Sunday 19 March 2017

SURBAJO

[3/18, 09:42] Zahra muhd mahmudπŸ’ƒ: πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€
        *SURBAJO*
πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€


Zahra Muhammad mahmud


Bismillahi rahmanir raheem
Allah yanufa nagama Allah gatan bawa Lfy
Seku sake sabon zama domin ga sabon darasi nakawomuku Innayi kuskure pls kutunasar dani



*page 1*

Sauri yake ya isa gida sabida yaga bakwai na safiya tayi. Tunda yaje sallar asuba bedawoba yana masallaci seyanzu
Addua yake Yi azuciyarshi Allah de yasa Aisha taga dama ta tashi daga baccinnata na qaddara
Tundaga shigarshi falo yafahimci adduarshi bata amsuba duba da ganin falon dayayi ahargitse kamar filin dambe duk da de dama sabon falonne zama acikin wannan yanayin

Jikinshi asanyaye yahaura sama inda dakinta yake
Ilai kuwa Tana kwance akan gado tana sharar bacci

Binta yayi da kallo zuciyarshi nakuna sabida tun jiya yashaida mata zekoma bakin ayki yau jirgin karfe takwas zehau zuwa phortercot amma shine ko tashi a bacci batayi ba
Inda sabo yasaba da halinta
Juyawa yayi yakoma dakinshi domin yayi wanka sabida yasan ko toilet dinta yace zeshiga yayi wanka seyakusa amai sabida karni da zarnin da toilet din yakeyi

Cikin Rabin awa har yagama shiryawa cikin kakinshi na soja
yayi kyau sosai sabida dama kyakkyawanne
Jakarshi yadauko sannan yadauko key din motarshi dakinta yanufa
haryanzu Tana bacci
Tashinta yayi
Koda tabude ido taganshi tsaki tayi sannan tace Amman wallahi al-ameen kaidan rainin wayone yanzu fisabilillahi ina bacci zakazo katasheni
Beyi mamakiba Dan yasaba dajin abinda yafi haka daga gareta
Nizan wuce yabata amsa
Kudi yaajiyemata kimanin dubu Dari uku a kan bedside drower  kallon kudin tayi awulakance sannan tace namenene wannan
Nacefanene kiyi amfani dashi kafin nadawo sabida inna tafi wata uku zanyi kafin nadawo
kan ubance inji Aisha tafadi tana sakkowa daga kan gadon sannan tace wallahi kayi kadan zakayi wata ukunne zaka mikomin 300k wallahi baze yiwuba tafada yayinda ta zubar da miyaun daya taru abakinta ajikin bangon dakin
Al-ameen bameson hayaniya bane Dan haka yace se nawa kike so
500k tabashi amsa bemusaba yadauko yakara mata sannan yace senadawo pls kiyimin addua
Agayas tabashi amsa gamida komawa takwanta
Fita yayi  wani kurtun sojane yazo dasauri yaamshi kayansa yasa aboot sannan yabudemasa bayan motor yashiga sannan Shima yazaga mazaunin direba yatada motor sukafita yayinda motoci biyu na sojoji sukasa motor atsakiya suka nufi Airport

suna zuwa kai tsaye jirgi yashiga Dantuni aka gama shirya komai
jirginsu yadaga zuwa rivers state

Safe trip  alameen


Love you all Maman Yusuf
[3/18, 09:43] Zahra muhd mahmudπŸ’ƒ: πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€
          *SURBAJO*
πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€


Zahra Muhammad mahmud



*page 2*



Tunda alameen yafita taci gaba da baccinta bata tashiba se Tara sannan tamike tashiga 🚽 tayo alwala tayi sallar asuba 😳


Tana idarwa kitchen tanufa madara ta kwaba akofi da Milo tazuba ruwan sanyi tajuya yayi kauri kamar chocolate
Tadauko gorar faro tadawo falo tafarasha
Aduniya babu abinda Aisha ta tsana irin girki Sam batason yinshi shiyasama bata iyaba

Zamanta keda wuya taji ana ringing bell dasauri taje bakin kofar taleka Dan ganin waye
Ihu tasa tun kafin ta bude kofar
Tana budewa suka rungume juna ita da bakinnata kawayentane su biyu
Kai tsaye dakin Al ameen tamusu masauki dan batason su rainata insukaje nata dakin
Afalonshi suka zauna hira suka shigayi dawadda tadace dawadda bata daceba suyi gulmar wannan suyi ta waccan
Can kuma tafara basu labarin yadda suke kwanciyar aure da mijinta kamar yadda suka saba (waiyyazu billah)
Shewa suke kawai suna kara zugata suna fadin eshat baby baki da wasa
Dariya tayi tabasu labarin yadda suka rabu yau da alameen
Daya daga cikin kawayennatane mesuna Ruky tace wo mutuniyar kina wuta muna binki da petur ina namu salary din tunda kin tatsa muma seki sammana koya kikace zuly baby
A wannan gaskiyane wacce aka Kira da zuly tabada amsa

eshat ce tafara mgn haba sisters harse kun roka ay kunwuce hakan agurina danhaka ku kwantar da hankalinku nifa wlh kunfiyeminshi so dubu agurina Danni Al ameen dashi da banza duka daya Suke. Kuma sabida nasan zanbaku naku kasonne yasa nace seyakaramin kudin Dankaka zanbaku 200k kuraba
Ihu sukayi suka rungumeta suka hada baki gurin fadin heyyy se madam Allah de yabiya Hajiya.

*ASALIN LABARIN*

al-ameen  jibrin sulaiman shine cikakken sunanshi matashine Dan shekaru 35 da haihuwa. dane ga rt major general jibril sulaiman
Mahaifinshi Dan asalin garin kanone awata anguwa daake Kira lungun gabari canne asalin tushensu amma sanadin aykin soja yasa yadawo kaduna da zama a malali yake da zama alayin sultan road
Hamshakin mekudine ajihar kaduna domin ajerin masu kudi nagarin in akace daya to tabbas shine nabiyu
Matarshi daya mesuna Hajiya binta suna kiranta da umma yaransu hudu. Kabeer shine nafari sannan alameen se munawwara da autarsu amal

gidan alhaji jibrin gidane gidan tarbiyya Dan yaransu gaba daya babu mehalin banza
Mahaifiyarsu nabasu tarbiyya Dede gwargwado kudi besa tayi watsi da tarbiyyar yarantaba
tunbayan da mahaifinsu yayi rt yakoma fannin business nakasa da kasa yanada kamfanoni a fadin jahohin nigeria mutumne shi metsoron Allah bashida buri dawuce a yaransa yasamu megadonsa a gidan soja kullum adduarshi kenan inda Allah yataimakeshi ya bashi alameen
tunda alameen yafara mallakar hankalin kanshi yaji yana shaawar zuwa aykin soja
Koda yatuntubi mahaifinsa da batun bakaramin farinciki yayiba
baayi satiba yasamomishi aykin dayake akwai hanya
shiko kabeer accounting yakaranta yanzu haka yana ayki a cbn yanada mata daya Da yaronshi guda daya mesuna Waleed kasancewar sunan abbansu yaci
munauwara kuwa yanzu Tana js3 yayinda auta amal ke primary 4

tunda alameen yafara aykin soja gabadaya hankalinshi yamaidashi abangaren aykinshi kullum burinshi yataimaki kasarsa

lokacin a kaduna yafara aykin kamin ayi posting dinshi zuwa Abuja

kamar kullum yauma yataso daga ayki da misalin karfe shadaya nadare a nda yake aykin dan haka ta Badarawa yabiyo dan zefi mishi saukin isa gida
 yawuto bustop kadan Dede galadima road jikin katangar gidan Baba boss yaganta tsugune Tana kuka ga gurin yayi shuru babu mutane har yawuce seyaji yanason sanin meyasa ta kuka kuma take zaune abakin titi
ribas yayi yadawo gurinta layin galadima road din yashiiga Dede gidan kallon kwallo yayi parking sannan yafito yatako da kafarsa zuwa inda take
sallama yamata agigice tadago kanta tana kallonshi kara matsawa kusada ita yayi yace yanmata meyafaru ne kika zauna anan kina kuka
ganin uniform din soja ajikinshi ne yasa tace aranta bari infada masa maybe yataimakamin
cikin kuka tace wlh mamanace tawuni yau Tana wankau har zuwa dare sannan tasamu kudin dazamuci abinci dashi  tunsafen bamuci abinciba shine yanzu ta aykoni insiyo garin rogon dazamu sha bansan yaakayiba kudin suka fadi shine nake kuka dannasan yau seta kasheni tafadi Tana sake rushewa da kuka
yaisa haka alameen yafadi yana kallonta balaifi tanada kyau dede gwargwado kuma yarinyace dabazata wuce 18years ba
yasunanki yatambayeta
sunana AISHA tabashi amsa
inane gidannaku nunamasa gidan tayi da hannunta danba nisa
taso muje yace da ita
zaromishi ido tayi tace wlh najemata ba sakonnan yankani zatayi Dan Allah kawuce ka kyaleni anan
bazata yankakiba nizan biyata kudin
Amman Anshi Wannan Kijewancan shagon kisiyomuku kayan tea 2k yabata godiya tashiga yimasa kamar zatayi sujada
dagudu ta tsallaka titin tasiyo kayan tean dawowa tayi tace nasiyo
gaba tayi yana binta abaya harsuka isa kofar gidan yace shiga kiyimin Sallama da mamannaki wucewa tayi tana murmushi Dan ita yau jitake kamar sallah saboda zasu sha tea Wanda rabonta datashashi tun kafin babanta yarasu yanzu ko kimanin shekararsa hudu da rasuwa 😜

mamanta Data fito taga sojane ke sallama da ita cikintane ya murda dakyar suka gaisa sannan yamata bayanin abinda Aisha tafadamasa
yakara dabata hakuri sannan yadauko kudi a aljihunsa kimanin50k  yabata yace tayi hkr duk sanda yasamu lokaci zedunga lekosu godiya Mama takeyi harda hawaye
sallama yamata yakarasa gurin motarshi yashiga yanufi gida


*wacece Aisha*


love you all Maman Yusuf
[3/18, 09:47] Zahra muhd mahmudπŸ’ƒ: πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€
          *SURBAJO*
πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€


Zahra Muhammad mahmud



*Page 3*



Aisha Bello Musa shine asalin sunanta haifaffiyar garin kadunace acikin anguwar Badarawa
Sunan mahaifinta malam Bello mahaifiyarta kuma sunanta maimuna suna kiranta da inna
Su ukune agurin iyayensu Aisha itace tafarko se kannanta guda biyu zaituna da Umar
Shekarar Aisha 18 mahaifinsu yarasu tun Tana js1
Mahaifiyar itace taci gaba da kulawa dasu har zuwa yanzu da Aisha ke ss2 awata makarantar gwamnati dake anguwarsu
Kannanta ma duk government schools sukeyi
Rayuwace suke mecike da kunci Dan abunda zasuci yafi karfinsu se inna tayi wankau suke samu suci abinci so daya arana
Aisha yarinyace me dogon buri arayuwarta kuma bata da godiyar Allah ko kadan
Tahadu dasu Ruky da zuly ne amakarantarsu inda halinsu yazo daya suka kulla kawance
Basuda ayki dayawuce suyi gulmar kawayensu har gida ansha biyo Aisha akan tayi gulmar wata akureta
Mahaifiyarta macece me sakaci da tarbiyar yaranta tun bayan mutuwar mijinta Wanda hakan yasamu asaline asanadin zafin talaucin dasuke fama dashi
kwasam segashi Allah yaturomusu alameen

Tunda alameen yatafi besake zuwa gidanba hasalima baya biyowa ta unguwarsu
Aisha tafi inna Damuwa darashin zuwannashi sabida tunda tadora ido akanshi taji takamu dasonshi
Har bakin titin anguwarsu take zuwa tatsaya kozata ganshi babban abinda yasa takesonshi mijine na nunawa kawa itako bata da buri dayawuce ace taburge kawayenta

Yau jummaa dawuri alameen yataso daga ayki ta Badarawa yabiyo har yawuce layin Su Aisha se yatuno da ita danshi harga Allah yamanta dasu tun bayan barinshi gidansu kwana yayi yashiga layin Dede kofar gidan yatsaya
Aisha ce atsaye azauren gidan Kai ba dankwali takira me agwaliba Tana siya tun agurin tafarasha fadi take Kai malam wannan da tsami
Mamakine yacika alameen ganinta dayayi ahaka gashi tasa wata πŸ‘• Data bayyana halittar kirjinta Dan har ta saman rigar ana ganinsu
Hon yamata dasauri takai dubanta inda taji hon din dagudu takarasa fitowa tanufeshi dasauri alameen yadauke idonshi daga kallonta sabida yadda take gudun yasa halittar kirjinta yin wani juyi na musamnam sabida Allah yawadata ta dasu
Karasowa tayi jikin motor Tana dariya
Sannu dazuwa soja sunan data kirashi dashi kenan
daurewa yayi yayi murmushi yace yauwa kanwata
Kashigo mana daga ciki tabashi amsa
Fitowa yayi suka shiga zauren gidan gaisheshi tayi
Yaamsa sannan yace
lalle bakyason shiri Dani tunda bakya muamala da dankwali kunyace takamata dagudu tajuya Tashiga gida tasako hijab sannan tafadawa inna sojan rannan yazo murnace takama inna dasauri tace uwaki Aisha shine kika barshi awaje yisauri kije ki kirashi yashigo dasauri tadawo gurinshi tamishi iso zuwa cikin gidan

Kan tabarmar da inna tashimfidamasa yazauna gaisheta yayi cike da girmamawa sannan yasanar dasu sunanshi dana mahaifinshi
Inna da Aisha ne suka hada baki gurin cewa Alhaji jibrin sulaiman de Wanda mukasani
mamaki tambayar tabashi sabida arude suka masa ita
eh shi yabasu amsa
Ajiyar zuciya sukayi dukansu daganan inna tabashi tarihinsu
yatausayamusu sosai inda daga karshe yayi musu alkawarin kulawa dasu

tundaga wannan lokaci alameen yamaida gidan inna kamar gidansu inyazo sallama kawai yake yashiga sosai yake musu hidima dantuni yasauyawa su Aisha makaranta ita da kannenta
Yayinda ita kuma Aisha kullum sonshi Karuwa yake azuciyarta
zuwa yanzu har waya yasemata iPhone6+ burin aisha yafara cika dantuni tasauya tayi kyau namusammam ga sutura Tana shiga ta alfarma bata da wata damuwa data wuce ta auri alameen
insuna waya so tari tasha yunkurin sanardashi halin datake ciki seta kasa
yau alameen ne yakawomusu ziyara bayan sungaisa da Inna ta tashi tafice dama zata barkane Aisha dawowa tayi kusa dashi tazauna tace Yaya alameen kamar yadda take kiranshi juyowa yayi Yana kallonta ganin yadda tanatsune yasa yagane mgnr dazatayi me muhimmaci ce sabida kwatakwata Aisha bata da natsuwa
yaakayine kanwata yatambaya
kunyace tarufeta amna bata dazabi dayawuce tasanar dashi
yaya Don Allah  zaka iya aurena? Jin tambayar yayi kamar saukar aradu danshi Sam bayason Aisha amatsayin wacce ze Aura danyafison mace me natsuwa
AA yabata amsa
kuka tasamishi tana Don Allah kataimaka kaaureni wlh tunda nafara ganinka naji inasonka katausayamin sonka zeiya kasheni wlh tafadi Tana ruko kafarshi
dasauri yamike yace amma Aisha bakida hankaliko taya zan iya auranki Bari kiji infadamiki bakya cikin jerin macen danakeson in Aura Danhaka bazan boyemikiba wlh banasonki kiyi hkr kinemi wani yana gama fadin hakan yajuya yafice daga gidan ranshi abace

innace tashigo taga Aisha kwance akasa dasauri takarasa kusa da ita ga mamakinta  farin kumfa tagani yana fitowa daga bakinta agigice tadagota ina babu numfashi ajiyeta tayi tafita tsakar layin Tana neman taimako napep akasamo akasa Aishan aciki inna Tashiga suka nufi asibiti


πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€
     *SURBAJO*
πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€


zahra Muhammad mahmud

*page 4*


Koda isarsu asibitin likitocine suka rufu akanta seda suka share awanni biyu sanna suka fito
Inna dasauri ta sha gaban daya fara cikinsu
Likita ya jikinnata
Dasauki yabata amsa
Sannan yace kibiyoni office  yajuya yanufi office dinshi inna nabinshi abaya
Bayan sunzaunane likitan yace mama meyasami yarinyarki hartake yunkurin kashe kanta tahanyar shan fiyafiya
Hankalin inna ne yatashi dajin abinda likita yace
Dakyar tabashi amsa da wlh bansaniba nide nasan bata dawata damuwa danko yauma lfy nafita nabarta dawowa nayi naganta a yadda nakawomuku ita
Murmushi doctor din yayi sannan yace kituntubeta tabbas akwai abinda yake damunta zaki iya zuwa kiganta dan tajima dafarkOwa godiya Inna tayiwa doctor din sannan tanufi dakin da Aishan take
Tana shiga suka hada ido daita dasauri takarasa bakin gadon tarukota
Kuka Aisha keyi tanacewa Inna nashiga uku alameen yace baya sona wlh inna Δ―nasonshi zan iya rasa raina akansa kitaimakeni Inna
Dankari itace kalmar data fito abakin Inna ajiyar zuciya  tayi sannan tace Aisha inbanda rigima irin taki inake ina Aminu yafi karfinki nesa bakusaba shine Dan shirme harda yunkurin kashe kanki sabida shi to wlh inbacci kike kifarka Aminu baze sokiba sabida ke ba tsarar auransabace
Kuka tasawa Inna kamar zata mutu hankalin Inna tash yayi rarrashinta tashigayi dakyar tayi shuru bacci yayi awon gaba da ita

Yau Monday Alameen ne yataso daga ayki gidansu Aisha yanufa sabida tunda yajita shuru kwana biyu bata dameshi dawayaba yasan tahakura dason datake mishi
Shiga gidan yayi kamar kullum kannen Aishan ne kawai agidan suma daalamun fita zasuyi ganinshi yasa suka nufeshi gaisheshi sukayi sannan yatambayesu inasu innanfa
Suna asibiti suka bashi amsa
meyafaru sukaje asibiti waye ba Lafiya
Aunty Aishane tasha fiyafiya tun shekaranjiya shine aka kwantardasu
innalillahi wainna ilahirrajiun itace kalmar da alameen yake nanatawa aranshi ko shakka babu yasan shine silar shan fiyafiyanta
Arude yatambayesu wanne asibitine
amsa suka bashi dacewa suma can zasu Kai abinci juyawa yayi yace to kutaho mutafi
Sun isa asibitin lokacin Aishan na bacci
Inna seda tayi mamakin ganinshi
Gaisheta yayi gami da tambayar me jiki
amsawa tayi cikin sakin fuska inda takara dabashi hkr abisa katobarar da Aishan tayimasa
Kunyace takamashi matuka inda yagaza cewa komai
Muryar Aishan ce takatsesu dacewa yaya kazo dubanine
dasauri yanufi gurinta yayinda Inna taja kannen aishan suka fice daga dakin
Gefen Gadon yazauna yakamo hannunta yarike yana kallonta tausayintane yakamashi ganin wai duk akanshi takeson barin duniya
Why Aisha? Itace yafurta
Kuka tasamishi tana Dan Allah Yaya ka aureni ko bakasona wlh ni inasonka inka gujeni bansan yadda zanyiba tafadi cikin kuka wanda yakarya zuciyarsa Dan alameen mutumne metausayi
rarrashinta yashigayi da kalamai masu sanyi
Yace kiyi shuru kinji naamice zan aureki amma sekin yimin alkawarin zaki cigaba dasona kobayan muΓ±yi aure Kai tadaga sannan tace har inmutu inasonka yaya nagode Da alfarmar dakamin
hira suka sha tasoyayya wacce azahirin gaskiya alameen tausayinta kawai yakeyi basoba kamar yadda tadauka se shabiyun dare yamusu sallama yawuce da kannanta yaajiyesu gida shima yawuce nasu Gidan da burin gobe zema mahaifinsa mgn akan zeyi aure danso yake cikin wata guda ayi auran dangani yake kamar Zatasake shan fiyafiyar.


maman yusuf
[3/18, 11:11] Zahra muhd mahmudπŸ’ƒ: πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€
         *SURBAJO*
πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€


Zahra Muhammad mahmud


*page 5*


Koda alameen yama mahaifinsa mgn akan yanason ya auri Aisha be hanashiba  sabida dama kullum adduarshi Allah yaba aminun matar daze Aura tagari
Mahaifiyarshima fatan alkahairi tamishi jin cewa Aishan bayar kowabace bedamesuba sude burinsu Allah yabasu zaman lfy

Tuni aka sallamo Aishan daga asibiti aka shiga hidimar biki sosai mahaifin alameen yasaki kudi ahidimar bikin
Kowa yaga hotonsu da alameen acikin kawayenta mamakin inda tasamoshi sukeyi itako Aisha abunnema yasamu se jijji dakai take ita adole tawucema saa

Inna tagyara Aisha sosai inda aka kawo lefenta akwati goma shabiyu cike da kaya na alfarma harda key din mota
Wayyo jamaa kuzo kuga murna gurin Aisha

Andaura aure akan sadakin naira dubu dari inda akabada dukiyar aure naira miliyan biyu
Jamaa Sun sami damar Halattar daurin aure aciki harda megirma gwamnan jahar kaduna inda shine yazama wakilin ango yaamsama alameen auren Aisha ahannun waliyyinta malam Adamu kani ga mahaifinta
bayan daurin aurene akayi walima da da misalin karfe biyar kuma sukaje dinner agaskiya shaanin bikin yakayatar anci ansha Masha Allah

Se misalin karfe takwas motocin daukar Amarya sukazo
Jamaa sukai tashiga da yan biki da yan gayyar sodi  Dan aje aga mazaunin Amarya

Aisha dakyar aka rabata da inna bayan tamata fada sosai Tana kuka aka shige da ita mota

Ankai Aishan gidan iyayensa tukun
Sosai suka tarbesu hannu biyu cikin mutunci dazaa tafi da ita dubu dari Momy taba Amarya
Sannan akawuce da ita gidanta dake rabah road babu nisa sosai dagindan iyayennasa
gidan yatsaru matuka sabida mahaifin alameen ne yayi komai yace Aishan base tazo dakomaiba

Yan rakiyar Amarya sunwatse inda yaraage daga Amarya se aminanta Ruky da zuly
Abokan angone suka rakoshi su biyar bayan raha dasukayi sukayimusu adduar zaman Lfy da, zuria dayyiba
sannan suka sallami su ruky da 50k sukadaukesu suka maidasu gida

umartar Aisha yayi dataje tayi alwala tazo suyi salla bamusu taje Tayo shidama tuni yayi
jansu sallah yayi rakaa biyu tanuna godiyarsu ga Allah
bayan sun idarne yake mata tambayoyi game da addininta
Yayi matukar mamaki daya tambayeta farillan alwala guda nawane tace guda uku inda farillan sallah suka zama asirin da bakwai 😳


Hankalinshine yatashi yashiga tambayar kanshi wacce irin Uwa nazabawa yaranane

Duk da yana cikin damuwa bebari taganeba inda yabarwa ranshi nanda wata biyu ze sata a islamiyya tamatan aure Dan baze zauna da jahilaba

Kajin daya shigo dasu yajawo gabansu inda yatashi dakanshi yadauko musu plate da kofuna
Aisha bazancan kunya zagewa tayi taci kajin sosai Wanda shi alameen abin kunya yabashi daga karshe yaso sashi dariya dangama Amarya Aisha hardasu tauna kashi hakade suka
Gama ci sukaje sukayo brush
Suna fitowa Aisha gado tanufa alameen ne yakwashe kwanukan yakai kitchen
Dakinshi yaje yasauya kaya zuwa na bacci sannan yakoma dakinta tananan kamar yadda yabarta
Cewa yayi bazaki sauna kayan jikin kibane kika kwanta dasu
wata Mika tayi gami da wata gyatsa mekarfi sannan tasakko akan gadon tanufi Wadrop Tana fadin wash wlh nagaji
Doguwar rigar bacci tadauko tasa duk yana kallonta sannan tazo tasake hayewa gado kayan data cire tabarsu akasa shi yakwashe mata yaadana shima hawa gadon Yayi bayan yakashe wuta yajamusu bargo. Kwanciyarshi keda wuya yaji Aisha tamirgino jikinshi inda tashiga bankaro kirjinta suna gogarshi
hankalinshine yafara tashi sabida betaba jinn hakanba
nande cikin dabara har tagama daga mishi hankali
wayyo abunka da sabon shiga yasha wuya kamin yasan hanyar daakebi shima seda taimakon Aisha
se alokacin tayi danasanin daukar shawarar su zuly dansune sukace tayimishi abinda tayi da farko
kuka tasamishi Tana rokonshi Allah annabi akan yayi hkr yakyaleta
ina alameen yayi nisa bayajin Kira duka dayakushi cizo babu wanda batamishiba amma abanza araina nace dama taya zeji bareshi dayake soja
besauraramataba se gefin asuba
kukako tayishi har muryarta ta dashe idanuwa sunkumbura baabinda yafi damunta irin breast dinta dasuke Mata zafi sabida sunji maza uwa uba kuma kasanta
shiyafara yin wankan sannan yahadamata nata ruwan dawowa yayi yabude bargon dasauri Aisha tarufe idonta Dan ba kaya ajikinta murmushi yayi yadaukota Kamar jaririya yakaita toilet jinta aruwan zafine yasata kwalla masa kara dan wani radadine taji yanashigarta
lallabata yashigayi har yasamu tabari yamata wankan yanadota atawul yadawo da ita dakin
itako har yanzu idonta arufe yake azuciyarta ko se tsinema su Ruky takeyi
agurin bacci yadauketa
shikuma kayansa yasauya yadauro alwala yatada sallah yana godewa Allah dayasa rawar kai darashin natsuwar Aisha besa ta zubar da mutuncinta
inda akarshe yaroki Allah dayasa sonta azuciyarshi dansuji dadin zama tare
be tashi agunba sedaeyayi sallar asuba sannan itama yatsheta tayi kuka tasamishi akan ita bazata iya tafiyaba daukarta yayi yakaita toilet din  tayi alwala yadaukota yadawo da ita doguwar riga yadaukomata da hijab tayi sallar azaune
bayan ta idar daukarta yayi yanufi Gado da ita kuka tasamishi tana bashi hkr dan tazaci zesake nemantane lakashemata hanci yayi yana murmushi yace matsoraciya babu abinda zanmiki bacci zamuyi
kwanciya sukayi yanata samata albarka abisa Kawobudurcinta datayi gidan mijinta ahaka har bacci yadaukesu yana rungume da ita


maman Yusuf

πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€
          *SURBAJO*
πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€


Zahra Muhammad mahmud


*page 7*


Basu tambayeshi meyasa baze tafi da Aishan ba sabida zuwa yanzu sungama fahimtar dannasu beyi dacen mataba

Tunda yatafi kullum seya kirata awaya intayi raayi tadauka inbatayiba kuwa inze kira so dari bazata dagaba
Haka inyasamu Hutu yazo gida sotari hutun baya karewa yake komawa sabida balain aisha
Rayuwa tayiwa alameen zafi awaje mutane yisuke kamar su goyashi sabida kulawa amma cikin gidanshi masaima yafishi daraja wannan wacce irin rayuwace  gashide yanada mata amma bata da amfani agareshi Allah kakawomin agaji.

*cigaban labari*

 Haka Aisha taci gaba da musgunawa alameen kullum Sabida shimutumne me hkr kuma dama duk soja seka sameshi da sanyi akan mace

Zuwa yanzu hakurin shi yasoma karewa dama dagamata kafa yake tunda yakoma ayki besake dawowaba seda yakwashe shekara guda sannan yadawo
Yauma bata gidan kuma tasan zedawo tatafi yawonta tunda yake daita betaba jin bacin rai irinnayauba kuma yasha alwashin yau seyayi maganinta

Yanazaune afalo tadawo kokallo be ishetaba tawuce dakinta. Seda tajima dashiga dakin sannan yamike yabi bayanta yanashiga kamar kullum yauma wayar take da kawayenta
Daga gidan ubanwa kike alameen yawurgamata tambayar
Seda tambayar tafirgitata amma dayake Kai na hayaki setace daga gidan ubanka nake ubana
wani wawan Mari yakifeta Dashi seda tafado daga gadon
Belt din jikinshi yacire yashiga dukanta takoina ran yanmaza yabaci haba ay yayi kokari tsawon shekara biyar yana hakuri
Aisha tun Tana ihu harseda ihunma yagagara seda yatabbatar da tayi laushi dankanshi yakyaleta
Sannan yadakamata tsawa Tana kwance akasa jikinta duk jini sabida tadoku ahannun soja Dan dukan kato yamata
yaci gaba dacewa cikin fushi anfadamiki tsoron ki nakeji ne dazaki dunga yimin abinda kika dama ina kyaleki wallahi Aisha nayi danasanin auranki danasani nabarki kinsake shan fiya fiyar ki mutu wlh daan rage mugun irin
Damutuncina agari amma agidana bandashi to wlh kinyi kadan dama nasamiki idone banza kazamiya kuma wlh kitashi yanzu ki gyaramin gida awa guda nabaki inba hakaba nalahira seyafiki jin dadi yafadi yayin dayayi kwallo da ita yafice daga dakin

Jikinta narawa tamike tafara aykin dukda ciwon dake jikinta besa tabar aykinba tanayi jiri nadibarta Dan yanzu wani mugun tsoronshi takeyi hhhhhh nace su aee anji maza

kafin lokacin yacika tuni gidan yayi clear dattinko data kwashe seda yacika katon dustbin
gidan se kamshi yakeyi komai yayi normal araina nace oh Aisha tazama zuma seda wuta

alameen tunda yafito daga dakinta garden din gidan yashiga seda yatabbatar lokacin daya dibamata yacika sannan yashiga cikin gidan mamakine yakamashi ganin yadda gidan lokaci kadan yasauya sewani kamshi yakeyi dakinshi yaleka komai normal harda sabon bedsheet tashimfidamasa har cikin ranshi yaji dadin ganin gidan ahaka sabida rabonshi daganin sa hakan tunranar daaka kawota gidan

dakinta yanufa yana shiga yaga Tana morping a tsugunne tana kuka tausayintane yakamashi  amma yayi saurin kawar dashi sabida sanadin tausayinne yajefa kanshi acikin halin dayake yanzu
Tsawa yadakamata sannan yace Dan rashin mutunci a tsugunne kike moping din dalla malama tashi
Jikinta se Bari yake tace Dan Allah Yaya kayi hkr bazan sakeba
Mamakine yakama alameen sabida rabonshi dajin irin wannan kalaman abakinta tun sati biyu da auransu

dalla yimin shuru sumumu kasau kawai bacemin dagani Jikunta narawa tadauki ruwan moping din taje toilet tazubar tawanke toilet din fitowa tayi tana rabe rabe inda alameen yakorata taje tayi wanka da gudu tashige bayin Dan tadauka yabiyota abayane
so uku Tana fitowa bayan tayi wankan yana maida ita tasake wani wai bata fitaba hakama brush seda makilin oral b yakusa karewa dan seda bakinta yasoma jini sabida brush sannan yakyaleta kantama adaren tatsefeshi tawanke shi tas haka ma shaving duka seda tayi
ita dakanta taji dadin kanta Dan har wata iskace take ratsata nace oh ji yiwa Kai mugunta

rigar vacci kawai tazira tahaye gado tuni bacci yayi gaba da ita dayake alameen yabar dakin
dawowa yayi yaga Tana bacci duka yakaimata abaya afirgice tafarka tadiro agadon
ubanwa yabaki damar bacci bayan baki sallameniba hkr tashiga bashi Tana hawaye alameen bakunya yakamota yashiga sarrafata bata hanashiba Dan Tana gudun shan duka
yau cikin nishadi yabiya bukatarsa inda besauraramataba se asuba nace Kai alameen batausayi

wanka yayi yafice masallaci Tana kuka tamike tashiga toilet tayi wankan tazo tayi sallah sabida kafin yatafi masallaci seda yamata worning akan ta tabvatar kamin yadawo tahada break fast sannan tayi gyaran gida tayi wanka tayi kwalliya idan yadawo yaga batayi daya acikiba zatasani
shiyasa tamike tafarayi jiri nadaukarta  sabida rashin bacci ga jikinta dake mata ciwo ahaka tadaure tayi komai kamar yadda yabukata har girkinma tayi duk da ba wani dadi yayiba amma yafi babu
dayadawo abun yaburgeshi har wani nishadi yakeji amma idan yatuno tilastata yayi seyaji duk ranshi yabaci



maman Yusuf
[3/18, 11:27] Zahra muhd mahmudπŸ’ƒ: πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€
          *BALLAGAZA*
πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€


