufa, inbanda abinka ay yanzu hutawa yadace inyi Dan haihuwa barkatai seyajawo natashi ayki dawuri,cuno baki tayi sannan tacigaba,dan haka ni kadena wannan maganar yanzu kabari sena gama karatu.

Al-ameen mamakine yacikashi naganin zallar kuruciyar surbajo, wacce yafahimci dole seya setamata hankali,magana yafara da cewa,
"baby yakike magana kamar bakida ilimi,menene aybu inkin haihu yanzu,karki sawa kanki akida tawasu mutane marasa tunani,tonide soyayyar dazaki nunamin itace kihaifamin yara,taya yaro daya kawai kice kinaso ki huta,hutun jaki da kaya ko?.itade Tunda yasoma mgn kallonshi take  Tana murmushi, Dan dama tafadine taji mezece.

Kallonta yayi yaga Tana dariya,dakatar da maganar yayi yana dubanta,rungumoshi tayi Tana dariya tace,my Legend kenan maida wukar surbajo tsokanarka takeyi,haifa maka yara inde Allah yabamu yanzu nafara so no need to be worry, rumgumeta shima yanada  dariya yace,

"lalle baby wato kinmaidani kakanki ko,seki  fadi maganar dakikasan dole Sena tada jijiyar wuya ko?to daga yanzu naganoki  bazan Kara bata bakina gurin maganaba wannanne hukuncinki, yana fadin haka yasureta yay cikin daki daita suna dariya.


Muleka gidan amaranmu.


Zuly da angonta Musa, soyayyace akashata bata wasaba har ta tsawon wata guda.bayaga haka,


Yau tun safe Musa yafita yabar gida shuru bedawoba har karfe goma nadare,hankalin zuly inyayi dubu yatashi,gashi wayarshi takira Tana ringing Amman baa dagaba, Tana nan zaune afalo  taji alamun bude get lekawa tayi ta window ganin motarshi ke shigowane yasa hankalinta yakwanta dasauri taje ta bude kofar, sannan tajuya dakinta takara gyara makeup dinta tafesa turare,sannan tadawo falon, sede me? Tana zuwa falon Musa tagani dawata yarinya maana karuwa tarukoshi yana tangadi ga kwalbar gulder ahannunshi yana korawa,

Salati tayi Tana fadin,

"nashiga uku Musa mezan gani acikin gidana,giya da karuwa , innalillahi wainna ilaihirrajuun, Wlh baze yiwuba,
kan budurwar tayi tana fadin,
"wlh yau se zina tazamemiki karshen aykinki aduniya matsiyaciya tsinanniya,
Musane yakatseta dacewa cikin muryarsa ta me Maye,

"narantse da girman Allah kika kuskura kika tabamin blessing Wlh Sena fafemiki ciki, kuka tasa tace,
" musa yanzu akan karuwa zaka hallakani?

amsa yabata dacewa,"eh karuwar kuma Wlh tafiki daraja a idona, ke!bakebama  uwarki wannan tafita mutunci a idona, Dan haka ki kula,yana gama fadin haka yaja hannun blessing suka shige dakinsa suka kullo kofa.

Kai ta dafe tafada kan kujera Tana kuka iya karfinta.
Tuge dankwalinta tayi Tana Ta share hawayenta dashi.
ranar zuly bata runtsaba Tana zaune afalo, Tana jiyo sautin bidirin da akeyi akan gadonta na Sunnah .

Washe gari da safe haka musa yasata agaba dole ta dafamusu ruwan wanka, kuma yace ta tabbatar ta hada musu breakfast kamin su fito,bata da zabin daya wuce tayi abinda yasata,dan bakaramin so takewa musaba Tana tsaron yasaketa takoma gidansu da zama, dama gashi ta juma batayi auranba.

haka rayuwar zuly taci gaba da tafiya agidan Musa,zuwa yanzu bakoyaushe yake kwana agidaba,wanda hakan ita yafimata dadi Dan in agida ze kwana toko da 'yan tayan kwana yake zuwa biyu ko uku Dan yanzu likkafa taci gaba yafi karfin mace daya sede biyu zuwa uku, kuma ingari yawaye duk kayansu itace me wankewa inba hakaba taci duka,koda wasa bata taba ba kawayenta labariba bare takai kararsa gidansu.

