Monday 27 March 2017

SURBAJO

[3/27, 09:15] zahra Muhammad mahmud: πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€
         *SURBAJO*
πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€


Zahra Muhammad mahmud



*page 51-52*



Alameen yaisa gida Lafiya ga mamakinsa Aishan senan nan take dashi ga gida yayi fes komai gwanin Shaawa

Dakinshi yawuce yana shirin shiga wanka itama tashigo dakin karasawa gurinshi tayi tafara tayashi cire botir din rigarshi

Toilet yanufa ahankali aisha tace honey nazo natayaka wankanne dasauri alameen yakalleta dan abun bakaramin mamaki yabashi ba
Murmushi yayi yace no nagode carab tace ay dole kace ka godemana da amaryarkace Yar cikinka tace zata tayaka dagudu zaka amince
Nice karaina baka kuma daukeni maceba to Wlh bari kaji infadamaka nima macece babu abinda zaa nunamin daga fari se gashi amma Bade diriba

Abun dariya yaba alameen ganin yadda take cika tana batsewa dawowa yayi yasureta suka shiga wankan tare koda suka fito shiryata yayi tamkar yadda yakewa surbajo sannan shima yashirya

Falo suka dawo sukaci abinci atare abun gwanin Shaawa mikewa yayi zefita aisha cikeda shagwaba tace itama zata bishi bamusu yace tazo suje

dasauri tadauko gyalenta da takalmi suka fice
Baniba hatta masu gadin gidan ganinshi sunjero da aisha seda abun yabasu mamaki se kallonsu mukeyi

Key yaamsa ahannun direba yau dakanshi zeyi driving
gaban mota yabude mata tashiga sannan shima yazagaya mazaunin direba yaja suka bar gidan

Guraren shopping yakaita suka yo shopping aisha komai guda uku take dauka Wanda KO baa fadamasaba yasan ita da aminanta take daukarwa
Shiko iyayensa da nata yayiwa shopping

Biyan kudin yayi suka fito kai tsaye gidansu Aishan sukaje
Mamanta kamar zata goyasu dan rabonta da ganin alameen tadade gaisheta sukayi sukadan taba hira sannan yaajiyemata siyayyar dayayomusu suka tafi tanata samishi albarka

Daga gidan su aisha gidansu yanufa
Aisha ganin yabi hanyar gidansune tajuyo tana kallonshi tace honey darefa yayi muwuce gidamana
KO kallonta beyiba yacigaba da driving dinshi

koda suka shiga gidan kowa mamakin ganinta akeyi dan rabonta da gidan tun ranar daaka kaita gaida iyayen miji ranar auransu sama da shekaru masu yawa

Ko afuska bawanda yanunamata sauyi cikin faraa suka amsheta sunjima agidan sannan suma yaajiyemusu tsarabarsu suka musu sallama suka wuce gida

Daren ranar alameen da aisha sunsha soyayya wacce rabonsu dashanta tun ranar da aisha tayaudareshi

soyayya akasha batawasaba dan sanadin hakan har surbajo tadunga kiranshi awaya ganin bekirataba amma bedagaba tabashi missed calls yakai ashirin amma bedagaba
Abun yabatawa surbajo rai wato dan yana tare da tinkiyar matarsane yaki daukar wayarta ranta bakaramin baci yayiba dan dama surbajo akwai kishi

koda safiya tayi alameen Yaga missed calls din babynshi hankalinshi bakaramin tashi yayiba yasanta sarai akwai daru
kiranta yashigayi amma taki dauka karshema a black list tasashi
Hankalinshi bakaramin tashi yayiba rasa inda zesa kanshi yayi

ranar yashirya yajibgi tsarava yanufi makarfi da isarsa murna suka dungayi da ganinsa babu kamar ardo hirar yaushe gamo suka dungayi
Har zekira surbajo yabata mahaifinta su gaisa to ba network kuma KO akwaima yasan va dauka zatayiba amma dabarace tafadomasa wayarshi yadauko yafara yima ardo vedio yace yafadi abinda yakeson fadawa surbajo inyaje zekaimata tagani ayko ardo dagewa yayi yadunga yimata nasiha cikin harshen fillanci seda yakwashe 30 minutes yana jawabin sannan yagama

