Sunday 19 March 2017

ALLAH GATAN BAWA

[3/13, 07:08] Ussaina: *ALLAH GATAN BAWA*✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨

*Bismillahirrahmanirraheem*
*Nagodewa Allah mekomai me kowa daya bani ikon rubata wannan littafi nawa me suna *Allah gatan bawa, ina rokon Allah yasa littafina yasamu karbuwa agurinku masu karatu,innayi kuskure kusanar dani da gaggawa domin in gyara ,dan adam ajizine nagode.*


*Page 1-10*


 Azaune take akan dakalin kofar gidansu hannunta dauke da kara tana wasa dashi  yayin dasauran yaran makwabtansu suma suke nasu wasan ita kuma tana binsu da ido domin ita Bata da yencin shiga cikinsu tayi wasan yarinyace yar kimanin shekara takwas da haihuwa wacce Allah yajabceta da lalura irinta zubar da miyau sanna kafarta daya dahannunta daya duk ashanye suke intana tafiya tana jefa kafarne yayin da hannun yake makale a kirjinta
wannan lalurarce tasa yara da sauran mutanen garin kyamatarta ko wasa basayi da ita sede tazauna agefe tana kallonsu

*Asalin labarinta*

Ilham bukar shetima shine sunanta na aynihi mahaifinta malam bukar shetima hafaffen garin medugurine acikin garin bama inda fadace fadacen daakeyi ayankinsu yayi sanadiyyar mutuwar iyayensa hakanne yasa yayanke shawara shiga cikin ayarin yan gudun hijira domin yin hijira daga yankinnasu. Bashi kadai bane agurin iyayannasa su biyu ne shida dan uwansa mesuna imamu amma rudin dagarin ke ciki yasa suka bacema juna yayi kukan bakin cikin mutuwar iyayensa da kuma bacewar yayansa Wanda besan awanne hali yakeba shiyasa yarungumi kaddara yayi hijira
Acikin ayarin yan gudun hijirarne yahadu da wata budurwa wacce itama ankashe iyayenta( Bata da kowa )me suna maryam tunda suka hadu yake tausayamata sabida ita macece shiyasa yashiga dawainiya da ita har suka shigo garin kano bayan ansaukesu asansanin yangudun hijirane washe gari yakirata gefe inda yashawarceta dasuyi aurene zefi kulawa da ita sabani basu da aure Batare da Bata lokaciba ta amince inda dattawan cikin yan gudun hijirar sukadaura musu aure bayan yabata sadaki nera dubu biyar
tundaga lokacin yadukufa gurin kwadago acikin gari har Allah yataimakeshi yakama masu hayar gida me daki biyu acan garin wudil sabida beda halin kamamasu acikin gari  be kaunar zamansu acikin sansanin "yan gudun hijirarne shiyasa yakamamasu haya bayan tarewarsu badadewa Allah ya albarkacesu dasamun karuwa ta cikin suncigaba da kulawa da cikin har zuwa haihuwa inda Allah yasa maryam tahaihu lafiya tasamu "ya mace  yarinyar kyakkyawace ajin farko sabida daga uwa har uban shuwa arabne sede kallo daya zaka mata kafahimci Bata da lafiya maana nakasasshiyace basuyi kasa agwuiwaba suka samata suna inda taci sunanta ilham bayan suna ilham iyayenta sundukufa neman magani amma duk inda sukaje amsa daya akebasu bazata warkeba tunda da lalurar aka haifeta hakan yasa suka hakura suka mikama Allah lamarinsu
ilham na dada girma lalurarta nakara bayyana ahaka har aka yayeta bayan yayetane Allah yasake basu wata 'karuwar inda wannan haihuwarma tasamu mace suka samata sunan mahaifiyar bukar fateema suna kiranta ameera bayan haihuwar ameera basu sake haihuwaba har zuwa yanzu da ilham kede shekara takwas ameera kuma biyar
rayuwa suke mecike da tsanani sabida malam bukar me karamin karfine wani lokacin ko yafita bayasamun dakon haka yake dawowa ahaka yakokarta yasa su ilham awata makarantar gwammanti ta pramary ilham na aji uku ameera aji biyu duk à tunaninsu ilham bazata iya komai amakarantaba amma Allahyataimaka yasa tana ganewa sede ko tambayarta akayi bazata iya fadaba sede gwaranci dan harshenta akarye yake. ko amakaranta tsokanarta suke yara sede ameera tatunda taremata dukda itama bawani wayo garetaba ita ilham kuwa sede taita dariya miyau nazuba tadauka wasa suke mata, to ko sundawo gidama yaran unguwa bakyaleta sukeba shiyasa mahaifiyarsu batason ilham nafitowa sabida ko ina hantararta akeyi tun mamansu na magana har tadena sabida tasan *Allah gatan bawane*

*Cigaban labari*

tanana zaune yaran suka fara tsokanarta itako se dariya take harda kwantawa miyau nazubowa daga bakinta, jiyo hayaniya da mahaifiyarta tayine akofar gida yasa tayi saurin lekawa daki inda tabarsu suna wasa da ameera ga mamakinta ba ilham sede ameera datakeyin homeworke dinta dasauri tadauki hijab dinta tasa tayi kofar gida sabida ta tambatar da ilham akeyi ayko ilai tana fita tayi tozali da ita tana dariya yara natsokanarta suna watsamata kasa bakinciki besa tayi yunkurin hanasuba illa iyaka dauko ilham datayi tashiga gida daita itako baabinda yadameta se dariya take .