Zahra Muhammad mahmud

*pls yanuwa Dan Allah ina barar adduarku yaron Aunty nane jariri bashida Lfy Dan Allah kusashi cikin adduarku a sallahπŸ™πŸ™πŸ™πŸ˜­πŸ˜­πŸ˜­*


*page 8*


Tundaga wannan rana Aisha take tsoron Alameen Dan ko fita bata sakeyiba sosai take jin maganarshi
Bangaren rayuwar aurema ko tanaso ko bataso inde shi yanaso anwuce gurin


Yau alameen ze koma bakin ayki inda yakafamata dokoki yakuma ce muddun ta karya daya takuka da kanta

Har airport Tamushi rakiya kamar gaske
Ay tundaga airport dinnan bata wuce gidaba kaitsaye gidansu Ruky tasauka kamar fadi Tana zama Sega zuly tazo nan suka shiga hirar yaushe gamo daga karshe Aisha tabasu labarin abinda alameen yamata
Dariya suka samata harda hawaye
Zuly tace dankari amma wlh Aisha kinbada mata yanzu tsayawa kikayi yadakeki tabdi ayko inde baki dauki matakiba wlh kinzama filin training dinshi

Ruky taamsa ay yana cewa zedokeki gabansa zaki rike iya karfinki inyaji zemutu wlh zedena ko ki dunga ajiye wuka agefenki dazaran yamiki wani wargi kinuna zaki masa kachiya wlh denawa zeyi amma taya zaki sakarmasa jiki yadunga labta wlh kin rikito

nande sukasata agaba suna huremata kunne basu bartaba seda suka tabbatar shawararsu taamsu agurinta Dan har haushin kanta tadunga ji amma bata baciba tasha alwashin inyadawo zegane kurensa.


      *Photacot*

Alameen ne zaune a office dinshi shida amininshi Usman fira suke gameda rayuwar duniya ananne alameen yashaida mishi labarinshi da Aisha harda dukan dayamata

Major Usman ne yace haba abokina meyakaika dukanta gaskiya baka kyautaba aysu mata insuna iskanci irin wannan akwai dukan daake musu yasasu haukacema gaba daya
dasauri alameen yamatso yace Kai haba abokina
wlh yabashi amsa

to wanne irine shi dukan alameen yabukata

ka kara aure shine mafita

ajiyar zuciya yayi sannan yace major kafi kowa sanin raayin mace daya ne Dani arayuwata so gashi nakuma Aura bandaceba baka tunanin yin wani auran ze Kara daga hankalinane

haba abokina wancan auran dakayi aurene bana soyayyaba maana aurene natausayi so yanzu inzaka sake wani wacce kakeso takesonka zaka Aura wlh inde kadace sekayimin godiyar shawarar Dana baka amma taya zaka tsaya mace tana gasaka bakadauki matakiba aywasu matan zumane seda wuta
dariya sukayi gabadaya suka tafa inda daga karshe alameen yace zeyi nazari akan zancan Usman

haka kwanaki sukai ta tafiya har Allah yadawo da alameen gida koda yazo yaga Aisha tayi fatali da dokokinshi be kulataba
anata bangaren tayi shirin ko ta kwana Amman ga mamakinta setaga ko kallo bata isheshiba
hakan bemata dadiba taso yakulata tace zata masa kaciya  shiko bawan Allah bata ita yakeyiba
.
shurun dayamatane yasa tasake Mike kafa ita adole taci dubu se Ceto kawayenta nakara zugata


     *RUGAR YALLI*


wata rugace ta fulani agarin makarfi ta jahar kaduna  jamaa dayawa basu San rugarba sabida Tana cikin dajine sosai ko yan garin se tsofaffin zamane sukasan da rugar sabida rugar gida ukune kawai acikinta gidan alhaji babba dagidan alhaji jume se gidan ardon rugar wato gidan alhaji yalli

duka gidajen Manyan gidajene sabida kowa dashi da zuriarshi yake zaune agurin

zahrau wacce akafi saninta da surbajo "ya ce agurin alhaji yalli wato ardon garin  Wanda aynihin sunanshi muhammadu Mahmuda asalinsu yangarin gwangolane dayake su fulanin tashine shine suka dawo wannan guri dazama
matanshi biyu sumaye wacce itace uwargida se amina wacce itace Amarya
yaranshi takwas inda sumaye takeda guda bakwai duka Mazda ita Kumar amina takeda guda daya wato zahrau
amina asalinta yar garin kadunace awata anguwa mesuna tudun wada layin kosai anan aka haifeta kaddarar aurece takaita ga auren ardo dakuma rabo danginta Sam basason aurannata dashi kasancewarta marainiya shiyasa tunda taaureshi danginta suka tsameta acikinsu

bayan haihuwar zahraune da shekara  biyar Allah yama amina rasuwa  ardo yayi kuka  kamr ranshi zefita
yanuwantama dasuka sami labarin rasuwarta sunyi kukan rashinta dasuka zo gaisuwa suka bukaci ardo yabasu zahrau sutafi da ita fafur ardo yahanasu yace meze dunga kallo  amatsayin amina idan yabasu ita
ransu besoba amma yafisu iko da ita haka suka tafi suna danasanin watsi da aminan dasukayi

Maman Yusuf

πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€
        *SURBAJO*
πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€


Zahra Muhammad mahmud


*page 9*



Zahrau ta taso cikin tsana da tsangwama  irinna kishiyar Uwa

Sumaye ganamata azaba takeyi tun tana karama aka fara sata zuwa kiwo zuwa yanzu taiya sosai dama ga aladar gidan insun fita kiwo dare yamusu to acan suke kwana ingari yawaye su cigaba da kiwon sede laasar nayi zasu komo gida

Shiyasa inzasu tafi suke tafiya da kanzo Wanda aka daka da gishiri da yaji da man shanu da tukunya sabida koda dare yamusu acan sugirka suci

Kokadan zahrau batajin dadin zaman gidan inde mahaifinta bayanan sabida inyananan bame dukanta sosai yake jida ita kuma gata sunan mahaifiyarshi yasamata shiyasa ake kiranta da surbajo

Yauma kamar kullum surbajo tafita kiwo ita da ya'u yayantane
Suna zuwa rafi suka hadu da arera yar gidan alhaji jume itama tafito kiwon itada yaynta saidu

Suna ganin juna suka rungume juna ita da areran sabida murnar ganin juna guri suka samu suka zauna suna hira

surbajo ayko inada wani albishir dazan miki inji arera

dagaske wanne irin albishir ne wannan kekuwa arera inji surbajo


Aradu dama jae ne dan gidan alhaji Babba jiya yazo gurin yayana zubairu danaganshi muka gaisa shine yace wai ince miki yana gaisheki

ihu surbajo tasa sannan tarungume arera tace

kai madallah aradun Allah naji dadin wannan albishir

Aydama nasan zakiji dadin shiyasa nafadamiki

Ranar agurin kiwo wuni surbajo tayi tanajin dadi Dan harga Allah sakon gaisuwar da jae ya ayko mata ta sanyaya zuciyarta


          *JA'E*

dane agurin alhaji babbah Dan kimanin shekara ashirin
kyakkyawane naajin farko dan duk mazan garin bawanda yakaishi kyau shiyasa kowacce mace take kaunarsa gashida da kyauta dan inde yace yanasonki to ko zakici soyayyar gyada da burodi kimore gashi ranar kasuwa kullin kosanki da yar yau na musammanne
Shiyasa kowacce mace burinta yace yana sonta
to surbajo ma Tana cikin jerin masu sonnasa


yau akwai biki agidan alhaji babba inda yake aurar da yarsa Safiyya yar kimanin shekaru goma shadaya
Su surbajo sune kawayen Amarya sabida suma shekarunsu sha dayanne

ga alada ta Fulani akwai wani wasa dasukeyi bayan shadi inda maza da yanmatane zasu taru suyi layi layin maza dabam haka namatama zasu fuskanci juna suna wakar
Wayyohoro hirobe gadaibe jadu jande wayyo horo hirobe gadaibe jadu jande. Seme kalangu yasa kida to matanne daya bayan daya zasu dunga fitowa su tsaya a tsakiyar filin se tagama kallon samarin Wanda yamata acikinsu shi zataje ta yalo da kafarta yin hakan nanufin  tanason yafito suyi rawa kenan kuma yawanci daga wannan rawarne soyayya take shiga tsakani hartakai ga aure


to wannan bikinma anshirya irin wannan wasan
Danhaka surbajo taruga kowa zuwa gurin sabida tanada gaba  sabida basa son arugasu zaban jae sabida a alada irinta wasan duk Wanda kika zaba fita zakuyi tsakiyar filin kuchase sosai to inkuma yaji yanasonki zece kufita afili kusami guri kuyi mgn


fili yacika bamazanba ba yanmatanba
su kuma mazan kowa burinshi Allah yasa surbajo tazabe shi Dan itama duk yanmatan garin tafi kowa kyau

anfara waka inda surbajo ce farkon fitowa tashigo filin tafara rawar Fulani irin wacce ake daga kafa dayannan ana saukewa sannan takarewa mazan kallo can idonta yasauka akan jae yanamata murmushi ayko batayi kasa agwuiwaba ta yaloshi ihu yayi sannan yashigo filin da kwambe suka fara rawa tare inda me kalangu yadunga wasasu dacewa kyakkyawa se kyakkyawa

bayan sungamane jae yacewa surbajo Sudan fita afilin ay sauran yanmatan naganin sunfita kowacce haushi yakamata inda sukasha alwashin se summa surbajo dukan tsiya akan yaloshin datayi

hakade yanmata da samarin suka ci gaba dawasansu har suka gama

itako surbajo tunda jae yace sukebe farinciki yabi yacikata dantasan yau tafi kowa saa a duniya

koda suka keben juya mishi baya tayi alamun jin kunya

shimade kunyar yakeji Danhaka shima bayan yajuyamata sannan yafara mgn

wato surbajo nadade inashonki amma nakasa fadamiki segashi yau Allah yakawo ranar dazan sanar dake danhaka Do Allah do annabijjo kishe kina shona.nide  aradu ina shonki

kunyace da dadi suka rufeta Dan haka ta ranta anakare takoma gurin arera

gudun datayi shiyabashi tabbacin tanasonshi Danhaka agurin yafara rawar cin nasara Dan yasan yama mazan garin nisa


maman yusuf
[3/18, 11:54] Zahra muhd mahmudπŸ’ƒ: πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€
         *SURBAJO*
πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€


Zahra Muhammad mahmud


*fans muna barar adduarku yaron da bashida Lafiya Allah yamasa rasuwa to kutayamu da addua Allah yajikansa yasa meceton iyayenshine sukuma iyayenshi Allah yabasu hakurin jure rashin sa ,rest in paradise my baby*


*page 10*


Tundaga wannan lokaci syy me karfi tashiga tsakanin surbajo da jae ko kadan basa son rabuwa da juna


Yauma kamar kullum jae yazo hira gurin surbajo

Akan wani ice suka zauna yayinda surbajo tajuyamasa baya sabida kunya
Gyada takawomusu da burodi sunaci suna hirar
Can jae yace surbajo aradu inna aureki nahaye nasan duk garinnan se andunga hirata saboda na auri sarauniyar mata

Dariya tayi tasake rufe fuskarta sannan tace aynima hakanne Dan yanzu haka yanmatan garinnan haushina sukeji Dan rannan munje kiwo nida arera su haulen gidan ku suka tsareni wai sesunmin duka ayko nida arera muka hadu mukaimusu dukan tsiya

dariya yayi sannan yace hauka sukeyi nibance inasonkowa acikinsuba shima Baffa cewa yayi inzabi wacce nakeso inde agarinnanne ze auramin nikuma nazabeki

Dadine yarufe surbajo harseda sautin dariyarta yafito

hakade suka gama hirar wacce yawancinta cin gyadar yafi yawa


****************************


Al ameen yanzu yafita harkar Aisha kwatakwata harkar gabanshi kawai yakeyi yayinda mahaifansa zuwa yanzu sunfara bashi shawarar yakara aure kuma yabasu tabbacin ze Kara yana neman wacce yake sone fatan alkhairi suka masa

alameen anturashi wani course kasar amurka inda seda yakwashe tsawon shekara guda acan yanzu idonshi yakara budewa ya waye fiye da tunaninku ko maganarshi yanzu tasauya Alameen Kenan Dan kimanin shekaru arbain da haihuwa amma babu me ganinshi yayi zaton yakai hakan

Aisha ma yanzu bata da lokacinshi Dan yanzu tazama yar business Dan haka kasuwancinta yafiyemata komai
Mahaifiyarta tanasane da irin tsiyar da Aishan  take tsulawa agidan miji amma kda wasa bata taba tsawatarmataba sabida gudun kar abin arzikin da Aishan take kawomata tadena

Su Ruky suma kullum cikin bata munanan shawara suke inda ahalin yanzu har sata takema alameen din yasan tanamishi satar Amman ko afuska be nunamataba Dan yafuskanci bata da wadataccen hankali


     ***************

surbajo Ankara zama yanmata inda yanzu shekarunta sha biyu da haihuwa Dankaka yanzu sumaye har tallan nono da fura take doramata tabi yanmatan rugar sukai cikin garin makarfin ranar dabata siyarba dukan tsiya take mata shiyasa surbajo bata dawowa gida da wuri matukar tasan bata siyarda nononba