yau da wuri Aisha tashirya, sabida tanason zuwa gidan zuly tawuni,sabida Tunda akayi auran so biyu taje shima lokacin ko wata batayiba.

karfe takwas na safiya a gidan zuly tamata,wanda zulyn seda ta firgita da ganinta,afalo tasauketa,Aisha ko mamakin abinda yaramar da zuly  tayi baki takeyi,kasa daurewa tayi seda ta tambayeta tace,
"kawas meke faruwane dake haka kika Yi baki kuma kika rame, kamin tabata amsane suka jiyo karar bude kofar dakin zulyn. Musane yafito shida 'yanmatansa guda biyu,kowacce ta rungumeshi  gashi kayan jikinsu kadai yaisa yasanar dasuwaye su ,
Arude Aisha take kallonshi, takalleshi ta Kalli zuly wacce tasunkuyar dakai Tana kuka,
Kasa cewa komai tayi se ido, Musa ko bakunya ya Kalli Aisha yace "madam ykk? ya gida kwana dayawa kinyi wuyar gani ,mamaki ne da tsoro suka hana Aisha bashi amsa, ko ajikinshi Illa ajiye panties and bras na yanmatanshi Wanda suka cire agaban zuly yace "gasunan washing and drying and then ironing kamin mudawo .bejira amsartaba suka fice shida 'yanmatanshi.

Azabire Aisha takai dubanta gurin zuly, tace,
"today I saw the thing that I have never think it will be happen to you ever in your life,please zuly wake me up kice mafarki nakeyi please, tafadi Tana girgiza zulyn wacce inbanda kuka baabinda takeyi.

Dakyar Aisha tashawo kanta tabata labarin abinda ke faruwa, zugata Aisha tashigayi kamarde yadda sukemata, ga mamakinta seji tayi zuly ta dakatar da ita dacewa, "Aisha waimeyasa kika dauka kowama banzane irinki,tobari kiji infadamiki kinga halinde danake cikiko,to wlh har gobe inason mijina kuma babu wani dalili dazesa inbarshi, zugarki gareni ki adanata kibari inkin samu wata shasha irinki seki bata tadauka Amman bani zuly ba, uhm Bari kiga inje inyi aykin lada tamike gamida kwasar kayan da Musa yaajiyemata na'yanmatanshi ta tafi wankewa.

kwakwalwar Aisha seda tadena ayki na 'yanmintina,  zuciyartace take harbawa da karfi yayin da wasu hawayen bakin ciki suka fara biyo fuskarta,bata da sauran magana Jakarta tadauka tabar gidan zuciyarta na mata kuna.


muje zuwa riders


Maman Yusuf
[4/3, 23:43] zahra muhammad mahmoud: 🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀
        *SURBAJO*
🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀


Zahra Muhammad Mahmud


*PURE MOMENT OF LIFE WRITE (P. M. L. W)*


*page 69-70*


Aisha dak'yar take ganin gabanta ahaka harta k'araso gida,jakarta da key d'in motar ta yardar akan kujera sannan ta haura sama inda D'akinta yake Tana kuka me tsuma zuciya.
Wayarta taciro domin kiran Ruky dan gani take Ruky bazata ci amanartaba, Tana kiranta bajimawa Ruky tadauka tace, "hello Ashanty ykk"?
  cikin b'acin rai tace, "Ruky dama gadar zare kuke kullamin bansaniba? "meyafaru"?
     Ruky ta tambaya, kwashe abinda Zuly tamata tayi tafad'awa Rukyn ,ga mamakinta seji tayi ruky tafashe da dariya sannan tace, "sannunki Aisha ammafa kinjima kina baccin asara wanda se yanzu kika farka, kuma Zuly tamin Dede data miki hakan dan inda nicema sena miki shegen duka ayayinda kika fara bani gurguwar shawarar", cikin kuka Aisha tafara magana dacewa,