love you all maman yusuf✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
[3/13, 07:08] Ussaina: *ALLAH GATAN BAWA*✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
_Writting by Zahra Muhammad mahmud_

*Page 11-20*

Suna shiga gida kai tsaye  toilet tashige daita tsifa tafara yimata sannan tawankemata kai Wanda yasha kasa sannan tayimata wanka tafito daita daki takaita sannan tayimata shafa tasauyamata kaya karkuso kuganta à time din kamar kadauka kagudu sabida kyan datayi.
Abinci tazubo mata tafara Bata abaki Wanda ita ilham har zuwa lokacin dariya takeyi sabida intafara dariya tana jimawa bata denaba itako mahaifiyarta kwalla kawai take sharewa natausayin diyar tata

        **************
Yauma kamar kullum suntaso daga makaranta, ameera narike da hannun ilham suna tafiya yara suna tsokanarta ameera sekuka take musu tana dan Allah kudena metayimuku Wanda agefe daya ita wacce abin yashafa inbanda dariya baabinda takeyi ganin hakane yasa yaran suka cigaba da tsokanarta ahaka har suka karaso gida babansu suka tarar akofar gida yana alwala  zashi masallaci ganinshine yasa yaran komawa da gudu sabanin da dahar cikin gida suke binsu
Sannu baba mundawo cewar ameera sannunku mamana kushiga gida ina zuwa bari nayo sallah yafadi tareda shafa kan ilham wacce takafeshi da ido ba um ba umum
Dashigarsu gida dakin mamansu suka shiga suka tarar da ita ta kabbara sallah  ameerace tayi kokarin zuwa daukar buta itama tayo alwalar tazo tabi bayan mamanta sukayi sallah. Tare da yima ilham adduar samun sauki.itako ilham kiciniyar cire safa take har suka idar bata cire KO guda dayaba ameerace taamsa tacire mata sannan mamansu tacire musu Uniform Wanda gaban rigar ilham jike yake da miyau Wanda hakanne yatilastawa rigar kodewa daga gaban  wanka tamusu sannan tajika musu garin rogo suka sha
bayan sungama sha ne malam bukar yashigo gida fuskarsa ba walwala kan tabarmar dasuke zaune yazauna cike da kulawa maryam take tabayarsa malam meke faruwa naga ranka abace. Yace haba maryam dama haka yara suke biyo ilham baki taba sanar daniba kamar sunga dodo Sun m'aida ita kamar abin wasa haba maryam kinyimin adalci kenan. Maryam wacce tunda yafara magana take zubar da hawaye dakyar tabudi baki cikin kuka tace haba baban ilham menene amfanin insanar dakai indaga hankalinka yarannan badenawa zasuyiba konakai kara gun iyayensu basa kwabarsu to yazanyi ilham de ba ita  tayi kantaba Allah ne yayi ta kuma shi dayayita ahaka nasan yanasane daita kuma nayi imani shine gatanta danhaka kaima kazubama sarautar Allah ido inda rabon musha kallo nangaba zakace nafadamaka takarasa zancan tana kuka. Jin maganganunta yasanya jikin bukar sanyi cikin sigar rarrashi yafara magana nafahimceki maryam kuma nima zanyi yadda kikace amma kinsa ba dadi adunga tsokanarta tace hakane amma bamuda yadda zamuyi sede mufadawa Wanda yayita
haka sukai ta tatyaunawa agame da matsalar ilham har akakira sallar laasar suka tashi domin bada fatali.






love you all 😘 maman yusuf
[3/13, 07:08] Ussaina: *ALLAH GATAN BAWA*✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨

_writting by Zahra Muhammad mahmud_

*Page 21*

*Bayan shekara uku*

Kwanci tashi bawuya agurin Allah yaune ranar dasu ilham suka gama pramary school ita da ameera sabida tun suna aji hudu akayima ameera jumping takamo ilham.cike suke da murna daganin ranar dagasu har iyayensu murna suke harda ilham wacce batasan meyakawo murnarba.atamfa 'yar leda babansu yasiyamusu akadinkamusu Riga da siket ba laifi sunyi kyau kuma sunji dadin kyautar da babannasu yamusu na atamfar,