Se tara nadare take baro cikin garin kamin tagama keto dajin ta iso rugarsu goma tayi
haka baffanta zetamata fada itade sede tai tabashi hkr itakuma sumaye na zugashi da cewa maza tafara bi shiyasa take dare bata dawoba itade surbajo sede kuka

wasawasa seda kaiwa dare agurin talla yabi jikin surbajo sabida bata da kan kasuwa Dan wani lokacin setakai laasar baasiya ko na kwaboba gashi nonon yafi Nakowa yawa acikin wainda suke zuwa tallan tare

duk sanda ta dawo se baffanta yazaneta sannan yamata fada akan dolene setayi cinikin inbata siyarba ta dawo mana inya tambayi sumaye ko itace take cewa surbajo karta dawo seta siyar munafukar har kuka take sawa tace haba alhaji yazaayi nacemata haka koban haifeta ba ay yatace kuma nasan hatsarin dake tattare da hakan da irin wannan kalaman take Rufe bakinshi

insuka koma daki ita da surbajo tashaketa takuma ce wlh inkika kuskura kika dawo gidannan baki siyarba yankaki zanyi
itade sede tayi kuka tafadawa Allah

jae yasha yimata juyen nonon yabiya kudin Dan kawai tasamu taje gida dawuri to yau da gobe tafi wasa
ba koyaushene yake da kudin juyenba seyafara rakata tallan sui ta yawo agari har su samu asiye haka sukeyi sunfi karfin wata guda suna zuwa tallan tare kwatsam rannan se sukayi kwantai basu sayar da wuriba ranar basu dawo gidaba se goman dare
lokacin Baffa yafito yabi hanya yagani meyasa bata dawo da wuriba dayake basu San jae narakata tallanba seganinsu yayi tare suna tahowa tsawa yadaka musu yace daga ina kuke cikin darennan
tsugunnawa sukayi sannan sukace daga talla wankesu yayi da Mari duka lokaci daya sannan yace nizaku maidar yaro wato dama abinda innarki take fadamin akan maza kikebi Ashe da gaskene to wlh yau zaki gane kurenki kaikuma zanga baffan nakane wawa kawai kekuma munafuka shige mutafi dagudu tamike tayi gaba Tana kuka koda isarsu gidan yaba sumaye labarin abinda yafaru cewa tayi ay gwanda dakagani da idonka Dan Dana fada baka yardaba aygashinan

ranar seda yama surbajo jinajina inda yakara da fadin  gobema ki kuma kaiwa dare awaje wlh Sena yankaki na huta kuma tallan nono bazaa Dena doramiki ba sabida aladarmuce kowacce yarinya tanayi Danhaka yazama dole kema kiyi daga yanzu in magaruba tamiki awaje ki kuka dakanki

haka taci gaba da Kukanta har zuwa washe gari batayi bacciba

maman Yusuf

πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€
        *SURBAJO*
πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€


Zahra Muhammad mahmud



*page 11-12*


Alameen yadawo hutu inda yasamu labarin anyi rasuwa akano zasu tafi gaisuwa duka family dinsu

Ayko haka suka rankaya gaba dayansu harda matar kabeer da yaransa gabadaya ran alameen ne yabaci ganin batashi matar acikin ayarin

Mota biyu sukayi kabeer ke Jan motar da iyalinshi suke ciki yayinda alameen kejan wacce iyayensa da kannansa suke ciki Dan be tafi da excode dinshiba sabida gaisuwa zasu


Sun isa kano Lfy sunyi gaisuwa an karbesu cikin mutunci da karramawa
  Seda laasar suka kamo hanyar dawowa gida Dan ba kwana zasuyiba

**************

Surbajo yau dawuri ta shirya ta tafi tallan nono Dan Tana gudun tayi dare kuma tasha alwashin yau intaje talla rokon mutane zata dungayi akan su siya

Tayi kwalliyarta cikin kayansu na Fulani inda fuskarta tacikata da digedige duk asunan kwalliya bakinta tacikeshi da bakin kwalli gaba daya  dan Tana tunanin rashin yin Kwalliyar ne yasa baa siyan kayanta

sallama tayiwa sumayen tadauki kwaryar nonon ta wuce


Koda tazo cikin gari jamaa bame bitakanta bare asiya kota rokesu basa siya Dan haka kuka tasa taci gaba da bin mutane akan su siya

haka tadunga bi kwararokwararo akan asiyi nonon mutum Hudu ne kawai suka siya ga nonon da uban yawa

haduwa tayi da Mari yar rugarsuce ita har ta siyar tambayarta tayi Don Allah  Mari ina kike kai nono da furarki asiye Dan Allah kifadamini

Murmushi tamata sannan tace aradu da nisa Dan sekin hau mota naira dari zaa kaiki a  akori kura
Dasauri surbajo tace fadamini Dan Allah  aradun Allah zani
Tashar yarine tabata amsa daganan tajata takaita inda zata hau motar

Godiya sosai surbajo tayi mata tahaye motor akori kuran suka tafi


**************

Alameen tafiya suke suna hira cikin nishadi sabida daddy bayason gudu amota shiyasa ahankali yake tafiya sabanin kabeer Wanda yakusa shiga kaduna Dan cewa yayi baze iya tafiyar wahainiya ba

suna zuwa tashar yari tayansu Yay faci dole Al ameen yay parking agefen titi dede wani masallaci gurin akwai jamaa sosai kamarde kasuwa fitowa yayi Dan yanemi Mesa iska yasamusu suwuce

agefe yaga Mesa iskar Danhaka yace yazo yasamusu dasauri Mesa iskar yasakamusu sabida ganin dankareriyar motor dasuke ciki
1k alameen yabashi mutumin se godiya yake
karaf a kan idon surbajo hakan ta faru Dan haka dasauri takaraso inda alameen keshirin shiga yatada motor dasauri tace sannu bawan Allah  Don Allah kataimakeni dasauri alameen yajuyo jin zazzakar murya namishi mgn

arba yayi da surbajo dauke da kwaryar nono akanta durkusawa tayi tana kuka tace Don Allah  kataimakamin kamar yadda Allah yataimakeka kasiyi nonon nan da fura wlh inna koma dashi bansiyarba yankani zaayi kuma inna Dade agurin tallan Baffa yace seya yankani takara rushewa da kuka

alameen mamakine yakamashi to inbanda haukar fillo shi mezeyi da fura da nono dahar zata ce yasiya motarshi yashige yana shirin tadawa dagudu surbajo tasha gaban motor tana kuka tace cikin kuka haba bawan Allah Allah fa nahadaka dashi kaji tausayinamana Don Allah hankalin daddy ne yakai gurunta mamakine yakamashi Dan haka dakatar da alameen yayi sannan yabude kofar motor yakirata karasowa tayi jikinta har rawa yakeyi
mommy ce tafara mgn dacewa  yanmata Lfy cikin harshen fulatanci kasancewarta mommyn bafulatanace
cikin Yaren fulatancin surbajo tabata amsa dacewa taimako nake nema akan asiyi nono da fura Dan inna koma gida yankani zatayi inbansiyarba inkuma najima agurin tallan Baffa dukana zeyi Don Allah  kutaimakamin

tausayintane yakama mommy
bayani tayiwa daddy game da abinda surbajo tace
tambayarta yayi da Hausa yace yarinya meyasa kika ga muyadace damu taimakeki
share hawaye tayi sannan tace sabida naga kuna da kudi Dan wancam  tanuna alameen da haushi duk yagama cikashi sabida batamusu lkcn datayi
taci gaba naga yabiya kudin sa iska naira dubu guda amaimakon naira talatin shiyasa
dariya sukayi harda sumunauwara

daddy yace to tundaga ina kikazo nan tallan tundaga rugar yalli tabashi amsa

jinjina Kai daddy yayi Dan yasan rugar duk sallah anan ake siyo shanun dayake rabawa mutane kuma agurin shi yallin wato ardon

ke yar wanne gidace a rugar daddy yatambaya
ni yar gidan ardoce
mamakine yakamashi yace nasan shi yanzu ke yarsace

washe baki tayi jin ance ansan baffanta tace eh Amman innata ta rasu

no wonder inji mommy shiyasa ake doramata talla inbata siyarba adoketa

shigo mota inji daddy yayinda yace munauwara dake gaban motor tadawo baya surbajo tashiga gaban

arude alameen yawaigo yace haba daddy time is going fa inakuma zamu da ita
gidansu zamu daddy yabashi amsa

dakyar surbajo tayarda tashiga motar Dan gani take guduwa daita zasuyi seda sukasha fama da ita tayarda tashiga

utone alameen yayi sannan yadauki haryar makarfin daddy kemasa kwatance
dan surbajo tunda tashiga tarungume kwaryar nononta sanyin ac yafara dukanta tafara bacci yin baccinnata seda yabasu daddy dariya ita me gudun asaceta gata Tana bacci

harsukazo makarfi surbajo baccinta take sha

maman Yusuf

πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€
         *SURBAJO*
πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€

Zahra Muhammad mahmud

*Banida Lafiya pls i need your prayers*

*page 13-14*

Daddy ne yace alameen yatashi surbajo Dan takarasa kwatancen gidan

Wani uban duka Al Ameena yakaimata acinya

Hande in bonide itace kalmar da surbajo tafadi da karfi asakamakon zafin dukan dataji

Arude tadago Tana kallonshi sannan tace Kai kado menayimka Kake buguna da zafi haka aradun Allah ka kuma senasa jae yabugemin kai

Dariya gaba daya motar akasa banda alameen Dan yaji haushin maganar

Kwatance surbajo taci gaba damusu har suka iso kofar gidan ardo

Ardo ganin motane yasashi tasowa yaiso gurin ga mamakinsa seyaga surbajo tafito daga gaban motar

Begama mmkb yaga daddy yafito shima Wanda shi alhajin burni yake cemishi

Dasauri yakarasa gurin daddy yana fadin ikon Allah alhaji kaine agidana yau Kai lale lale

Mommy ce tafito itama Tagaida ardo tace nashori yace jam sago

Iso yamusu zuwa cikin gidan sumaye jiki na Bari tafito Tana lalelale kodo jabbama anan jabbeko

Ruwa takawo musu bayan sungaisa tabasu guri

daddy yace haba ardo yanzu mene amfanin dukiyarka dazaka Bari ana dorawa yarka tallah harda samata dokar inbata siyarba se anyankata daganan yakwashe labarin yarda suka hadu da surbajo yafadawa ardo

mamakine yakama ardo jin ashe sumayece kecewa seta siyar zata dawo gida amma munafukar tace ba ita bace tasa yana dukan marainiyar Allah

shima fadawa daddy yayi abinda yasani danshi vashida masaniya akan sumayece take cewa kar tadawo seta siyar

Nande daddy yayta mishi waazi akan yadena bari ana dorawa surbajo tallah kuma yamasa alkawarin bazaa sakeba
da daddy zasu tafi dubu dari yaba ardo sannan yaba surbajo dubu hamsin akan tasiyi kayan sawa ay surbajo dukawa tayi kamar zatayi sujada Dan godiya duk da batasan yawan kudinba ammade tasan masu yawane

sumayema daddy yabata murna kamar tayada zani
Rakosu sukayi bayan ardo yasa daya daga cikin yayanshi me suna sammani yadebowa su daddy kwarya biyu ta Kwai sannan jarka guda ta zuma me kyau
Sumaye ma kwaryar manshanu tabasu duka akasa abooth din motor
Su daddy suka shiga duk abinnan daake alameen betako kafarsa kasaba sabida takaici shi koda excode dinshi bayason tafiyar dare bare yanzu shinema driver  ranshi yagama baci ko ardon daga cikin motar yagaisheshi

sungama shiga yayi ribar's yajuya kan motar  dagudu surbajo tazagayo setin window dayake tace

kado arage mugun hali aradu bacin baffanka yabani kudi dase na kira jae yabugeka tafadi Tana murguda masa baki afusace yaja motar suka wuce ranshi namishi zafi suko su daddy se dariya suke masa babu kamar munauwara gurin tsokanarshi abu kadan tace kado aradu jae seya bugeka shide be tankamusuba

.se Tara nadare suka iso kaduna agidan yakwana yaki zuwa gidanshi Wanda ita Aishan ko ajikinta Dan itama tafiya gidansu tayi takwana acan

kodasafe dayaje gidan bata dawoba se wajen tara sannan tashigo ko ta tambayeshi ina yakwana kawai hidimar gabanta taci gaba dayi

kuyi hakuri dawannan banida lfy ne

Maman Yusuf
πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€
         *SURBAJO*
πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€

Zahra Muhammad mahmud

*page 15-16*

Tundaga wannan rana vaa sake dorawa surbajo tallah ba sede taje kiwo

Ardo Dan Yi yayi kamar ze saki sumaye seda yaranta sukai tabashi hkr sannan yahakura
Sosai sumaye tayi nadamar abinda taaykata tai taba ardon hkr kuma tace bazata sakeba

Abangaren soyayyar surbajo da jae kuwa se abinda yayi gaba Dan yanzu ma intaje kiwo shima yaje to hirarsu suke sha har cikin zukatansu suke son junansu Dan yanzu jae yace zefadama baffanshi aje nemarmasa auran surbajo Wanda hakan bakaramin farinciki yasa surbajo ba danji take tafi kowacce mace saa aduniya araina nace Anya surbajo harda Aisha kuwa

***************

Alameen bejimaba yakoma bakin aykin Dan zamannashi baida amfani tunda matar gidan batasan darajarshiba Dan ahalayenta kaf babu abinda yasauya
Gidanshi kuwa inda kazanta nasawa gini yafadi datuni nashi yajima da faduwa

Aisha ce zaune itada aminanta suna gulmar wata kawarsu anmata kishiya carab Aisha ta amshe zancan dacewa kan ubancan nahango alameen yamin kishiya Wlh dase nakonata kurmus Dan alameen Danni kadai akayishi shiyasa koda wasa betaba attempting Kara aureba Danni kadai naisheshi rayuwa 😜dariya suka samata Dan zancan nata dole Adara su sungama kokarin alameen da har yanzu besaki Aisha ba dansu burinsu yasaketa tadawo gida suzama daya tunda su har yanzu basuda mashinshini amma ita dayake ballagazace bata gane nufinsu akantaba

Haka de taita cika bakin alameen be isa yamata kishiyaba koze mutu inko yayi seta kona matar
aminan nata nazugata dacewa shi yama isa ay baze ma faraba

Babbar sallah ta taho Dan haka ana saura sati daya Al ameen yanufi gida danyin bikini sallah agida

wannan Karon Aisha tayi murna dazuwanshi Dan gaba daya shaawarshi takeji kuma ita bata iya zinaba shiyasa takosa yadawo Dan tasamu karbuwa agurinshi gyara ko ina nagidan tayi har kudi taware takira masu yin penty sukayiwa ciki dawajen Gidan turaruka kalakala haka tadunga sawa gidan duk Dan tafaranta mishi rai ga abinci yakai kala goma Data siyomishi a restaurant duk Dan yaji dadi. Itama wani gurin gyaran gashi taje me suna maman Izzuddeen beauty Saloon sukayimata gyaran kai hardasu eye lashes suka samata dayake Maman Izzuddeen taiya aykinta shiyasa Aisha sosai tayi kyau
Daga Saloon gurin wata Hajiya me gyaran jiki taje wacce ake Kira da Maman Gidado tamata gyaran jiki sannan tamata lalle wayyo fans naso kuna gurin dakunsha kallo araina nace ikon Allah wato Ashe Aishan tasan abinda yadace Amman batayi se yanzu datake dawata manufa tadaban aranta lalle taamsa sunanta ballagaza