se laasar alameen yamusu sallama yatafi bayan yacikasu da abun arziki albarka suke tasamasa


yana isowa kaduna gida yawuce dan yagaji sosai Kiran surbajo yashigayi amma bata shiga yadamu sosai kuma baze jure rashin Jin muryartaba

adaddafe yayi sati guda mutumin dazeyi wata daya amma dakyar yayi sati sabida surbajo taki daga wayarshi Sam

shiryawa yayi zekoma Aishan  kuka tasamishi akan itama yatafi daita sosai take kuka dakyar ya rarrasheta akan tayi hakuri in yaje zedawo da surbajo seyatafi da ita dakyar taamince wannan karon su Aisha harda kuka alameen zetafi shi abunma dariya yake bashi dan shagwabar datakeyi KO kyau bata mata dan Bata sababa

haka yatafi yabarta cike da kewarsa

surbajo nakwance afalo tana kallo taji anbude kofa dasauri takai dubanta gurin alameen ne atsaye yana kallonta sunkuyar dakanta tayi tana wani killer smile aranta tace kai mata kissa tayine dama dabiyu taki daga wayar tashi dantasan baze iya jure rashin Jin muryartaba Wanda tasan yun hakan zesa yadawo gareta da gaggawa murna tayi sosai yayin da gefe daya kuma take godewa fatee benee data koyar da ita irin hakan

shine yakatsemata tunani dacewa baby bako oyoyo ko ko baya murna da zuwana

murguda baki tayi tace har kagama soyewar da wannan basamudiyar matar taka ayna dauka seka shekara kamin kadawo

alameen yace alamarin mata se Allah invakayi ahankaliba sesu haukata
.karasawa gurinta yayi yahiga rarrashinta besha wuyaba tasakko dama fushin na karyane yagama goge laifinsa Tunda yadawo gareta
[3/27, 10:07] zahra Muhammad mahmud: πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€
        *SURBAJO*
πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€


Zahra Muhammad mahmud


*page 53-54*


Watan haihuwar surbajo yatsaya kuma taje Γ mmata scaning ance namijine dan haka alameen Baya nisa da ita gudun kar haihuwa tazo bayanan

Wata ranar jummaa dasafe surbajo tafara jin ciwon nakuda amma basosaiba haka tadunga daurewa gudun karta dagawa alameen hankali hardare bata denajiba ciwonma sekaruwa yake

Ahaka harsuka kwanta tana ganin yayi bacci tamike tasoma safa da marwa dan ciwon sosai take jinshi sewajen karfe hudu na asuba alameen yafarka yaga bata kan gado dasauri yadiro daga gadon akasa yaganta atsugune se gumi takeyi tana nishi hannunta rike da kwankwasonta
Dasauri yarukota yana tambayar Lafiya

Mararta take nunamasa dasauri yasaka jallabiya itama yasamata hijab yakinkimeta yakai mota sannan yadawo yadauki kayan haihuwa asibiti yakaita mafi kusa dasu dan gani yake gidan Usman yamasa nisa

likitocine suka rufu akanta yayinda alameen addua kawai yakeyi Allah yasauketa Lafiya

Karfe shida nasafe Allah yasauki surbajo Lafiya yayinda tahaifo danta kyakkyawa mekama da alameen komai nasa na alameen ne

nurse ce tazo tama alameen albisheer gamida mikomasa yaron

allahu akbar Allah megirma alameen har hawaye yayi nafarincikin samun dan dayayi yaronko sekallonsa yakeyi idonsa tar akan ubansa

Alameen tambayar surbajo yayi nurse din tace tashiga wankane yanzu zaa fito da ita dakin hutu kosawa yayi yaganta Yaga irin murnar dazatayi

Baajimaba aka fito da ita tana zaune akan keken daake tura marasa Lafiya tana ganin alameen tasoma murmushi shima shiyakeyi rikemata hannu yayi da hannu daya dayan hannun kuma yana rungume da dansa