           *********
Yau watansu ilham daya dagama makaranta suna zaune atsakar gidansu suna wasa yayin da iyayensu suke hirar rayuwar duniya. Yarone yashigo gidan da sallamarsa bayan Sun ansa yagaishesu sannan yadubi malam bukar yace baban ilham ana sallama Dakai akofar gida wani mutumi gabanshine yafadi sannan yace kaje kace ganinan zuwa yaron yamike yafita yayin da malam bukar shima yamike, da sauri maryam tasha gabanshi tace "abban ilham yanaga daga cewa ana sallama dakai hankalinka yatashi kode akwai matsalane. Hannu yasa yashare gumin daya keto masa yace "Maryam banfada mikibane amma wallahi tun watanni uku dasuka wuce kudin hayarmu yakare kuma megidan cemin yayi yabani wata biyu inkawo masa kudin inba hakaba zesa wasu agidan kuma kinga yanzu har wata uku shida yacemin wata biyu nasan yazo karbar gidansane shiyasa kikaga hankalina yatashi. Cike da damuwa take kallon mijinnata tace "meyasa bakason sanar dani damuwarka abban ilham ni aganina abokin kuka shi ake fadawa mutuwa  meyasa kaboyemin ?    Kiyi hakuri itace kalmar daya iya furtawa yafita kofar gida dan ganin me sallama dashi  abinda yaguda shiyatarar megidan yagani atsaye dashi dawasu katti guda biyu   tun kafin yayi magana megidan yarigashi yafara magana cikin fushi "sannunka mallakau wannan ay ko gadona gareka se haka ko ancemaka abanza nasamu gidan dazan barka kaita zama batare dakabiyaniba cikin muryar tausayi malam keba megidan hakuri har kasa yaduka yana bashi hakuri amma shi KO ajikinshi karshema wainnan katti yacema sushiga gidan sufito masa dakomai da kowa nagidan kafin malam yayi magana tuni sunshige gidan umma (sunan da ameera ke Kiran mamansu kenan)tana zaune à inda malam yabarta seganin katti tayi suna shigowa  kafin tayi magana taga malam yashigo yana share hawaye  tambayarsa  tashiga yi "malam meke faruwane ? Cikin muryar kuka yace "maryam megidanne yace mufitarmasa daga gida wainnanma dakikaga sunshigo fitardamu da kayanmu yasasu suyi,jeki kidauko mayafinki  juyawa tayi jiki ba kuzari tadauko hijab dinta dama kayansu nasawa agana must go suke dan haka dauka kawai tayi tunkafin takai ga nade katifarsu kattinan sunrigata wurgota kofar gida haka suka shiga wurgi da komai n'a gidan tsinke basu bariba daga karshe suka taso su malan bukar agaba shida iyalansa zuwa kofar gida bayan sunfitone sukaga kofar gidan cike da yan kallo manya da yara.makulli megidan yasa yakulle gidansa yawuce shida yaransa kota kansu be biba ganin jamaa nakara yawa akofar gidanne yasa malam bukar fara tattara sauran tarkacensu kama daga tukwane bokiti dadai sauran kayan tarkacen gida yakulle acikin wani buhu katifarma yasa igiya yadaure dama taji jiki yana gama daure katifar yadorama ameera ummansu kuma tadauki gana must go din kayansu tarike hannun ilham har zuwa lokacin kuka sukeyi dukansu harda ameera sabanin ilham datake tafaman sanaartata wato dariya malam bukar buhun kayan daya daure yadauka yace sutaho sutafi sudena zama agurin suna tarawa kansu mutane tafiya suka farayi dauke da kayansu suna kuka yaran garin kamar jira suke suka bisu abaya suna musu ihu sekace sunyi wani laifi kuma manyan gurin bawanda yakwabesu sabida makwabtansu  suntsanesu badan komaiba sedan kawai Allah yabasu ilham
haka suka cigaba datafiya yaran namusu ihu karshema suka fara jifansu seda sukayi nisa dagarin sannan yaran suka koma




Love you all 😘 maman yusuf
[3/13, 07:08] Ussaina: *ALLAH GATAN BAWA*✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨

_writting by Zahra Muhammad Mahmud_

*Page 23*


Mutanen dake gurinne sukayo kanta domin Bata taimakon gaggawa  daukarta sukayi  sukasa amota tare da gawar malam   .sukuwa su ameera suna zaune Jin shirun yayi yawane yasa ameera mikewa takama hannun ilham suma sukayo hanyar titin zuwansu yayi daidai   dazaasa ummansu amota dagudu ameera takarasa gurin tana Kiran ummansu   mutanenne suka juyo gareta      domin Sun fahimce mahaifiyartace har anhada daita amotar Sun fara tafiya sannan ta tuno da ilham dake can gefen titi  har zatayi magana sekuma tayi shuru sabida atunaninta ilham ba inda zataje harsuje sudawo tuna hakane yasa tamaida hankalinta kan ummansu wacce ke kwance rai a hannun Allah.
Asibiti akanufa dasu umma emmergency aka shiga daita yayin da malam kuma akayi mutuare dashi tagaban ameera akawuce dashi se alokacin hankalinta yakai gareshi wani gigitance ihu tasaki tayo kansa tana  ihu nurse ne suka riketa itako ihun Kiran baba take ahaka har aka shige dashi ciki duk wani me imani inyaga ameera se yatausayamata malam yarasu ga umma à emmergency rai  a hannun Allah
Dakyar nurse din suka rarrasheta tayi shuru abunka da yaro har wasa tafara. Kwatakwata tamanta da wata ilham hankalinta nakan umma tunda ance mata babanta yamutu. Secan da magariba aka fito da umma daga emmergency zuwa dakin 'yan paralyse domin itama umma asanadaiyyar faduwan datayi takamu da paralyse gabadaya barin jikinta daya yashanye har gefen fuskarta  .bayan ansa umma adakinne nurse suka kira ameera zuwa dakin likita, tabayoyi yafaramata kama daga sunansu, daga ina suke, awacce anguwa suke (dayake wainda suka kawosu  su suka bige malam. Daga cewa bari suyi sallah suka gudu ) sunansu tafadi sannan tafadi anguwarsu. Abinci likita yasa aka Bata daga nan yasa aka maida ita  gurin ummanta gefen gadon tazauna sannan tabi jikin ummanta da kallo har zuwa fuskarta ganin yadda fuskar ummanta tasauya yasa tasanya kuka tana jijjiga umman tana fadin umma.gaba daya dakin bawan da betausayawa ameera da ummanta ba tananan har bacci yadauketa ajikin ummannata.