Bata dawo gidaba ranar se laasar Tana zuwa wanka tashiga Wanda seda takusan share awa guda a toilet Dan rabonta da wankan takusa sati guda sede tayi ciki tsami tafita Tana fitowa kwalliya akasoma ba batun sallah danko alwala batayoba haka tagama Kwalliyar ta ta cakare a wasu tsinannun English wears masu bayyana surar jikinta
falon kasa tadawo ta harde zamanta ba jimawa taji alamar bude get wani sanyine yaratsata Dan tuni magungunan data shashsha dawanda ta matsa sunfara aykiπŸ™„

dasallamarshi yashigo Dan tundaga kofar gida kanshi yafara kwancewa daganin sabon penty
yanashigowa falo faduwa yakusan Yi sabida arba da Aishan dayayi Tana takowa zuwa gareshi se girgiza kirji takeyi abinda yafi tsolewa alameen ido suman tsaye yayi rungumar da Aishan tamasace tafarko dashi kallonta yakeyi cike da matsanancin mamaki Dan tunda yake da ita bata taba rungumeshi Dan yadawo ba sede shi yarungumeta mamakinshi be karuba seda Yaji muryarta Tana fadin sannu da zuwa Rabin Raina

wani dadine yalullube alameen tabvas yanzu ya yarda Allah yashirya mishi Aishan shi rungumeta yayi shima nanfa suka shiga kissing din juna dakyar alameen yakwace kansa danta Aisha bataki komai ayishi agurinba kan kujera suka nufa suka zauna yayinda Aishan tahaye kan cinyarshi tazauna Tana masa wani malalacin murmushi

sannan tace sannu dazuwa hubby na ya hanya cike da farinciki yace hanya Lfy baby na yana sameki Lafiya tabashi amsa gamida fari πŸ™„da idanuwanta

janshi tayi tarakashi toilet danyayi wanka ga mamakinsa Aisha yau harda tayashi yin wankan

yana fitowa ta tayashi shiryawa sannan tajashi zuwa dinning
alameen murna kamar ta kasheshi ganin kulolin abinci kalakala nande yashiga dibar gara yana samata alvarka bayan yagama alwala yayi zefita masallaci sallar magrib dasauri Aishan Tasha gabanshi tace haa hubby ina zuwa kuma
sallah zanyi Gimbiyata yanzu zandawo kema jeki kiyi sallar yana gama fadin hakan yamata kiss agoshi yazagayeta yawuce
tsaki Aishan taja Wlh Dan karta ja yafasa biyamata bukatane da tamasa rashin mutunci Dan tsabagen rainin wayo yasan abinda take nufi amma shine harda wani tafiya masallaci sallah
dakinta tawuce tazauna Dan sallar cewa tayi tahada da asuba danko azahar batayiba 😳
alameen bedawoba seda yayi sallar ishai sannan yashigo gida
bata falo danhaka dakinta yanufa Yatura kofar yashiga hasbunallahu waniimal wakeel itace tafito abakinsa sabida arba dayayi da Aishan haihuwar uwarta babu kaya ajikinta jikinshi ne yafara Bari dasauri yaje yarungumeta yashiga ayka mata da sakwanni masu wuyar fassara to abinka daya jima beyiba jinshi yake kamar ango ajan gado suka yada Zango sosai suka Raya wannan dare Wanda se asuba alameen yasaurara mata yayi farinciki sosai da canjin dayaji Aishan tayi Danjinta yayi takara test

dasafe yashirya zeje gidansu gaida iyayensa yanemi Aishan datamasa rakiya wata uwar harara ta wurga masa sannan tace
Bainda zani kajimu da mutum shikenan daga Dan sakar maka fuska se raini yanemi yashigo to contract ne kuma yakare bukatar maje hajji sallah Dan haka karka nemi ka takuramin amfaninka nawannan lokacin agurina yawuce sewani jikon tawuce tabarshi agurin
jiri ne yafara daukar alameen dasauri yazauna yadafe kanshi yana karanta adduar datazo bakinsa wato Aisha tayaudareshine da duk abinda tayi Dan yabiyamata bukata badan Allah ba wannan wanne irin balaine
dakyar yasamu zuciyarshi tadena zafi yana zaune agurin tazo tawuceshi tafita yawonta
mikewa yayi jiki bakwari yanufi gidan iyayensa sosai sukayi murna dazuwanshi
daddy ne TaiwanYauwa aminullahi dama Kabir nake jira yazo na aykeshi tunda gaka kazo sekai kaje
cikin ladabi da biyayya yace to daddy ina zanje
rugar yalli inda muka taba zuwa muka Kai wata yarinya gidansu can Zan aykeka kasiyo shanu dazaa rabawa mutane
carab munauwara taamshe daddy cewa zakayi gidansu me kiranshi kado budurwar jae zaka aykeshi gabadaya falon sukasa dariya duka alameen yakaimata ta gudu
kudi daddyn Tamiko Yamiko masa a ledar viva yace gasu miliyan ukune kasiyo yadda yakama murmushi alameen yayi sannan yaajiyewa daddy kudinsa yace ze siyomasa danashi kudin inda sabo daddy sunsaba da kyautatawa daga alameen din albarka sukai tasamasa yamusu sallama yatafi bayan daddy yatambayeshi zegane gidan yace eh zegane  har munauwara nacewa kode tazo tarakashine yamata banza yawuce

da azahar ya iso garin yana faking surbajo nafitowa zata tafi kitso tsayawa tayi Tana kallonshi yayinda shima tsayawar yayi yana kallonta

cike da TaiwanTsiwa tace aradu wannan kadon bayan bakin halin har maita gareka  yoto inba mayeba taya zaka tsaya kana kallona kamar nacimaka bashi nagade kudin daaka bani kyauta aka bani kuma bakai kabaniba baffankane bare kace sukazo ansa sede idan bakin halin nakane zaka gwadamin aradu ko dakasha sanda Danni bani daukar raini tafadi harda murguda baki
alameen dariyace takwacemasa tabbas ya yarda da zancan mutane dasuke cewa yanfulani Nada katobara

surbajo ganin yanamata dariyane yasa takwance dankwalin kanta tasake Damara dashi dama akwai wata damarar daure akugunta karasowa tayi gabanshi tatsaya taruke kugu ita ala dole zatayi maganinsa tunda yake mata dariya  wata dariyarce tasake kamashi yace ikon Allah yau nahadu da gamona inba hakaba taya daga zuwana bancimikiba
ban shamikiba kitareni da balai

surbajo tsayawa tayi Tana kallonshi tunda yafara dariya dimples dinshi suka lotsa hankalinta yakoma kanshi  aranta tace Ashe akwai Wanda yafi jae kyau dama bansaniba hannunta takai dede setin dimples din ta taba dariyar dayakeyine tatsaya sakamakon jin antabashi afusace yajuyo zekaimata duka dagudu takwasa Tana cewa woo nacuceshi nataba ramin nacuceshi nataba ramin harta kule yadena ganota
haba alameen mezeyi inba dariyaba shi tunda yake betaba nishadi irinnayauba yana dariyar ne ardo yafito yasameshi
ganinshine yasa yadena dariyar da faraa yanufeshi suka gaisa ardo yamasa iso zuwa cikin gidan anan alameen yafadamasa abinda yakawosa zagayawa dashi ardo yayi gardengarken shanun yagama zaba yabiyashi kudinsa inda harda ihsani yamasa sannan yabaShi kudin daze dauko motor dazaa zuba shanun akawo musu kaduna  Dan dama inaka siya ardonne yake kaimusu sallama yamasa yatafi bayadda ardo beyi dashiba yatsaya yatafi da nono amma yaki

yafara rakiyatafiya kenan yahadu da surbajo tadawo daga kitson tsayawa yayi Dan yaga tanufoshi soyake tasake bashi dariya Dan duk wani bacin ran da Aishaaisha tasashi dariya da surbajo tabashi dazu yakawar masa dashi
karasowa tayi tace kado zaka tafine kai yadagamata yana murmushi  tace to Dan Allah  kabarni nasake taba ramin fuskarka aradu bazan fadawa kowaba inma bazaka Bari nataba Dan Allah ba togashi kabarni nataba a naira  goma  tafadi tana kwance habar zaninta tadauko naira goman dariya alameen yakeyi danshi Wlh yanzu kallonta yake tamkar katoon
Mika hannu yayi yaamshi kudin sannan yatada motarshi yatafi yabarta dagudu tabi bayan motor Tana cewa kado katsaya kabani kudina gudu take iya karfinta alameen na kallonta ta mirror  yana  dariya dataga bazata iya kamoshibane tace kaci wuta balbal ban bakaba tadauki dutse tawurga ma motar dayake surbajo ta iya jifa seda tasamu motor
Alameen  Allah ne kawai yakaishi gida Lfy Sabida daya tuno surbjo dariya yakeyi lalle ya yarda fillo akwai wowta baabinda kebashi dariya irin nacuceshi nataba ramin wannan Abu nabashi dariya  ahaka har yaiso gida

itako surbajo  Allah yaisa tajata yafi kwando dubu sabida naira gomanta Dan kudin da daddy yabata gona ardo yasiyamata dasu goman data ba alameen ardone kullum yake bata goma takashe toshine tayau alameen yagudu da ita har kuka tayi akan naira goman koda sukaje makarantar dare kasa karatu tayi  sabida gomanta yayinda tasha alwashin duk randa taga kado seya sani

taku har kullum

Maman Yusuf

πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€
        *SURBAJO*
πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€


Zahra Muhammad mahmud



*page 11-12*


Alameen yadawo hutu inda yasamu labarin anyi rasuwa akano zasu tafi gaisuwa duka family dinsu

Ayko haka suka rankaya gaba dayansu harda matar kabeer da yaransa gabadaya ran alameen ne yabaci ganin batashi matar acikin ayarin

Mota biyu sukayi kabeer ke Jan motar da iyalinshi suke ciki yayinda alameen kejan wacce iyayensa da kannansa suke ciki Dan be tafi da excode dinshiba sabida gaisuwa zasu


Sun isa kano Lfy sunyi gaisuwa an karbesu cikin mutunci da karramawa
  Seda laasar suka kamo hanyar dawowa gida Dan ba kwana zasuyiba

**************

Surbajo yau dawuri ta shirya ta tafi tallan nono Dan Tana gudun tayi dare kuma tasha alwashin yau intaje talla rokon mutane zata dungayi akan su siya

Tayi kwalliyarta cikin kayansu na Fulani inda fuskarta tacikata da digedige duk asunan kwalliya bakinta tacikeshi da bakin kwalli gaba daya  dan Tana tunanin rashin yin Kwalliyar ne yasa baa siyan kayanta

sallama tayiwa sumayen tadauki kwaryar nonon ta wuce


Koda tazo cikin gari jamaa bame bitakanta bare asiya kota rokesu basa siya Dan haka kuka tasa taci gaba da bin mutane akan su siya

haka tadunga bi kwararokwararo akan asiyi nonon mutum Hudu ne kawai suka siya ga nonon da uban yawa

haduwa tayi da Mari yar rugarsuce ita har ta siyar tambayarta tayi Don Allah  Mari ina kike kai nono da furarki asiye Dan Allah kifadamini

Murmushi tamata sannan tace aradu da nisa Dan sekin hau mota naira dari zaa kaiki a  akori kura
Dasauri surbajo tace fadamini Dan Allah  aradun Allah zani
Tashar yarine tabata amsa daganan tajata takaita inda zata hau motar

Godiya sosai surbajo tayi mata tahaye motor akori kuran suka tafi


**************

Alameen tafiya suke suna hira cikin nishadi sabida daddy bayason gudu amota shiyasa ahankali yake tafiya sabanin kabeer Wanda yakusa shiga kaduna Dan cewa yayi baze iya tafiyar wahainiya ba

suna zuwa tashar yari tayansu Yay faci dole Al ameen yay parking agefen titi dede wani masallaci gurin akwai jamaa sosai kamarde kasuwa fitowa yayi Dan yanemi Mesa iska yasamusu suwuce

agefe yaga Mesa iskar Danhaka yace yazo yasamusu dasauri Mesa iskar yasakamusu sabida ganin dankareriyar motor dasuke ciki
1k alameen yabashi mutumin se godiya yake
karaf a kan idon surbajo hakan ta faru Dan haka dasauri takaraso inda alameen keshirin shiga yatada motor dasauri tace sannu bawan Allah  Don Allah kataimakeni dasauri alameen yajuyo jin zazzakar murya namishi mgn

arba yayi da surbajo dauke da kwaryar nono akanta durkusawa tayi tana kuka tace Don Allah  kataimakamin kamar yadda Allah yataimakeka kasiyi nonon nan da fura wlh inna koma dashi bansiyarba yankani zaayi kuma inna Dade agurin tallan Baffa yace seya yankani takara rushewa da kuka

alameen mamakine yakamashi to inbanda haukar fillo shi mezeyi da fura da nono dahar zata ce yasiya motarshi yashige yana shirin tadawa dagudu surbajo tasha gaban motor tana kuka tace cikin kuka haba bawan Allah Allah fa nahadaka dashi kaji tausayinamana Don Allah hankalin daddy ne yakai gurunta mamakine yakamashi Dan haka dakatar da alameen yayi sannan yabude kofar motor yakirata karasowa tayi jikinta har rawa yakeyi
mommy ce tafara mgn dacewa  yanmata Lfy cikin harshen fulatanci kasancewarta mommyn bafulatanace
cikin Yaren fulatancin surbajo tabata amsa dacewa taimako nake nema akan asiyi nono da fura Dan inna koma gida yankani zatayi inbansiyarba inkuma najima agurin tallan Baffa dukana zeyi Don Allah  kutaimakamin

tausayintane yakama mommy
bayani tayiwa daddy game da abinda surbajo tace
tambayarta yayi da Hausa yace yarinya meyasa kika ga muyadace damu taimakeki
share hawaye tayi sannan tace sabida naga kuna da kudi Dan wancam  tanuna alameen da haushi duk yagama cikashi sabida batamusu lkcn datayi
taci gaba naga yabiya kudin sa iska naira dubu guda amaimakon naira talatin shiyasa
dariya sukayi harda sumunauwara

daddy yace to tundaga ina kikazo nan tallan tundaga rugar yalli tabashi amsa

jinjina Kai daddy yayi Dan yasan rugar duk sallah anan ake siyo shanun dayake rabawa mutane kuma agurin shi yallin wato ardon

ke yar wanne gidace a rugar daddy yatambaya
ni yar gidan ardoce
mamakine yakamashi yace nasan shi yanzu ke yarsace

washe baki tayi jin ance ansan baffanta tace eh Amman innata ta rasu

no wonder inji mommy shiyasa ake doramata talla inbata siyarba adoketa

shigo mota inji daddy yayinda yace munauwara dake gaban motor tadawo baya surbajo tashiga gaban

arude alameen yawaigo yace haba daddy time is going fa inakuma zamu da ita
gidansu zamu daddy yabashi amsa

dakyar surbajo tayarda tashiga motar Dan gani take guduwa daita zasuyi seda sukasha fama da ita tayarda tashiga

utone alameen yayi sannan yadauki haryar makarfin daddy kemasa kwatance
dan surbajo tunda tashiga tarungume kwaryar nononta sanyin ac yafara dukanta tafara bacci yin baccinnata seda yabasu daddy dariya ita me gudun asaceta gata Tana bacci

harsukazo makarfi surbajo baccinta take sha

maman yusuf
[3/18, 14:08] Zahra muhd mahmudπŸ’ƒ: πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€
        *SURBAJO*
πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€


Zahra Muhammad mahmud


*page 17-18*


Alameen tunda yadawo gida ko Aisha tabata masa rai baya damuwa sabida yanashiga damuwar surbajo take fadomasa arai yayita dariya shikadai
Naira gomanta ko duk inda zashi da ita sabida inya Kalli kudin suna sashi nishadi yanason komawa rugar Dan yaga irin bidirin da zaayi in suka hadu da ita Dan yasan tabbas akwai artabu


Anyi sallah da sati guda alameen yakoma bakin ayki
Sosai wannan Karon yakejin dadin aykinnasa sabida baya tare da damuwa ko kadan Dan daya tuno surbajo yake samun natsuwa

yauma tafe suke a mota shida amininsa Usman tambayarshi yayi yace yadai mutumin naga tunda kadawo daga pass gaba daya kasauwa dariya bata maka wiya kode madamce tasamu twins ne
Murmushi alameen yayi Sannan yace hmm Usman kenan wanne irin twins Aisha zata samu abinda ranar dazan dawo naje mata sallama naga wasu tablet a kan mirror dinta a time din tana toilet nadauka nakaranta naga nahana daukar cikine abun yadauremin kai banmata maganaba sabida nasan kanta ta cuta Danni Wlh aure zan kara kwanannan