Al-ameen yau surprise visit yakeso yaba Aisha,shiyada bekirata yasanar da ita zuwanshiba yafiso sede taganshi kawai.
  Shigowa yayi cikin gidan cikin sand'a dan beso ko motsinshi taji,mamakine yakamashi ganin gyelanta da key d'in mota akan kujera afalo Wanda ko ba'a sanar da shiba yasan daga anguwa tadawo,ranshi yabaci amma seya had'iye b'acin ran yahaura sama inda d'akinta yake,wayar dayaji tanayine yasa yadakata a 'kofar d'akin yana sauraron abinda take cewa.

_"Ruky dama akwai ranar dazata zo kuci amanata?,wlh koda wasa banta'ba tunanin faruwar haka daga garekuba, kuncutar dani dayawa kuka dunga zugani akan nadunga batawa mijina rai,har sata seda kukasani namasa, k'arshe ma baku barni hakaba harseda kuka sa nakashewa Surbajo 'ya tun tana ciki tahanyar nunamin zuwa gurin boka yamata asiri, wlh kuncutar dani da yawa bazantab'a yafemukuba,yanzu dawanne ido zan dubi Surbajo da Al-ameen ince suyafemin nice nakashewa surbajo 'y'a"?_


"Da idon dakika dubi bokan dayayi asirin dashi zaki dubemu, Al-ameen yabata amsa lokacin dayake k'ok'arin shigowa cikin d'akin"

wayar dake hannunta tace ta fad'i yayinda jikinta yake rawa tako'ina, hkr takeson bashi amma ina kalmar ta'ki fitowa,jada baya takeyi sabida ganinshi datayi yana k'ok'arin ciro belt d'in jikinshi.

Al-ameen tunda Allah ya halicceshi betab'a jin b'acin rai kamar nayanzun da yakeji ba,dukanta yashigayi kota'ina batare da tausayiba,garin dukanne yakaimata wani naushi a hannu Wanda hakan yajawo hannun yakarye, seda yaga tadena motsi ya k'yaleta,kuka yakeyi sosai aranshi yake tunanin rashin imani irinna Aisha.

Fita yayi daga d'akin yaje nashi d'akin durowar dayake ajiye mahimman takardu yabud'e yad'auko result d'in Aishan na asibiti Wanda akace bazata K'ara haihuwaba, be tab'a nunamata result d'inba kuma mahaifiyartama ya rok'eta karta fad'amata shiyasa Aisha batasan komaiba game da rashin sake haihuwar dabazatayiba.

Dawowa d'akinta yayi d'auke da takardar, akwance yasameta Tana ihun hannunta daya karye, tsawa yadakamata sannan yace,

"Dagani har Surbajo baki cuci kowaba Illa kanki,kuma nide ban yafemiki ba Wanda nasan itama bazata yafemikiba, yarinyar nan bata tare miki komaiba Amman kika d'auki karan tsana kika d'ora mata,bakiji tausayin  wahalar datasha da cikin ba kika iya zuwa aka kashe abinda zata haifa,to Alhmdllh Allah yasaka mata ta hanyar data dace, ga result d'inkinan Wanda likitan daya amshi haihuwarki yabayar, nacewa keda haihuwa se wani ikon Allah sakamakon magunguna nahana d'aukar ciki dakike sha",  wurga mata takaddar yayi,sannan yad'ora da cewa "kinma kanki A'isha.kuma kitattara naki ya naki kibarmin gida nasakeki saki d'aya"
  ,wata gigitacciyar 'K'ara tasaki bayan yagama maganar.

Dak'yar tajawo jiki tazo gabanshi tana kuka tana rok'onshi ya gafarta mata,hankad'eta yayi yafice daga d'akin kai tsaye harabar gidan yanufa,umarni yabawa megadi dacewa yatabbatar nanda 30minutes Aisha tabar masa gida kuma inta fita yakullemasa gidan, driver yasa yakaishi gidan iyayensa.


Maman Yusuf

No comments:

Post a Comment