      **********
Bata farkaba se dasafe se lokacinne tatuna da ilham dagudu tafito daga Dakin tana ihun Kiran ilham karo sukayi da doctor ganinta afirgicene yasa   yariketa yana tambayarta meke faruwa dakyar ta iya fadamasa dasauri yadauketa yasa amota suka tafi gurin dayake banisa amma koda zuwansu va ilham ba alamarta sede  kullin kayansu juyo sukayi jiki bakwari bayan sungama duba ko ina nagurin ba ilham asibitin suka koma  ameera nata aykin kuka.



love you all😘 maman yusuf
[3/13, 07:08] Ussaina: *ALLAH GATAN BAWA*✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨


_writting by Zahra Muhammad_

*Page 22*


Tafiya sukayi me nisa sannan suka sami kasan wata bishiya suka zauna domin su huta. Har zuwa lokacin hawaye bedena zuba à idonsuba
Malam ne yakai dubansa fuskar ilham wacce ko baa fadamasaba yasan tagaji da hannu yayimata alama datazo kusa dashi.bamusu tamatso hannunta yarike yafara magana "ilham mu munyarda Allahne yayiki kuma yabamuke badan bayason daya daga cikinmuba kuma insha Allahu masu kinki nangaba se Sun huta à  inuwarki kiyi hakuri daduniya aduk yadda tazo miki .yafada yana zubda hawaye itako ko ajikinta danma tagajine danasan baabinda ze hanata darawa wani wata sarka yaciro awuyansa yadauramata awuyanta gami da fadin Allah ya albarkaci rayuwarki gaba daya suka amsa da ameen
Umma takatseshi tahanyar fadin malam kayi shuru haka Allah nan  kuma shine gatan kowa. Tana gama magana tamike  malam ne yace inazuwa kuma bayan hutawa mukeyi,tace wallahi kishin ruwa nakeji shine zan tsallaka titincan inga ko zan samo  ruwa, mikewa yayi yanafadin haba ina gurin shine ke zaki neman ruwa zauna inje inkawomuku. Haka tazauna badan ranta yasoba shikuma yatafi debo ruwan yanatafiya yana waiwayensu kamar  ze jiyo kuma sede yatafi sunanan zaune suka fara jiyo hayaniya abakin titin  gaban umma ne yafara faduwa tana tambayar kanta meke faruwa   takejin hayaniya haka kamar bazata jeba cam kuma tamike tanufi gurin tana zuwa taga anzagaye ana kallon wani abu karasawa itama tayi gurin yayinda bugun kirjinta yatsananta  tana karasawa gurin INNALILLAHIWAINNAILAIHIRAJIUN
Malan tagani kwance cikin jini mota tabugeshi kanshi ya rabe gida biyu ko baa fadamata ba tasan malam rai yayi halinsa yanke jiki tayi tafadi kasa sumammiya



love you all 😘maman yusuf
[3/13, 07:08] Ussaina: *ALLAH GATAN BAWA*✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨

_writting by Zahra Muhammad mahmud_

*Page 24*


Suna isowa asibitin dakin da mama take suka nufa auna ta likitan yafarayi da mamakinsa yaga ba numfashi atare daita hankalinshine yafara tashi yana gudun kar ace ita ma babu ita awo n'a musamman yashiga yimata sede yamakaro Allahn dayayita yafishi kaunarta innalillahi wainnailaihirrajuiun itace kalmar dayake nanatawa zufa ce tashiga keto mishi ta koina dubansa yakai gun ameera wacce har Yanzu kukan rashin ganin ilham takeyi. Tausayinta ne yakamashi Jan hannunta yayi suka bar dakin bayan ya rufe gawar umman wasu nurse guda biyu yagani yabasu umarnin akai gawar umma mutuware
Office dinshi yashiga da ameera bayan Sun zaunane yafara magana " kiyi hakuri kinji kowa dakalar kaddararsa ketaki kaddarar Bata da kyau amma kigode Allah kinji .kai kawai tadagamasa sabida Bata fahimci meyake nufiba duba da kankantar shekarunta. Address dinsu yasake tambayarta tasanar dashi Jan hannunta yayi suka sake fita kai tsaye unguwarsu yaje da ita wani makocinsu yasamu mesuna malan sule bayan sungaisane yake tambayar sa shin koyasan wannan yanuna ameera dago kai malam sule yayi yakare mata kallo sannan yace yasanta yar gidan malam bukarce inafatande lafiya. Lafiya kalau likita yabashi amsa daganan likita yakoro masa bayanin abinda yafaru  harda mutuwar umma se anan ameera taji ummansu itama tarasu kuka tasamusu me tsuma zuciyar duk wani me imani shikanshi malam sule kukan yakeyi yakara da fadin jiya jiyannan mutanennan sukabar gidannanfa yanuna gidan ashe tsautsayine yafitardasu Kuka yasake barkewa dashi
likitane yakatseshi dacewa malam ba kuka zakayiba sonake ka kaini gidan megari inyimishi jawabi sabida asan yadda zaayi da gawarwakin. Tashi malam sule yayi gami da fadin biyoni muje gurin me garin. Kama hanya sukayi likita narike da hannun ameera ,akafa sukaje gidan megari dayake banisa bayan sungaisa dame gari sukayimishi bayanin abinda ke tafe dasu megari bakaramin girgiza yayi da labarinba duk da besan malam bukar amma yatausayawa rai shela yasa akayi agari akan jamaa suzo fada zaayi janaiza sannan yamike yabi doctor suka dunguma zuwa asibitin da isarsu akasaka gawarwakin amota bayan doctor yagama daukar hotonsu awayarsa sannan yayi cikecike a file dinsu. Kai tsaye kofar gidan megari akayi dasu Wanda yacika da jamaa cikin gida aka kaisu akamusu wanka megari yasallacesu aka kaisu gidansu nagaskiya
Wayyo rayuwa kowa nagurin yatausayawa wainnan bayin Allah se addua ake musu nasamun rahamar Allah.bayan anyi adduoine doctor yace zewuce sabida yanaso zetafi gida dan shi acikin garin kano yake ayki yakawoshi wudil. yanemi megari daya bashi ameera yatafi da ita dan zamanta agarin zedunga tuna mata danginta tana shiga damuwa.hakuri megari yabashi akan yayi hakuri zuwa Adan kwana biyu sabida karyayi gaggawar bashi ita daga baya danginsu nagurin iyaye suzo nemansu dan haka yayi hakuri aga abinda hali zeyi. Va ason ran doctor yatafi yabartaba wacce harzuwa lokacin daze wuce kuka takeyi ita ummanta dakyar ya rarrasheta bayan yamata alkawarin zekaita gurinta, naira dubu goma yakirgo yaba megari akan asiyamata  kayan sawa .yanacikin maganar ne  yatuna da kayansu nabayangari dan haka motarshi yanufa yaje yadebo kayan Wanda bawanda yatabasu sabida bawasu kayan kirkibane. Megari yaba kayan sannan yabukaci da à adanasu kodan gaba. Sallama yama megari yawuce, bayan tafiyarsa megari yasa akashiga da kayan cikin gidan shima shiga yayi rike da hannun   ameera yana shiga matanshi sukayo kanshi kowacce burinta yabata ita sabida me gari baya haihuwa dan haka dukansu basu da y'aya ganin inyace gawacce  yaba abin ze zama da rigima shiyasa yace dukansu yaba kowa nada iko akanta ameera kenan baiwar Allah .





jamaa ina labarin ilham ne ?



love you all 😘maman yusuf
[3/13, 07:08] Ussaina: *ALLAH GATAN BAWA*✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨

_writting by  Zahra Muhammad mahmud_

*Page 25*


Iham tunda ameera tatafi tabarta take tsaye abakin titin bata matsaba tananan har kowa yawatse bata da alamar motsawa.
Gungun wasu almajirai sukazo wucewa sundawo daga yawon bara suna zuwa daidai da ita kawai seta bisu dan ita atunaninta gidansu zasuje tafiya sukayi metsayi
Sannan suka iso wani dan kauye dayake suna da yawa shiyasa basu lura  da itaba tsayawa sukayi abakin titi da alama tafiyar dasukayi sunyitane  dan samun ragin kudin mota baa kauyan zasu tsayaba wata motace kirar akori kura tazo wucewa dasauri almajiran suka fara tsaida motar
Motar harta giftasu tadawo da baya ina zuwa direban motar yatambaya. Kano suka hada baki gurin bashi ansa gyara parking yayi sannan yafito yabude musu kofar bayan motan dasauri almajiran suka fara darewa kan motar har sungama hawa ilham natsaye sabida ita bazata iya hawa da kantaba direbanne yawaigo yaganta atsaye atunaninshi tafiyarsu daya danhaka batare da Bata lokaciba yadauketa yasa acikinsu bayan yarufe kofarne yace dasu kudin motarsu naira hamsin hamsin  basu musaba sukace Allah yakaimu lafiya zagayawa yayi yatada motar   sukadau hanya
Tafiya sukayi medan tsayi  sannan suka iso kano parking yayi agefen titi sannan yasakko yabudemusu kofa kowa inze sauka seya mika kudinsa harsuka gama sauka yarage saura ilham sauko da ita direban yayi sannan yamika mata hannu alamar takawo nata kudin kallonshi kawai take da lumsassun idanuwanta Wanda KO baa fadaba yunwa takeji
Ganin Bata da niyar magana yasa yakyaleta yashige motarsa yawuce yabarta agurin sukuwa dama almajiran sundade da wucewa.
Tananan tsaye har akafara Kiran sallar magaruba bata matsa a inda takeba amma zuwa lokacin tafara kuka sabida rabonta da abinci tun karin safe  kukantane yajanyo hankalin wata mata meseda kunu da kosai kanta  .kobaa fadamataba tasan yunwa ce tasa yarinyar kuka dan haka kunu tazubamata kunun da kosai taje gurinta tabata kallon ilham datayine yasa zuciyarta tashi sabida ilham inbanda warin rana da karnin miyau ba abinda takeyi ga wani zarni daya cika gurin asaka makon fitsarin datayi ajikinta
 Seda me kunun tayi dana sanin bata kunun a robarta. Itako ilham nagani kunu  bata tsaya  tunanin komai takafa robar abakinta batadamu     da zafin kununba tashanye tas sannan taci kosan ay tana gama sha takwanta agurin sebacci da gudu me kunun tabar gurinta domin lamarin ilham yafara Bata tsoro  Yarinya dakyau kamar    aljana sannan gata nakasasshiya ay bata bata lokaciba tahada kayanta tabar gurin




