Sunday 19 March 2017

SURBAJO

🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀
         *SURBAJO*
🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀


Zahra Muhammad mahmud 


Zahramuhammadmahmud.blogspot.com


*page 31-32*


Ankai amarya Lfy inda dangin mahaifiyarta suka kara yimata nasiha game da zaman gidan miji itade surbajo se kuka takeyi 

Kamin goma nadare kowa yawatse anbarta ita kadai Bilkisu ce tace mata takulle kofarta karta bude se intaji alameen ne ayko haka tayi kulle kofar tayi duk da bata iyaba seda bilkisun takoyamata

Gefen gado tasamu tazauna tadunga bin dakin da kallo irinna kauyanci komai yamata kyau sede ita wasu abunma batasan menene shiba 

Siket da rigane ajikinta nawani material purple colour semayafin data rufa dashi fari takalmin kafarta ma farine kanta ba dankwali sede farin ribom daaka kama mata gashi dashi 
Mikewa tayi tacire mayafin dan tagaji tunda aka fara bikinta take rufa mayafi to itade yau tagaji shiyasa tacire 

Falonta tadawo tazauna akan two sitter sanyin AC naratsata komai na falon yaburgeta 

zamanta bajimawa taji ana nurking din kofar mikewa tayi taleka ta ramin da Bilkisu tace tadunga lekawa 
Alameen tagani tsaye shikadai bude kofar tayi takoma gurin zamanta tazauna 
Da sallamarsa yashigo 
Suman tsaye yayi lokacin dayayi arba da surbajo tamasa kyau sosai musamman gashinta daya zuba har gadon  bayanta bakikkirin se shining yakeyi 

Ledar daya shigo da ita yaajiye sannan yasami daya daga cikin kujerun yazauna 

surbajo amare kallonshi kawai takeyi ba um ba umum shima itadin yake kallo murmushi yayi yace baby na babu ko gaisuwa irin wannan shan kamshi haka konayi laifi ne 
murguda baki tayi tace yoto shikenan sokake insaki baki inta zuba agabanka kaidin daba kunyace gareka ishashshiyaba yanzu kace zaka daukeni kamar wata yarka to aradu kakiyayeni kajide nafadamaka tafadi Tana Kara daure fuska ita ala dole batason raini 
dariya zancannata yabashi babu abinda yake burgeshi da ita irin son girmanta 

mikewa yayi yakoma kujerar datake kai dasauri tamike tana shirin barin gurin cikin zafin nama yarikota tafado kanshi 
Riketa yayi tayadda bazata kwaceba sannan yace baby na Wlh bakida kunya ke kodan irin kukannan da amare keyi in antafi anbarsu bakiyiba Dan mayafin dasuke rufe fuskarsu dashi shima bakiyiba kin yiwa ango magana dawuri se ansiyi baki shima duka bakiyiba se rashin kunya kikemin to ki kiyayeni ko yanxu nayi Maganin rashin kunyar taki yafadi yana shafo gashin kanta 
Surbajo kokarin mikewa takeyi Amman yahanata ayko budar bakinta se cewa tayi hddijan amma aradu kado akwai raini yo inbanda abunka ko kukan nakeyi aka kawoni gidannan me shegen kyau ay aradu nadena kukan kuma wannan kayan kyalekyalen duniyar inna rufe idona ay bazan gansu da kyauba  kuma dakake cewa nayi magana da wuri badole inmaka magana da wuriba gudun kar kace zaka lashemin bakina kamar tsohon Maye ni wallah narasa mekakeji acikin lashewa mutane baki kallonshi tayi sannan tace Don Allah kado mekakeji inkana tsotsewa mutane baki batagama fadin mezata fadaba yahada bakinta danashi yashiga kissing  besaketaba seda yaji dakyar take numfashi kallonta yayi yaga jikinta yamutu murmushi yayi yace baby to kinji abinda nakeji inna lashewa mutane bakin 

surbajo baki yamutu mikar da ita yayi suka shiga kitchen dinta dake falonta yadauko plate da cup suka dawo falon ledar daya shigo da ita yadauko yajuye naman kaza a plate din sannan ya tsiyayamusu fresh milk a cup yamatso dasu gabanta wayyo surbajo idonki idon nama ay tuni ta watsake daga kasalar da yasamata takai hannu zata dauki naman caraf yarike hannunta yace au ci zakiyi batare danamiki tayiba wani kallon banza tawatsamasa sannan tace aa kallonshi zanyi kamar yadda kaima naga kanayi 
murmushi yayi yace inde zakici namannan to akwai sharadi inde kikaci sekin biyani  ko ajikinta tace inde biyane me saukine zanbiya koma menene bani naci murmushi yayi sannan yamikamata 

seda taji takoshi over sannan tahakura da naman sannan tashanye cup biyu na fresh milk din 

mikewa alameen yayi sannan yamika mata hannu takama yadagata toilet suka nufa brush yadauko yamiko mata bayan yasa maclean kallonshi tatsayayi danbatasan amfaninshiba mamakine yakama alameen  ganin surbajo batasan brush ba Amman bakinta baya wari kwatantamata yadda zatayi yayi wayyo shazumamu aytana gogawa taji zakin maclean tas tashanye kumfan hankalinta kwance tamika masa brush din yakaro mata wani 
Kobe tambayaba yasan shanyewa tayi dariya yashiga Yi sannan yasamata wani yacemata inde tasake hadiyewa mutuwa zatayi Dan yaganota mutuwace kawai kebata tsoro ayko bata sha dinba duk da ranta naso haka tadunga zubarwa har suka gama suka dauro alwala suka fito 

shiyajasu sallah rakaa biyu ta nafila bayan sun idar yamata tambayoyi gameda addini ga mamakinsa duk tabashi amsa dede sabanin Aisha 

mayafinta yabata tarufa yaja hannunta zuwa falonshi zaunar da ita yayi sannan yanufi dakin Aisha 
sallama yayi yashiga tanajinshi tamasa banza karasawa yayi yasamu guri yazauna bata gaisheshiba shiya gaisheta sannan yace tazo falonshi yanason magana da ita. 

1 comment:

  1. Nice blog keep on the good work

    Www.duniyanfasaha.blogspot.com

    ReplyDelete