Kai haba mutumina Usman yatambaya cike da murna
Wallahi kuwa aure zan kara inji alameen

tokodai soyayyace take saka yawan nishadi
dariya sukayi gabadaya
sannan alameen yaba Usman labarin surbajo Usman harda hawaye Dan dariya
Alameen yaci gaba Usman Wlh bawai sonta nakeba sabida yarinyace gaba dayanta kawai drama dinta nakeso shiyasa nake ganin auranta kawai zanyi tazo gidana amatsayin cartoon inkalla inyi dariya
Kokuma takalleka tayi dariya ba darabon kaine zaka zama cartoon din agurinta inji Usman yafadi yana dariya

Haba Usman nidin yarone dazan tsaya ina shirme kawai nafadamaka for personal use zan ajiyeta


dariya usman yakeyi sosai sannan yace Allah yabada saa amma Wlh zakace nafadamaka kaine zaka koma cartoon din at the end of the day

Dariya alameen yayi yace zanko baka labari ni dannayi dariya kawai Zan auri yarinyarnan Wanda kaima intayi wani shirmen agabanka seka dara


**********

Seda alameen yakwashe wata uku sannan yazo hutu  wannan Karon besamu tarba daga gimbiyarsa ba shima bedamuba sabida badan ita yazo hutunba Dan madam surbajo yazo

Iyayensa sunyi murna dazuwansa dama kuma sungaji da ganin shi a halin dayake sunason subashi shawara agameda rayuwar gidanshi
Bayan yagaishesu mahaifinsa yace yanzu aminullahi haka kazabawa kanka rayuwa da macen dabatasan ciwon kantaba bazaka iya daukar matakiba duk Inda nafita labarinka Akeyi mace tamallakeka ko haka kaga Dan uwanka nayi anasa gidan haba aminullahi kasanifa mace itace mutum amma Kai ga irin wacce kazabowa kanka kayi tunani kagyara rayuwarka
mahaifiyarsama fadan Tamasa dama kuma sunbarshine badan komaiba sedan kar ace suncika sa ido arayuwar yayansu
godiya alameen yayi sosai sannan yashaida musu aure yakeson karawa
sosai sukai farinciki dajin zancan dansuma abinda ke ransu kenan
mahaifinshine yace aina kasamo matar aminullahi
murmushi yayi yana sosa keya yace daddy kumma santafa
faraace takaru afuskokinsu inda daddy yace Kai alhdllh wacece
surbajo yabasu amsa gabadaya sukasamasa dariya
mommy tace ikon Allah tagida ma kana fama ina zaka iya da shirmen surbajo ban hanakaba amma Allah yasanya alkhairi Kai kaji kagani
daddy da tun dazu dariya yake seyanzu yace aminullahi na yar fillo to iyayenta sunsan dazancan
aa yabasu amsa inade so daddy kaje kanemarmin aurannata
badamuwa aminullahi daddy yafadi yana dariya
sallama yamusu yatafi Dan dama yakosa sugama magana yatafi Dan surbajo yakeson gani

yana fitowa yadauki hanyar makarfi shikadai dan bako inane yakeson excode Dinshi subishiba bare irin wannan tafiyar tazuwa yada manufa 😜

da azahar yaiso garin makarfi lokacin surbajo taje yo icce
parking yayi akofar gidan dayake yau larabace mazan gidan suntafi cin kasuwa Dan kasuwar makarfi ranar laraba take ci

surbajo ce tashawo kwana da iccen datayo akanta kamar amafarki taganshi atsaye ajikin motarshi
habawa xubar da iccen tayi ta runtuma da gudu gurinshi Tana zuwa rigarshi takama Tana fadin yauwa wana Kama ay dama nafadi aradu nakamaka sekaji jiki gashiko yau kaida kanka ka kawo kanka har gida tabadi Tana kokarin gyara damararta da hannunta daya daya kuma Tana rike dashi Dan kar yagudu
shiko alameen dariya abun yabashi Dan yasan zaa rina

surbajo dataga yana dariya  naushi ta dirka masa aciki sannan tacigaba da kaimishi duka takoina ba abinda keba alameen dariya seganin itace ke dukan Amman itace ke kuka Tana aradu Seka bani kudina bazan yardaba gashi dukan datakeyi ko zafi babu kamar badukannasa takeyiba
be hanataba seda tagaji Dan kanta sannan takyaleshi Tana haki

sannu alameen yamata yana dariya yace ammafa kinsha ayki

dagowa tayi da jajayen idanuwanta datasha kuka tace jiki kamar karfe dukanka nakeyi amma ninakejin zafi aradu senamaka abinda koda wasa akace ka kuma yimin rashin kunya bazaka kumaba tafadi harda nunashi da hannu shide binta kawai yake da ido yayinda gefe daya kuma yana daukarta awayarshi
shigewa gida tayi Takai iccen sannan tadawo ga mamakinsa tsugunnawa tayi agabanshi tanacewa Dan Allah  kado kayi hakuri kabani kudina aradu nasha kuka sabida kudina daka gudu dashi danhaka seka karamin akan nera gomata kaji kado
murmushi yayi sannan yace naji zanbaki kuma zan karamiki akan nakin tonikuma dukan dakikamin anawa dannima biyana zakiyi inba hakaba inje  inkiramiki sojoji sukamaki
akidime surbajo tamike Tana shirin guduwa jin yaambaci sojoji rukota yayi dasauri yace ina zaki muna magana kuma
cikin barin jiki tace aradu nayafemaka kudin kuma Don Allah karka kiramin wainnan mugayen mutanan niko ganinsu banaso yin sabida nataba ganin yadda sukayiwa wani mutumi dukan tsiya akasuwa suka ciremishi kaya aradu mutumin yabani tausayi Danhaka kayafemin aradu bazan kumaba
ganin ta tsoratane yasa alameen kwantar mata da hankali tahanyar cewa haba surbajo ayko nakirasu bazasu iya yimiki komaiba sabida kyanki
ay surbajo najin haka tahau dariya sannan tace dagaske kakeyi basa Kama mekyau
ehmana dagaske nakeyi
kwace hannunta tayi daga rukon dayamata sannan tace to aradu nafasa yafemaka kudina seka bayani
dariya alameen yayi yace ayko bazan bakiba sabida ke kikace kin yafemin

kallonshi surbajo tayi sannan tace zaka biyanine tun biya nada dadi

sunanan Ardo yadawo dafaraarsa ya tarbi alameen Yayinda yarufe surbajo da fadan meyasa bata kawomasa ruwa da shimfidaba alameen ne yace nine nace tabarshi base takawoba
sannan Ardo yadena fadan
mamakine yarufe surbajo tace a zuciyarta hoddijan aradu kado ko a makaryata shinadabanne kato dashi amma baya kunyar karya

cikin gida ardo yaja alameen  suka zauna suna hira

sato jiki surbajo tayi tafito inda motarshi take tsinke tasa acikin tayoyin tasacemusu iska gabadaya  Tana gamawa ta ruga gidansu arera Tana dariyar mugunta ita atunaninta hakan datayi baze Hana. motor tafiyaba sede  yahanata yin sauri dalilin dayasa tasacemishi iskar kenan


alameen hira tayi dadi Shina Shida Ardo besan magaruba takusaba seda yakalli agogon hannunshi mikewa yayi domin tafiya ardo nata samishi albarka kyauta yayiwa ardo metsoka sannan yafito daga gidan  tsayawa yayi yana waigen ta ina ze hango cartoon dinsa tazo suyi sallama amma be hangotaba ardo yace aykawai kayi tafiyarka inde surbajoce takai takwas nadare bata dawoba tanacan suna wasa da saointa
bahaka alameen yasoba Amman bashida zabin  dayawuce yatafi sabida  dare yafara Yi ga hadari yahadu sosai
shiga motarsa yayi batare daya Lura da barnar da surbajo tamasaba seda yakunna motar security dake jikin motar yafara kara alamun akwai Matsala amotar fitowa yayi danganin meyasami motar
innalillahi wainna ilaihi rajuun ita kawai yake maimaitawa ganin tayoyin motarshi a sace kobaa fada masaba yasan aykin surbajone dafe kanshi kawai yayi yana kallon motar yama rasa abinyi dama daya tasace dase yadauko spare din tayar dake boot yasa to duka hudunne gashi garin ko mashin babu me ita bare asamu Mesa iska wayarsa yadauko babu network sam
kamin yagama yanke abinyi ruwan sama yafara sakkowa
ardone yakaraso kusa dashi yace Aminu akwai matsalane
kai yadagamasa sannan yamasa bayanin abinda yafaru da motar amma befada masa surbajo ce tamasa ba Dan yasan tsaf ze iya Zaneta

suna nan tsaye ruwan yakarasa tsugewa kamar da bakin kwarya dasauri ardo yajashi zuwa wata bukka wacce dama anyitane sabida baki
zama yayi akan gadon karan dake ajiye adakin ardone yajawo kofar bukkar yakare wacce take ajiye agefe itama takarace
sunanan zaune ruwan betsayaba se misalin bakwai da Rabi nadare
ruwan alwala ardo yaje yakawomasa yayi alwala yay sallah sannan ardo yakawomasa barguna guda biyu da fitilar aci balbal yace gashi yashimfida daya yarufa da daya yayi hkr yakwana anan inyaso gobe da safe ardon zeje cikin gari yakira mesa iskar yasamasa
alameen bakinciki yagama rufeshi bakomai yake bashi haushiba se irin yadda ze kwana Abukka batare da wani tsaroba ko kofar arziki babu ga sanyi daaka fara kamar jaura tawuce shiyama zeyine gurin bacci akan gadon kara amma ya yaiya bashida zabin daya wuce hakan
komawa motarshi yayi yadauko bindigarshi  da touch light Wanda yaajiye amotar sabida tsaro

surbajo se takwas tanufo gida itadasu arera dasuka rakota tabayan gida tashigo gidan Dan haka batasan alameen betafiba alwala tayi sallah sannan tafara tunanin oh kado koyaje gida yanzu oho sumayece takirata tace tazo takaiwa
bako abinci yana dakin baki  mamakine yakamata nayaushe sukayi bakon daukar abinci tayi tuwan dawane da miyar kuka danya yasha manshanu Wanda aka zuba a akushi na musamman tanufi bukkar bakin dayake motor alameen bakace kuma akasan bishiyar mangwaro yayi parking dinta surbajo bata Lura da itaba sallama tayi kofar bukkar daga ciki aka amsa shiga tayi taajiye kwanon abincin tajuya zata fito fisgota yayi da karfi tafada jikinshi zata samasa ihu yarufe bakin da hannunshi haska Mata fuskarshi yayi sannan yasakarmata baki arude tace kado meya hanaka tafiya gida  kallonta yayi sannan yace haba surbajo  meyasa Zaki sacemin iskar tayakinsan motar kuma bazata tafiba inba iska  tausayinsane yakamata hawayene suka fara zubowa daga idonta cikin kuka tace Dan Allah kado kayi hkr  aradu bansan motor bazata tafiba nadauka saurine bazatayiba Dan Allah  kayafemin  nasa Zaka kwana a inda baka saba
tausayinta alameen yaji amma hakan baze hanashi hukuntata ba danyayi alkawarin yimata hukunci bindigarsa yazaro ya saitata kan surbajo


Maman Yusuf
[3/18, 14:09] Zahra muhd mahmudπŸ’ƒ: πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€
         *SURBAJO*
πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€


Zahra Muhammad mahmud


*ina barar adduarku gobe in Allah yakaimu zanyi tafiya so atayani da addua inje Lafiya in dawo Lfy Wanda nataba batawa rai pls agafarceni nima nayafema kowa ngd*


*page 19-20*


Surbajo idanuwantane suka fito kurukuru ganin bindigar datayi jikinta sebari yake

Alameen yace umarni zanbaki inkika kuskura kika ki bi sena harbeki yafada in a serious talk

Girgizamasa kai yakeyi alamar tayarda

Cigaba yayi da magana yace  surbajo yau kinbatamin raina sosai so dole ne nahukuntaki Dede da iri laifin dakikamin

Don Allah kado kayi hakuri aradu bazansakeba

Tsawa yadakamata wacce ta tilastata yin shuru jikinta nabari
Kara matso da bindigar alameen yayi dede goshinta aytuni fitsarin datake rikewa ya kubce alameen seji yayi yajike da fitsari bedamuba yacigaba da cewa

umarnina shine zan aureki ko kinaso kobakyaso     kuma idan kika sake kika nuna cewa nina tilasta miki aurena harbeki zanyi

surbajo wacce tunda yafara magana   numfashinta ke barazanar daukewa dakyar tace Don Allah kado kayi hkr inada Wanda nakeso kumashi zan aura

Bigemata baki yayi yace ay ba raayinki nakeson  jiba umarni nabaki kuma dole kibi inkinki ko dagake har Jaen sena harbeku

Jikintane yakama Bari kamar mejin sanyi tace kayi hkr Don Allah karka kashemini jae aradu naamince zan aureka

Wani malalacin murmushi alameen yasaki alamun samun nasara cikin ruwan sanyi

alameen bekyale surbajo tatafiba seda yagama tsoratata sannan yace tawuce

da gudu tafito tayi cikin gida kamin takai cikin gidan tafadi yafi so uku sabida agigice take  koda tashigo Kowa yashige dakinsa  sabida sanyin daakeyi itama nata dakin tashige wutar jin dumi ta tarar sumaye takaimata dakin ga kuma abincinta a akushi
 Gaban wutar taje tazauna bayan ta karo kofar dakin

kuka tashigayi Mara sauti duk da tabon daya bata mata kaya bata damu taciresuba
ita kawai tunaninta alameen Dan fashine Dan inba Dan fashiba baabinda zekawo bindiga gurinsa itayau yazatayi da rayuwarta Ashe Dama basuda rabon aure da jae gaskiya kado mugune Allah seya sakamana  tafadi Tana cigaba dakukanta
Wanda babu mesharemata

ranar azaune surbajo takwana kowanne motsi akunnanta Dan tsoro takeji takwanta kado yazo ya harbeta

Shima alameen Tana fita ruwa yadiba yasa ajikinsa inda fitsarinta yashafa sannan yaci abinci data kawomasa  gaskiya yaji dadin abincin ruwa yasha sannan yakwanta badan yayi bacciba seda yaji dadin tuno dramarsa da surbajo juyi kawai yake yana murmushin jindadin gano surbajo nada tsoro dayayi
ayko yasamu abinyi shima ranar beyi bacciba

da sassafe ardo yaje cikin gari nemo mesa iska yaci wuya kamin yasamu Wanda yaamice zebiyoshi zuwa rugarsu

suna zuwa yasa iskar alameen Wanda tuni yashirya yabiya mutumin kudinsa sannan yakarasa gurin ardo domin suyi sallama sosai ardo yadunga kara bashi hkr abisa tsautsayin dayafaru  sallama yamasa yanufi gurin motarshi kamar anjefota yahango surbajo tafito daga gidan dauke da tulu Zata dibar ruwa tsayawa yayi harta karaso
ko kallonshi batayiba Tana kokarin wuceshi Dan ita yanzu tsoronshi takeji
kiran sunanta yayi arude tajuyo Dan tunda take babu Wanda yataba kiranta da sunanta taji dadin sunan kamarshi
tsayawa tayi ainda take
ba gaisuwa yatambaya

kayi hkr ina kwana murmushi yayi sannan yaamsa da Lfy
yakara da ina Zaki ruwa zan debo tabashi  amsa
muje inrage miki hanya yafadi sannan yajuya yashige motarshi bude mata gaban motar yayi tsayawa tayi kamar da karta shiga sekuma ta tuno bindinga dagudu taje tashige yarufe kofar yatada motor suka tafi


afuwan
akwai tafiya agabana maassalam

maman yusuf
[3/18, 14:11] Zahra muhd mahmudπŸ’ƒ: πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€
         *SURBAJO*
πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€


Zahra Muhammad mahmud


*page 21-22*


Tafe suke yana janta da hira har suka iso bakin rafin yana parking Ta bude motar tafice
Tanufi rafin ko sallama bata masa ba