Love you all 😘maman yusuf
[3/13, 07:08] Ussaina: *ALLAH GATAN BAWA*✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨

_Writting by Zahra Muhammad mahmud_


*Page 26*



Tanan kwance agurin kowa yazo wucewa sede yamata fatan samun lafiya domin azatonsu mahaukaciyace
Tana gurin har zuwa karfe daya nadare se alokacin tafarka koda tafarka Bata tsorataba cigaba kawai tayi da tafiya duba da yadda garin kano dan musa me kwankwasiyya yawadatata da haske dan haka ilham tafiya kawai takeyi batunanin komai ba mutane sede jefi jefin motoci masu wucewa
Duk motar datazo wucewa nacikin motar kallon mahaukaciya sukemata bare yanzu data cire hijab dinta acan inda tasha kunu gashin kanta awaje yake gashi da yawa har gadon bayanta .tayi tafiya meyawa har tazo dai dai gadar yankura anan tayada zango ajikin gadar daga gefen titi baccine yasake dauketa agurin ba ita tafarkaba se da garin Allah yawaye shima tafarkane asakamakon hayaniyar mutanen dataji akanta bude ido tayi ahankali sannan tamike zaune tana kallon mutanen dakowa yatoshe hancinsa asakamakon warin kashin datakeyi domin kuwa kashi tayi akwance
Korarta mutanen suka farayi haka tamike tana kuka ko tausayinta basujiba wata bayarabiya harda marinta tana harkadata. Jinsaukar marin akumatuntane yasata sakin kuka me tsanani gami da kwasa da gudu ay tana fara gudun mutanen suka fara dariya sabida gudun abin dariyane koni naso nadara kawai dannasan wacece ilhamne shine yahanani gudune irin naguragu tana fara gudun tafadi kanta yaji ciwo amma bata damuba burinta kawai tagudumma matar domin tunda tazo duniya baataba marintaba se ranar
Seda taci gudunta me isarta Wanda duk inda tawuce da gudun dariya jamaa keyi dan gudun abin dariya ne sannan ta tsaya tana haki yunwa tafaraji danhaka tafara neman abinci tahanya bin guriguri tana kuka kofar wani restaurant ta tsaya tana kuka to aciki akwai costomers suna brakefast acikinsu akwai Wanda yafara amai sabida ganin ilham dayawa daga cikikuma fita sukayi suka bar abincin ganin haka yasa matar me gurin tasowa takama ilham da duka bata barta seda tamata shegen duka sannan takoma ciki tadauko ruwan wankewanke ta kwaramata zuwa lokacin inka kalli ilham bazakace itabace sabida gaba daya fuskarta ta kumbura dan duka
matarce tafara balai dan ubanki gobe ma kikara zuwa kofar shagona ki korar min costomers mayya kawai wuce kibani guri. ilham nakwance agurin sabida jikinta yayi tsami ga yajin ruwan data watsamata yashigarmata ido da duk inda taji ciwo kuka kawai takeyi ganun ilham Bata da niyar tashi yasa matar janta akasa seda tayi nisa da ita sannan ta wurgar da ita cikin wata kwata Allah sarki ilham marainiyar Allah.




love you all 😘maman yusuf
[3/13, 07:08] Ussaina: *ALLAH GATAN BAWA*✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨


_writting by Zahra Muhammad mahmud_


*Page 27*


*Bayan shekara biyu*


Zuwa wannan lokacin duk Wanda yasan ilham baze ganetaba sabida gabada takoma tamkar mahaukaciya sabida datti gashin kantama yadankare akanta kamar bata dashi
Rayuwace takeyi me cike da tausawa sabida ko abincin dazata ci yanzu yakoma sede tabi bola tasamu hakanne yasa duk Wanda yaganta yaga mahaukaciya
Har yanzu atiti take kwana ko kangon da baa gama ginashiba.
Yanzu shekarunta sha uku kuma awannan lokacinne Allah yakawomata jinin al'ada(wayyo Allahna)gaba daya jinin yagama bata mata jiki sabida jinin irin me rushing dinnanne ga azababben ciwon mara Wanda inya murda mata sede taita birgima har Allah yayayemata kuma koda jamaa sunga tana birgimar babu me bi takanta dan azatonsu duk acikin haukarne
Shiyasa yanzu warin datakeyi namusammanne ko ina tabi korarta akeyi babu me Jin kanta kuma lalurarta se abinda yakaru basauki sena Allah.