Dakin hutun aka kaita tadan huta amma lafiyarta kalau babu mecewa ita tahaihu ga yaron kato dashi masha Allah

alameen mikamata yaron yayi yace baby kinga kyautar Allah ko karbar yaron tayi tana kallo harda hawayenta lokacin da yaron yasoma dariyar kuda da jarirai sukeyi alameen dasauri yadaukeshi hoto
Nande sukasa yaron atsakiya suna kallo surbajo takaiwa alameen duka tace Wlh dear kayimin wayo duk wahalar nan danasha amma babyn dakai yake kama
Dariya yayi yarungumota yace haba baby daga jikinafa yafito kinga ko ay dole yamin kara yasan nima wahalar nayi nande sukai ta abin dariyarsu karfe takwas likita yasallamesu kai tsaye gida suka nufa
Da isarsu yafara kiraye kirayen waya yana sanarwa surbajo tahaihu yan kaduna har hoton babyn yadunga turamusu

Usman jiyayi  kamar shi akayiwa haihuwar dan tausayin alameen yakeji  ace ashekarunsa KO haihuwar fari beyiba
kayan barka suka siyo shida Hafsat cikin bayan motarsa harda kayan wasa suka nufo gidan masu jego
nanfa Hafsat tadunga yiwa surbajo tsiya wuni sukayi agidan har Usman yayinda su Fatee benee sune kan gaba kawa tahaihu

daga kaduna daddy yakira alameen yace gobe yadawo da surbajo gida sabida akula daita dakyau amsawa yayi cike dajin dadin irin soyayyar da iyayensa kema surbajo

washe gari dasafe dakanshi yashirya iyalinshi suka daga zuwa kaduna

Sun Isa Lafiya suna shiga falon gidan aisha ce zaune itada aminanta seganinshi sukayi yashigo rungume da jariri surbajo nabiye dashi abaya

dasauri aisha tamike bakinta har rawa yakeyi gurin tambayarsa
horney yaron waye wannan tana leka fuskar yaron dasauri taja da baya tanafadin pls alameen karka cemin yaronkane pls murmushi yayi yace why not zan ki fadamiki he is my son danane da babyna tahaifamin jiya
wata gigitacciyar kara tayi tayanke jiki tafadi dasauri aminannata sukayo kanta shima alameen gunta yanufa
surbajo ko amshe danta tayi tawuce part dinta hankalinta kwance

itako aisha Sun yafa mata ruwa amma abanza Bata farkaba dasauri suka sata amota suka nufi asibiti
seda likitoci suka jima akanta tafarko se kuka takeyi tana fadin wlh baze yiwuba dole nima kamin ciki nahaihu taya yarinya zatazo daga bayana amma ace harta haihu so biyu ni ko bari bantaba yiba

wuni Aishan tayi a asibitin sannan suka sallamota shiko alameen dama tun rana yabar asibitin sabida Mommy takirashi tace gidansu zekai surbajo kuma haka yayi zuwa yayi yadauketa yakaita gidan iyayensa

murnar dasukayi daganin jikansu nagurin alameen tanada yawa ga yaron har yafi alameen kyau daddy dakansa yamasa huduba

dangin mamanta ma baabarsu abayaba sunzo barka kuma kullum se sunzo wata mata aka dauko tanama surbajo wankan jego

gata bairin Wanda baa nunamata
 alameen yakoma gurin ayki se ana gobe suna yaduro

ranar suna yaro yaamsa sunan Yusuf sabida daddy yace kyan yaron yakai asamasa sunan Yusuf  sabida aynihin me sunan shima kyakkyawane fatansu Allah yasa yabiyo halin mesunan

fadin irin shagalin daakayi ranar sunan se data 1gb takare bangamaba😜
su Fatee sune agaba dan itama tazo sunan dan itama har gayya tayo na kawayenta masoya surbajo. su Eshat,maryam Taheer, Juwairiyyatu,zahra,hafsat daheer, lawisa,hameeda,ummu Yusura, Aunty Nafeesat Aliyu,maman Muallim,mrs lukman,ruky Afeshe, Ussaina  m lawan kai suna dayawa dan motoci sukayo sukazo taron sunan anci ansha anyi danasha inda taro yawatse cike da farinciki

se fatan Allah yaba mejego Lfy da yusuf


maman yusuf

No comments:

Post a Comment