Murmushi yayi sannan yace halin surbajo se ita shima bedamu ba yaja motarshi yawuce yana fita agarin wayarshi tafara ringing abokinshine Usman bayan sungaisa yace yanemi wayar alameen  din besamuba ko Lfy

Dariya yayi sannan yabashi labarin abinda yafaru tsakaninshi da surbajo  dariya shima Usman din yayi yace shege mutumina wlh dukanku kunburgeni kunyi dede Allah de yanuna mana ranar bikinnan
Hakade suka Dan jima suna hira daga baya sukayi sallama


Alameen gidansu yasauka yaci abinci anan abba yake shaidamishi sati mezuwa zasuje nemarmasa auran surbajo
.sosai alameen yanuna jin dadinsa   dajin zancan godiya yamusu sosai sannan yanufi gidanshi fuskarsa dauke da faraa

Koda isarsa Kai tsaye cikin gidan yanufa bayan yagama gaisawa da masu tsaron Lafiyarsa


Yana shiga falon Aisha ta taso afusace ta kama kwalar rigarsa tarike sannan tace daga ina Kake kuma agurin wacce shegiyar ka kwana batare daka sanar daniba tafadi cike da rashin kunya
ran alameen tuni yafara zafi jin takira surbajo da shegiya

Dagowa yayi yace sakeni inwuce Aisha banason rigima yanzu

shewa tayi sannan tace ay Wlh inkaga nasakeka kafadamin gurin wacce ka kwana ko anfadamaka bansan taketakenka ba ay Tunda kafara zama bunsuru nagane to Wlh baka isaba bade agidannanba

Tass yadauketa da Mari kamin tawatsake yasake Kai mata wani  daga bisani yarufeta da duka ihu take Tana neman agaji   seda yamata dukan dashi kanshi besan iya adadinsaba sannan yakyaleta tuni tajima da sumewa
Ko ajikinshi ya dauko ruwa yasheka mata  tafarko
sannan yabata amsa dacewa
Aisha Tunda nake bantaba ganin jaka kamarkiba   dakikiya kawai mahaukaciya
Wai kindauka tsaron ki nakeji to Wlh ko daya tausayinki nakeji amma Tunda kin nunamin kedin dabba ce Wlh sena baki mamaki kuma dakikace daga ina nake daga gidan matar dazan Aura nake kisama ranki Wlh aure zanyi nanda sati guda kuma it doesn't matter to me kome nene ze faru yafaru banza tinkiya kawai ko kigyara halinki ko kada ki gyara damuwarkine ko tablet nahana haihuwa dakike sha keze cutar baniba Danni wuyarta nayi auran
ya ingijeta tafadi akan tiles sannan yawuce yabarta da faasshen jiki se kuka takeyi


********

Surbajo Tunda alameen yatafi kullum da tunaninsa take kwana take tashi sosai take kewarsa sakamakon so da kaunarsa dasuka addabi zuciyarta tabbas yanzu tana sonshi dari bisa dari zuwa yanzu sunfara samun sabani da jae ganin yanzu batashi takeyiba shiyasa yaja baya shima da ita duk da yanasonta amma baze jure tadunga shareshiba

su daddy sunje nemama alameen auranta inda ardo yay matukar murna da afkuwar hakan badan komaiba sedamutuncin iyayensa
kamar yadda alammeen yafadawa mahaifinsa daga baya cewa shima bayason bikin yawuce sati guda tokoda suka sanar da ardo bemusamusuba aka tsaida ranar auran sati mezuwa bayan an tambayi surbajo shin kotana sonshi ta amsa da eh tanasonshi


Ayimin afuwa nayi tafiyane

maman yusuf
[3/18, 14:12] Zahra muhd mahmudπŸ’ƒ: πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€
         *SURBAJO*
πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€


Zahra Muhammad mahmud


*page 23-24*


Acikin satin aka soma shirye shiryen biki dan ranar asabar zaa daura auren

Aisha Data fuskanci dagaske aure alameen zeyi hankalinta vakaramin tashi yayiba Dan haka tanufi kawayenta subata shawara  

Koda isarta gidansu zuly kuka tasa mata tace kawata nashiga uku alameen aure zeyi Dan Allah kitaimakeni narasa abinyi

Wani dadine yarufe zuly Dan Dama sun jima suna jiran wannan ranar Amman  afili kukan tasa itama suka rungume juna dakyar sukayi shuru zuly tace wannan tashin hankali dame yay Kama wallahi bazamu zuba ido muna kalloba semun dauki mataki ki kwantar da hankalinki
Gobe in Allah  ya kaimu zamuje gidan wani malaminmu yaiya ayki sosai zeshare miki hawayenki sosai Aisha tayi murna da shawarar aminiyartata Dan bata bar gidanba se dare


Alameen murna yake sosai Badan komaiba sedan auren cartoon dinshi dazeyi
Usman dariya kawai yakeyi dazaran yaji alameen yakira surbajo da cartoon Dan yana da tabbacin alameen dinne zekoma cartoon din

Shiri suke sosai musamman gidansu alameen Dan sunfi kowa murna da auren da alameen zeyi
Dubai mommy taje tahadowa surbajo kayan lefe da kayan daki sabida sunce ardo base yayiwa surbajo kayan dakiba su zasuyi

Dakuna biyu dake falon kasa nagidan alameen aka shiryawa surbajo kayanta  aka kulle dakin yayinda kayan lefenta aka ajiye gidan su alameen sabida ardo yace a ajiyemata acan



**********

jae dayasamu labarin surbajo aure zatayi har gida yaje yasameta koda tazo
jae rufe idonsa yayi ya zazzagamata masifa har yana cewa auran kwadayi zatayi kuma insha allahu se an sakota kuka surbajo tasa Tana rokonsa ya yafemata Dan tasan bata kyauta mishiba amma bata da iko da zuciyarta  takamu da son alameen me tsanani Wanda tanajin bazata iya rabuwa dashiba kuma ita badan kudinsa takesonsaba sedan Allah
Jae shima kukan yakeyi Dan kukan surbajo yadagamasa hankali cikin kuka yace ya yafemata Allah kuma yabasu zaman Lafiya da mijinta daganan yawuce yatafi yabarta Tana Ta kuka


alameen shida Usman suka dauko hanyar makarfi Dan sunason ganawa da Amarya suji shirye shiryenta

da isarsu ardo yasaukesu a dakin saukar baki yasa aka kawo musu fura da nono me kyau sosai Usman yasha furar sabanin alameen dashi ba cimarshi bace

seda suka Dan jima dazuwa sannan aka turo surbajo wacce ta yafo mayafi tarufe fuskarta sabida jin kunya sallama tayi tashigo dakin tasami guri tazauna daga nesa dasu dakyar ta iya gaishesu suka amsa cike da barkwanci

Usman yace amaryarmu kunyarmu kuma kike Yi haka
Ko fuskar bazaki budeba
Ay surbajo jitayi wata kunyar tasake kamata Dan haka Kara Rufe idonta tayi Tana murmushi daga cikin mayafinnata
hakade Usman yay tajanta da hira amma takasa bashi amsa sabida kunya
mikewa Usman yayi yafice daga dakin Dan yabasu guri su tattauna

shuru ne yabiyo bayan fitar Usman
jin shurun yayi yawa ne yasa surbajo zaton sun fitane daga dakin ne dukansu yaye rufar datayi tayi carab idonta yasauka akan na alameen da tun tuni ita yake kallo dasauri tamaida rufar
matsowa alameen yayi gab da ita har jikinsu na gogar juna lullubin ya bude surbajo kankame hannunta tayi a kirjinta sabida batason yakalleta murmushi yayi Dan yafahimci me take boyewa hannuwanta yakamo yaruke anasa sannan yabita da ido yana karewa halittarta kallo ba laifi duk da kankantar shekarun surbajo hakan be hanata mallakar duk wani Abu da yamace ke daukar hankalin da namiji dashiba

surbajo duk Ta takura da irin kallon da alameen yake mata kokarin kwace hannunta takeyi amma takasa cikin siririyar muryarta tace kado Don Allah kasakarmin hannuna Wlh kunyarka nakeji tafadi Tana runtse idonta
akasalance alameen yafara magana sabida kallon kirjin surbajo dayayi yahaifar masa da damuwa sabida surbajo batasa bresiar ba hasalima bata da ita garigar jikinta me budadden wuyane irin na Fulani shiya Kara bayyanar da halittar dukiyar fulaninta ganin hakanne yasa hankalinsa yasoma tashi

dakyar yace surbajo kunyata kuma yanzu kikeji ko kinmanta saura kwana biyu yarage kizamo mallakina  Toni banason kunyar nan taki kinji ko kai tadaga masa
yaci gaba ko bakyasona ne
dasauri tace kado aradu ina sonka kawai inajin kunyarkane kunnenta yaja da Dan karfi Wanda hakanne yasa ta samishi kukan shagwaba Dan dama surbajo gwanace gurin kukan banza bare yanzu dame dalili yasamu

alameen yace daga yau nasauke sunan kado inkika kuma kirana dashi kuma zanyi Maganin bakin daya kirani da sunan kadon

cikin kuka surbajo tace aradu kado bazan Kuma........bata karasa fadin abinda zata fadaba yahada bakinshi da nata yashiga kissing kamar yasamu sweet
hankalin surbajo kusan barin jikinta yayi asakamako fadawa duniyar dabata taba sanin akwaitaba arayuwarta
seda yajita jikinta yagama mutuwa sannan yakyaleta surbajo dasauri ta janyo mayafinta tarufe jikinta har fuskarta jikinta se rawa yakeyi ita bata san sunan abinda yamataba jikinta duk yamutu
ga wata matsananciar kunyarshi data kamata shima daurewa kawai yayi amma Allah kadai yasan yanayin dayakejin kansa

hira yay tajanta da ita amma bata bashi amsa hakanne yasa yamike yace tosu zasu tafi dubu dari yabata akan kozatayi amfani dasu  dakyar taamsa sannan tayomasa rakiya inda Usman yake jiranshi ajikin motarshi dakyar surbajo tayima UsmUsman sallama sannan tacewa alameen kado kugaida Gid.......bata karasaba tasa hannunta tarufe bakinta sannan  takwasa da gudu tayi cikin gida
dariya alameen yayi Dan yasan me yasa surbajo guduwa
mota suka shige bayan sunyiwa ardo sallama suka dauki hanyar kaduna
Usman se tsokanarshi yakeyi


Maman Yusuf
[3/18, 14:13] Zahra muhd mahmudπŸ’ƒ: πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€
        *SURBAJO*
πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€


Zahra Muhammad mahmud


*page 25-26*


Abangaren uwargida Aisha kuwa jitake kamar takashe kanta dan bakinciki sabida koda sukaje gurin bokan su Zuly cemusu yayi kawai suyi hkr Dan aure ba fashi se anyishi shiyasa gabadaya tarasa natsuwarta ga alameen yanzu yayi wuyar gani sabida shirye shiryen bikin

Ganin tadamune yasa su Ruky kwantar mata da hankali dacewa tabari akawo Amaryar bayan kwana biyu sumata dukan tsiya hakanne yasa Zuciyart yin Sanyi danko kayan fadan kishiya daaka bata batabi takansuba kawayentane suka dau na dauka itama suka zabarmata Wanda zata sa in amfara bikin


**********

Surbajo Tunda alameen yatafi yabarta kullum cikin tuno abinda yamata takeyi itade batasan sunan abunba amma in tatuno abun namata dadi har addua take Allah yasa yakara yimata πŸ˜€

Ardo sosai yake shiri shima Dan tun ana sauran sati guda bikin kullum se an kwantar da sa anyanka dangin maman surbajo suma baa barsu abayaba sunzo bikin kwansu da kwarkwatarsu suma sunyma surbajo shatara ta arziki

         *RANAR BIKI*

ranar asabar 31-12-2011 dubban jamaa suka shaida daurin auran Zahra Muhammad mahmud (wato surbajo)tare da angonta alameen jibrin sulaiman daurin auran dayasami halattar manyan shuwagabanni da yankasuwa uwauba sojoji manyansu da kanana
Ko ina kakai dubanka alummane tako ina  ranar garin  makarfi bamasaka tsinke sabida yawan alumma ga jiniya takoina natashi kowa mamaki yakeyi me alameen zeyi da surbajo yar kauye kamar haka hakade akagama taron daurin auren jamaa suka fara watsewa

Dayake tare zaa wuce da Amarya tuni motocin daukar Amarya sunfara dibar jamaa
Inda yawancinsu mutanen kaduna ne sabida ardo yace yana gudun kauyancin yan rigarsa shiyasa masu natsuwar kawai aka dauka
Amarya survajo wacce ke nade cikin wata lafaya Medan karan Kyau da tsada se kuka takeyi sabida rabuwa da gida dazatayi ammafa tayi kyau sabida wata yarinyar yayan mamanta me suna Bilkisu dasuka zo daga kaduna itace tayima surbajo Kwalliyar duk da ita surbajon bataso Amman seda akayimata kuma tayi kyau farinta yafito sosai
Sumaye tajima Tana yiwa surbajo fada akan zama da miji haka yan uwan mamantama sunmata fadan sabanin ardo da kukan da surbajo takeyi yakeson sashi kuka dakyar yaiya cemata surbajo aure ibadane kiji tsoron Allah.... Hawayen dayake tarewane suka kubce dsauri yabar dakin dabaze iya jure ganin kukan surbajoba

dakyar aka ja surbajo zuwa gurin motor dazata dauketa wacce ango alameen yake ciki yana jiranta yayinda Usman ke zaune agaban motar shida driver abaya alameen ke zaune se motoci guda hudu biyu gaba biyu baya sunsa motor atsakiya  excode dinshine

bayan motor aka budema surbajo tashiga  dakyar Tana shiga takifa kanta akan cinyarta tacigaba da kukanta bata lura da alameen dake gefentaba

tuni motocin suka fara tafiya   ana jiniya Usman dake gaban motar ne yajuyo yana fadin
haba amaryarmu aymana afuwa haka munyi laifi Amman aymana afuwa

alameen ne yaamshi zancan dacewa sede inkaine kayi laifin Amman baniba wayace taamsa tanason auran kagako tunda taamsa dole tadau naannabawa tunda taga Dan fari me dimples tamakalemishi ita wai me wayo tacuceni ta taba raminko ay ga makomar cutarnan yakarasa zancan yana dariya

dasaurin surbajo tadago kanta Tana kallonshi Dan bata dauka yana motarba ido suka hada danshima ita yake kallo dasauri tayi kasa da idonta Dan bazata iya jure irin kallon dayake mataba

hannunta yakamo yana kallon zanen lallen dake Zane akan hannun lallen yayi kyau sosai wasa da hannun yashiga Yi tasigar daduk macen daakayiwa setaji dadin hakan

jawota yayi jikinshi yarungume yafara yimata magana akunne
yace
baby waya miki wannan lallen
dakyar tabashi amsa da Bilkisu ce tayimata
wannan Kwalliyar fa yatambaya duk itace tayimin tabashi amsa
kinyi kyau sosai yafadi yana hada bakinshi danata seda yafara kissing seda yaga yana shirin fita daga hayyacinsa sannan yasaketa
surbajo wacce bataso yadenaba kwanciya tayi ajikinshi Tunda yasaketa  rungumeta yayi yana shakar kamshin jikinta tuni bacci yadauki surbajo gyara Mata kwanciya yayi ajikinsa tayadda bazata wahalaba kamin sukai gida
dago idonsa yayi carab suka hada ido da Usman ta mirror  yanamasa dariya dan duk abinda yafaru tsakaninsu akan idonsa akayi
kunyace takama alameen Amman se ya maze yace to munafiki saidonnaka wato har akan mata da mijiko to thanks God  matatace ay yafadi yana hada rai dariyace takwacewa Usman yace ikon Allah inbanda tsarguwa nimekaji nace
aynasan zakacene shiyasa natari numfashinka inji alameen
dariya Usman yasake yi  yace rufamin asiri da kallon mata da miji ni kawai cartoon din Tom and Jerry nake kallo

duk yadda alameen yaso daurewa kar yayi dariya Amman yakasa duka yakaiwa Usman yana dariya yace saido de bakyau
harsuka iso gida Usman na tsokanar alameen Wanda kunya tahanashi ramawa


itako surbajo har suka iso gidan iyayen alameen bacci takeyi hankalinta kwance



maman Yusuf
[3/18, 14:14] Zahra muhd mahmudπŸ’ƒ: πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€
         *SURBAJO*
πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€