       ***********
Zuwa yanzu ameera na js2 sabida megari yamaida ita makaranta kuma har yanzu bata manta da yar uwarta ilhamba shiyasa kullum megari cikin bada cigiyarta yake sabida megari idan akwai abinda yatsana shine ganin ameera cikin damuwa  Sam baya kaunar bacin ranta dan inkaga ameera yanzu bazaka taba cewa ba yarsa bace kuma suma matansa kowacce cikin kyautatamata suke ba banbanci. Rayuwar ameera de se sonbarka matsalarta daya ce rashin yaruwarta ga doctor kullum cikin yimata ayke yake duk week-end kuma yana hanya dan yanzu sunsaba dashi kamar dan uwanta haka tadaukeshi shima kuma zallar tausayintane aranshi dakuma wani abu Wanda yabarma ranshi sezuwa lokacin dazata mallaki hankalin kanta.


love you all 😘maman yusuf
[3/13, 07:08] Ussaina: *ALLAH GATAN BAWA*✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨


_writting by Zahra Muhammad mahmud_

*page 28*




*Anwar  umar mutallib*


Dane ga shugaban kasar nigeria meci ayanzu wato Alhaji umar mutallib manumfashi.shekarunsa basu wuce 35 ba dane  daya tamkar dubu agurin mahaifinshi subuyu Allah yaba iyayenshi shine nafari agurin iyayenshi se kanwarsa mebinsa khadija wacce taci sunan mahaifiyar alhaji yasa suke cemata ihsan.
Mahaifiyarsu hajiya zainab ita kadaice agurin mahaifinsu shiyasa tazamana itace first Lady of Nigeria. Hajiya zainab macece kyakkyawa domin ita asalinta mutanen labanonce tsayawa fadin kyau irinna hajiya zainab zezama kauyanci sabida duk wani abu da ake kira kyau ga y'a mace takai karshenshi don kyannatane yake karasawa mijinta kaunarta.duk da kyau irinnata se Anwar yace bata iyaba domin yafita kyau nesa bakusaba mutumne shi miskili naajin farko kasaita gareshi kamar jinin sarauta   yayi karatunshi tundaga pramary zuwa secondry school a turkish school dake abuja inda yawuce da karatunshi na jamia a can kasar mascow har zuwa yanzu daya hada masters dinshi akan fannin petro chemical engenearing
Zamansa akasar waje yasa yafara neman mata tun yanayi kadankadan har yakai matakin daze hada mata uku akan gado daya kuma yayi amfani dasu batare daya gajiba sabida Allah yayoshi acikin jerin maza mabukata koya shaawa tamotsa masa baya iya hakura seya biya bukatarsa
Abokanshi nacan sunyi iya yinsu wajen ganin sunkoyamasa shan giya da coccane amma abin yaci tura domin shi baya kaunar abinda zegusar masa da hankalinsa. Anwar Wanda akafi sani da the most handsome domin haka kowa yake kiranshi sabida kyan Anwar ko ajinsin Larabawa da indiyawa se an tona zaa samu irinshi (kunsanme ? Duk kyansa bekai ilham ditaba)yana da gashi akansa metarin yawa yanayin gashinnasa tamkar arnav din kushi koya yamotsa bakinsa se beauty point dinshi yafitu sosai farine shi sosai kuma yanada tsayi amma bacanba sannan yanada faffadan kirji Wanda yake amurde hakan yasamo asaline asakamakon daga karfe daya keyi arayuwarsa baya kaunar komai sama da iyayensa da kuma kanwarsa kuma duk abinda zeyi yana bashi lokacine lokacin nafita shima yabar abin misali inze gana dawani zece yabasa minti biyar tofa dazaran minti biyar tacika tashi zeyi yafice yabaka guri baya wasa da lokaci hakane yasa baya wasa da ibada duk iskancinsa baya barin sallah
Anwar mutumne shi Wanda beba soyayya muhimmanciba  ko matan dayake hulda dasu basonsu  yakeyiba  kawai for personal used yaajiyesu dan ko numbarshi basudashi
Ko bayan yagama karatu mahaifinshi yayi yayi dashi yadawo gida amma yaki kullum ansa dayace am on my way dady very soon tun mahaifin namishi uzuri har abin yafara Bata mishi rai dan haka yasa masu bincikamasa me Anwar yakeyine daya hanashi dawowa gida duk Wanda yasa binciken ansa daya suke Bashi neman mata yakeyi wannan batu bakaramin tada hankalin mahaifinshi yayi ba domin dede gwargwado suna iya bakin kokarinsu gurin ba yaransu tarbiyya dagashi har mahaifiyarsu kudi da mulki besa sunyi wasa da tarbiyarsuba hakannema yasa bekai ihsan karatu kasar wajeba don yana gudun zamani amma yau abinda Anwar zemasa kenan. Hakanne yafusatashi yakirashi awaya yana gaisheshi amma ko amsawa beyiba illa cewa dayayi cikin muryar fushi wacce Anwar bedauka dad dinsa yanada itaba. Duk abinda kakeyi anan inada labari kuma wallahi duk hukuncin dana dauka akanka ka kuka da kanka dan hukuncin baze maka dadiba danhaka duk abinda kakeyi kabarshi kabiyo jirgi ranar asabar kasauka a kano sabida nima zanje kanon wani taro semu taho abuja tare kuma wlh inbaka tahoba daga yau kanemi wani uban niba mahaifinkabane.yana kaiwa nan yakashe wayarshi yana huci
zuface tashiga karyowa Anwar kamar ruwa domin iya tashin hankali yashigeshi   jifa yashigayi daduk abinda hannunsa yakai kai yanayi yana fadin wayyo allahna wanne munafikine yahadani da dad. Hakade yagama dan matashin haukarsa yafara shirin barin kasar domin saura kwana biyu asabar din tacika.