*slm masoya littafin ballagaza to nayi gyara yanzu sunan littafin yatashi daga ballagaza yakoma surbajo duba da akwai littafi mesunan ballagazan inafatan zaku anshi sabon sunan littafin da hannu biyu*


*page 27-28*


Koda akayi parking aharabar gidan surbajo bata tashi daga baccinba ganin bata tashin bane yasa alameen gyara zamansa a motar Dan cewa Usman yayi da direban su sauka amotar danshide baze fitaba se surbajo ta tashi a bacci sauka sukayi suka barshi Usman yace ah lalle wannan cartoon yana kyau  tonide badaniba nashiga ciki inta tashin inajiranka yafadi yanamasa dariya  

Mommy dasauran dangi masu jiran karasowar Amarya jin ance motar amaryar takarasone yasasu fita domin taryota

Sede ga mamakinsu sojoji ne kewaye da motar rike da bindigu cikin shirin kota kwana abun yabasu mamaki

Tsayawa sukayi suna jiran abude motar
tsawon minti goma baa budeba yasa Momy tambayar daya daga cikin sojojin

Kai wai amaren basu isobane ko bawannan bace motar amaryar
Cike da girmamawa yace madam Amarya taiso amma  oga shima yana cikin motar bande san abinda yahanasu fitowaba sede ko zakije ki gani

Murmushi Momy tayi sannan aranta tace dakyau aminullahi wato mu zenunawa yayi Amarya ko zeci uwashi ne dawannan shegen rawar kan

munauwara takira tace taje gurin motar tace injita tace aminullahi yafito da Amaryar haka kota sabamasa

dagudu munauwara tanufi motar abinnema yasamu Dan ita akwai son Amata irin wannan ayken

nurking glass din motar tayi seda tadan jima tana nurking din sannan yasauke glass din motar ganin munauwarace
Yana saukewa idonta yasauka kan surbajo dake ta faman bacci kwance ajikinshi
Dariya tayi sannan tace Bross kana hutawafa to mommy tace Wlh ranka ze baci inbaka fito da amaryaba tafadi Tana dariya takara dacewa su Bross ko kunya juyawa tayi da gudu zata bar gurin dasauri yarukota yace zaki sani wato ninema mara kunyan ko kwacewa tayi taruga gurin mommy Tana dariya
tace mommy Wlh amaryar ma bacci takeyi maybe shine abinda yahanashi fitowa daga motar

bata  rufe bakiba taga daya daga cikin sojojin yanufi motar yabude kofar
Alameen ne yafito sannan yamika hannu yadauko surbajo dake bacci

Yanufi su mommy nanfa abokanan wasa suka shiga tsokanarshi masu dauka awaya suna dauka Dan abun koni yaburgeni

jin hayaniya da surbajo tayine yasata   farkawa ganin abinda kefaruwane yasata Fara kiciniyar kwace kanta Dan gaskiya kunyace takamata sosai
Ganin tanason   saukane yasa alameen sauketa
Lafayar dake jikinta takara ja tarufe fuskarta jikinta se rawa yake sabida kunya mommy ce takarasa ta rungumota tana fadin barka da zuwa cikin zuriata Allah  yasadamu da alkhairin dake tattare dake yakawar da sharrin
Ameen sauran jamaar suka amsa daganan aka shige da ita cikin gidan falon daddy aka kaita alameen ma yabi bayansu
nasiha sosai daddy yamusu inda akarshe yagargadi alameen akan yarike amanar yar mutane kuma yayi adalci atsakaninsu
daganan akawuce da surbajo part din mommy domin shiryata zuwa gurin dinner  shima part dinshi na gidan yanufa
Usman yatarar da wasu abokansa su biyu suna hira dashigarshi suka juyo kanshi suna tsokanarshi babu kamarma Usman harda cewa shi ko alabari betaba jin ango Mara kunya kamar alameenba
dariya alameen yayi sannan yace
Kai alhdllh nagodewa Allah dayasa nazama nafarko atarihi

duka suka kaimasa dukansu suna dariya
daganan suka shiga shirin zuwa gurin dinner wacce zaayi a bafra international hotel dake no11b yakubu avenue off alkali road unguwar rimi kaduna
Sosai suke shiri inda Amarya mommy tadauko me kwalliya tashiga yimata sosai tayi kyau wedding gown akasamata light blue gaskiya bame kallonta yayi zaton wai shekarunta sha hudune sabida surbajo akwai Kira kuma bame zaton tasan hanyar wani abu waishi kauye bare aje ga ruga ita kanta data Kalli kanta a mirror tantama tashigayi akan anya itace kuwa

alameen ma shadda yasa light blue shima yayi kyau sosai yayinda sauran abokansa suka sa farar shadda

kawayen munauwara sune suka zama yanmatan Amarya dangama surbajo baazo da kawarta kodayaba
suma yanmatan Amarya fararan dogayen riguna sukasa yayinda Suka daura head ja takalmi ja
gaskiya sunyi kyau

takwas nadare motoci suka fara dibar mutane zuwa gurin taron

yayinda uwargida Aisha ma tagama shiryawa cikin wani yellow din material doguwar riga takalminta red head dinta ma red Jakarta ma red ce se mayafin Data Dan yafa shima red itama ba laifi tayi kyau aminanta kuma pink din material suka sa da duk wani Wanda yazo ta bangarenta duk pink sukasa

muje zuwa


maman Yusuf
[3/19, 08:35] Zahra muhd mahmudπŸ’ƒ: πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€
         *SURBAJO*
πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€


Zahra Muhammad mahmud



*page 29-30*


Gabadaya jamaa sungama tafiya gurin dinner se Amarya da ango yarage

Motar dazasu tafi aciki ta iso dan haka alameen dakanshi yanufi falon Momy inda surbajo kezaman jira dan babu kowa agidan duk Sun tafi harda su mommyn


Dasallamarsa yashiga falon dakyar surbajo ta amsa gamida dago fuskarta

Wow itace kalmar alameen tafarko jikinshi narawa yakarasa gurinta hannunta yakamo yamikar da ita tsaye yayi hugging dinta kissing dinta yake kokarinyi dasauri surbajo takwace jikinta gamida ballamasa harara tace hoddijan aradu baka isaba yau inma wani asirin akabaka kadunga samin abaki da bakinka to yau takare danni yau KO abinci banajin zanci sabida gudun kar jambakina yagoge shine kai godaigodai dake kawani zo zaka lashe minshi da bakinka ko to Wlh a hir dinka takarasa maganar tana murgudamasa dan bakin dayasha makeup

Dariya abun yaba alameen yadda tayi maganar gunta yanufa da niyar kamata nanfa surbajo tasa gudu shima yana binta sunata zagaya dakin wedding gown dinta taja yakamata sabida Jan kasar datakeyi rungumota yayi jikinsa yana kokarin yimata Kiss wayarsa tashiga ruri dasauri yaciro wayar a aljihunsa mommy ce ke kira dasauri yadaga tunkafin yayi mgn mommy tafara fada
Aminu baka da hankaline kuntara jamaa a guri amma har yanzu baku isoba banason shashancin banza fa
Hakuri yashiga bata sannan yakashe wayar danshi ganin surbajo dayayine yasa yamanta akwai dinner da zasuje
Be tsaya bata lokaciba ya dauketa cak bayan yadauko mata fos dinta kai tsaye motar yanufa da ita tun kamin yakaraso wani soja yabude masa murfin bayan zaunar da ita yayi sannan shima yazagaya yashiga direba yaja suka dau hanya yayinda sauran motocin excode dinshi suka sa motar a tsakiya ana jiniya


Dayake ba nisa tsakanin gidan da hotel din so basu wani dauki lokaciba suka iso

Isowarsu keda wuya abokan ango da kawayen Amarya suka fito daga hall din danyima ango da Amarya rakiya zuwa ciki

Fitowa yayi sannan yakamo hannun surbajo itama tafito nanfa masu hoto da video camera suka shiga aykinsu

Kawayen Amarya da abokan ango ne suka sasu atsakiya
Sun fara tafiya surbajo se kokarin faduwa takeyi sabida takalmin kafarta me uban tudune ganin hakan da alameen yayi ne yasa be Bata lokaciba yadauketa kamar jaririya itakuma tasakalo hannunta ta wuyansa
Ihu da tafi kawayen suka sa dan gaskiya koni sunburgeni

Daganan suka fara takowa zuwa cikin hall din yayinda MC yashaida shigowarsu
Nanfa kallo yadawo kofar dazasu shigo

aisha ko wuyanta kamar ze tsinke dan tsawon datake karamasa nason hango ango da Amarya
shigowarsu seda numfashinta ya dauke yadawo bakaramin razana tayiba da ganin alameen dauke da amaryarsa

suko sauran jamaar dake gurin tafi kawai suke musu masu daukarsu hoto nayi har suka karasa gurin zamansu zaunar da surbajo yafarayi sannan shima yazauna
surbajo kara rufe fuskarta tayi da mayafinta sabida tasha kunya daukota da alameen yayi daurewa kawai tayi tabarshi yadaukota  dan tasan intace dakanta zata tafi faduwa zatayi

nanfa aka shiga gabatar da abinda yakaisu gurin inda MC yabukaci da ango yabude fuskar amarya batare da Bata lokaciba yabude fuskar surbajo

innalillahi wainna ilaihirrajuun itace kalmar da aisha ke furtawa dan ta gigice da ganin kyau irinna surbajo hawayene suka fara biyo fuskarta na bakin ciki dasauri Zuly tasharemata gudun kar wasu sugani rarrashinta suka shigayi amma kosu Sun jinjina dakyau irinna surbajo

hankalinta besake tashiba seda taji ana Kiran ango da Amarya sufito su yanka cake

duk abinda ake fadi da turanci akeyi kuma surbajo batajin turancin alameen  ne yamike sannan yakamo hannu surbajo yamikar da ita suka nufi gurin cake din dakyar surbajo take tafiya sabida gudun karta sha kasa duk da de rabin jikinta na jikin alameen
tafiyar Tata seta karamata kyau dan wasu dauka sukayi yanga takeyi harsuka karasa gurin cake din alameen besaketaba koda suka tsaya zagayo da hannunsa yayi ta kugunta yariketa ahaka suka yanka cake din aka tafa musu MC yace Amarya taba ango abaki cikin harshen turanci
surbajo batajiba alameen ne yaradamata akunne waigowa tayi tana harararsa akan yace tabashi abaki shikuma yana murmushi wayyo jamaa zokuga yadda wannan kallo da surbajo tayi yakoma na so da kauna ga alameen yanata murmushi

yanko cake din surbajo tayi tanufi bakin alameen kara rungumeta alameen yayi ta kwantar da kanta a kirjinshi ahaka tasa mishi cake din abaki huuuuu kawai mutane ke fadi dan wasu liki suka fara zuwa suna musu agurin dankoni Sun burgeni
shima alameen ahakan yabata cake din tana kwance ajikinshi

bayan sunkoma gurin zamansune aka bukaci ango yayi Godiya ga jamaar dasuka taru dominsu nan alameen yayi jawabin cikin harshen turanci bayan yagama aka bukaci Amarya tayi itama alameen ne yafada mata abinda MC yace yakara dacewa tayi da hausa kuma don Allah karta dunga sako aradu Γ  maganar murmushi tamasa Wanda yadauki hankalinsa sannan taamshi loudspeaker tafara magana cikin harshen filatanci
wow bakaramin burge mutane tayiba danko babu Wanda yayi zaton batajin turanci
bayan tagama ne akabukaci ango da Amarya su fito fili su taka
alameen ne yarukota suka fito filin yana rungume da ita aka samusu wakar da Sani slowly yamusu ta auransu suka fara takawa a hankali nanfa kowa yamike yafara yiwa ango da Amarya liki

aisha kuka take harda majina n'a bakinciki da sauri aminanta suka fitar da ita daga cikin hall din gudun karsuyi abin kunya
kai tsaye gida suka nufa da ita suna bata hakuri itako fadi take wayyo Allah alameen yakasheni yacuceni yarasa wacce ze auromin amatsayin kishiya se wannan gogaggiyar Yar bokon😜 nabani ni aisha
sude hakuri suke ta bata

acanko ango da Amarya ne keta cashewa
baa tashi ataronba se goma nadare

suna dawowa aka sa surbajo tayi wanka aka shiryata cikin shigar alfarma  aka nufi gidan mijinta da ita


maman yusuf

2 comments:

  1. Na yi imani da wanda ya mallaki 100% na zuciyarka ya cancanci yaΖ™in. Haka ne, ina alfahari saboda ban taΙ“a bin shawara mai kyau daga iyayena ba lokacin da nake son yin aure. Akwai yakin tsakanin iyalinmu biyu sannan mijina ya kasance jaririn uwarsa, 'yan uwansa sunyi amfani da shi da yawa wanda ya yanke hukunci ba tare da tuntube su ba. Abinda ya mamaye ni shine lokacin da dan shekaru 36 ya nemi iyayensa da wasu dangi su yarda kafin su gana da kowa da kowa, mafi munin abin da ya faru lokacin da aka umurce shi ya kawo ni zuwa Ζ™asarsu a Rampart, New Orleans, yana da haΙ—ari don karΙ“ar wannan gayyatar.Gamar tsakanin iyalanmu ya fara lokacin da ya karshe (wannan kimanin shekaru 4 da suka wuce), iyalinsa sun ba da wasu ka'idoji idan yana da matata (muna zama tare da su), na yi fushi lokacin da miji yarda da farin ciki da yanayin su (don haka mahaukaci). Iyalanmu sun yi tawaye kuma sun bukaci ya kamata in rabu da shi nan da nan.Na yanke shawarar ba shi harbin karshe kamar mutum wanda ya riga ya dauki 100% na zuciyata, na dauki haΙ—ari na tafiya ta ruhaniya tare da su ta hanyar tuntuΙ“ar Doctor Sharaja ta sharajasid @ Gmail.com, Ban sani ba amma mahaifin ruhaniya ya rigaya ya san zan shawarce shi. Da farko dai ya gaya mani hatsarin da nake ciki da kuma yadda miji ya zama bautar tun lokacin da aka haife ni, yadda suke ci gaba da kwakwalwa ta wanke shi don yin abin da suke so. Kamar yadda abin da mutum yake gani a hankali kawai, na gane cewa babu wanda ya ga abin da na gani a cikin mijina kuma wancan ne dalilin da ya sa na yi amfani da taimako na SHARAJA SHIRYA don cire shi daga cikin wahala. Idanunsa inda aka bude ta SHARAJA SID a karo na farko, iyalinsa sun Ζ™aunace ni kuma sun ba da duk bukatunmu, iyalanmu sun san zaman lafiya tun bayan Ζ™aunar da aka yi. Yana da shekaru 2 bayan Ζ™auna da mijina ya ci gaba da inganta kowace rana ba tare da tsangwama daga iyalinsa ba. Na jira tsayi sosai don raba wannan yanki mai ban mamaki. Na gode da lokacinka da kuma SHARAJA SID. Na san shi ta hanyar karatun wasu shaidun ban mamaki game da blogs .. rubutu firist sharajasid ++ (234) 9066-376197

    ReplyDelete
  2. wayyo Allah kusama cigabaa pls

    ReplyDelete