        **********

         *Asabar*


da misalin karfe goma sha daya nasafe jirgin su Anwar yasauka  à filin jirgi na malam aminu kano tun kafin zuwan jirgin airport  din cike yake da security takoina sabida Anwar koda saukar jirgin shine mutum nafarko daya fara sakkowa wayyo Allahna sisters kuzo kutayani gani sanye yake cikin blue jins da farar shet sannan yadora katuwar rigar  sanyi baka wacce tsayinta yakai har guiwarsa kanshi yasa hular sanyi fara yayinda yanade wuyansa da irin wannan siririn abunnan namaza(bansan sunanshi ba amma wani lokacin har rawani sunayi dashi)red colour  inkuka ganshi bazaku so kudauke ido akanshiba domin yahadu saukowa yafarayi cikin tafiyarsa ta kasaita tunkafin yagama sakkowa aka shimfadamasa red carpet yasauko akai yaci gaba da tafiya har zuwa inda aka ajiyemasa motar daze hau wata bakar jeep ce kirar kamfanin Ford tinted ne gilas din motar murfin baya aka bude masa yashiga sannan akarufe sauran motoci kimanin guda goma sha daya suka rufawa motarsa baya yayin da gurin yacika da jiniya duk inda suka wuce kallonsu akeyi yayin da duk ababen hawa nakan titi suke basu hanya ahaka har suka iso govement house koda isowarsu wani kayataccen falo aka saukeshi Wanda ga abincinan na alfarma yaci iya cinshi yabar nabari jus kawai yasha sabida yaci abinci ajirgi nafeesace tayi sallama tashigo cikin falon y'a ce game girma gomnan jahar kano cikin ado nadaukar hankali se kwarkwasa takeyi Wanda shiwanda akeyi dominsa ko kallo bata isheshiba ita kuwa Allah ne yajarrabeta da sonshi tunda dadewa shiko basonta yakeyiba
koda tagaisheshi dakyar yaamsa suna nan zaune akayi ringing bel ita tabada umarnin ashigo wani sojane yashigo yadan kame gami da sarawa sannan yace ranka yadade  his highness yanason ganinka mikewa yayi kawai batare da ya amsaba yabi bayansa har zuwa wani falon. Mahaifinshine aciki tare da gomna suna hada ido da mahaifinsa yaji gabadaya kunya takamashi dakyar ya iya gaishesu cikin sakin fuska suka amsa har mahaifinnasa kamar bawani abu dayamasa gomnane yamatso yarungumeshi ajikinshi yajashi har kan kujerar dayake zaune yana fadin haba dan gidan dady yau gaisuwar daga nesace bazaazo jikin dadynba ko shide dukar dakai kawai yakeyi domin beson hada ido da mahaifinsa
bayan sundan taba hira megirma shugaban kasa yamike yace zewuce sabida yau yakeso yakoma abuja tashi akayi gaba daya harda gomna domin masa rakiya zuwa airport jerin gwanon motocine sunkai kimani guda talatin takoina jiniya ke tashi sukayoma shugaban kasa rakiya  ga garin akwai hadari sosai anfara yayyafi jamaa kowa yafake sekallon
Motocin akeyi kan kace me ruwa yabarke kamar da bakin kwarya
adede wannan lokacin ilham natsaye abakin titin ruwa nadukanta amma bata damuba sabida hakan sabontane tananan atsaye har motocin shugaban kasa sukazo wucewa
gomna da shugaban kasane abayan motar yayinda  Anwar ke zaune agaba shida direba.
karar jiniyar da ilham tajine yasata firgicewa dan haka Bata bata lokaciba gurin fara gudu gashi ana ruwa. Kamar ance Anwar yawaiga inda take haba mezeyi inba dariyaba dan abin gwanin bandariya dariya yake har rike ciki yana kwanciya  Jin dariyarsane yasa mahaifinsa kallonsa da gaggawa Wanda shi tuni yamantama da mahaifinsa yake tafe. Adede lokacin ilham santsi yakwasheta garin gudu tayi samasama tafado kasa haba Anwar ay har ihu ga kwalla data cikamishi ido dan dariya  mahaifinsa mamakine yakamasa karara sabida tunda aka haifi Anwar betaba dariyar dazakaji sautintaba se yau
Anwar Wanda garin dariya har pointing dinta yakeyi batare dayasaniba hannunsa mahaifinsa yakalla dan ganin abinda yake yiwa dariya har haka  Allah sarki ilham yagani wacce zuwa lokacin harta mike tacigaba da falla gudunta na guragu ay Anwar nagani shima yacigaba da dariyarsa shiko mahaifinsa wani murmushi yasaki Wanda kai tsaye zamu iyan kiranshi namugunta  wayarshi yadaga yakira motar bayansu yabada umarnin adauko mishi ilham asa amotar Wanda Anwar dan dariya shibemasan mahaifinnasa yayi wayarba haryadena ganinta bedena dariyaba ahaka harsuka iso airport  ko gurin shiga jirgi anriga shigewa da ilham dan haka begantaba ahaka harsukayi sallama da gomna suka shiga jirgi  gurin zamansu daya da dadinsa amma koya yatuna yadda ilham tafadi har fadowa yake akujerarsa dan dariya sude security se kallon abin mamaki sukeyi  itako ilham tunda akadaukota amota take bacci sakamakon heater dake kunne amotar har akasata ajirgi bacci take  shiko mahaifin Anwar kallonshi yayi fuska dauke da murmushi yace aransa my son kenan ay dariya yanzu kosomata




love you all 😘maman yusuf

No comments:

Post a Comment